✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Takaddamar soyayya: Tsakanin maza da mata, wa ya fi rikon alkawarin soyayya (3)

Saba alkawari da rashin mutunci a sha’anin soyayya, mazan ne ko matan? Yau ma dai za mu ci gaba da tattauna wannan maudu’i, inda masoya…

Saba alkawari da rashin mutunci a sha’anin soyayya, mazan ne ko matan? Yau ma dai za mu ci gaba da tattauna wannan maudu’i, inda masoya maza da mata ke barje guminsu kamar haka:

Hamisu Bayan NEPA Malumfashi (08028907564), shi ma ya garzayo da nasa bayanin, yana cewa: “FDK, da fatan kana cikin koshin lafiya. Yaya kokarin da kake na sada zumunci? Allah Ya sa mu dace. To, gaskiya maza sun fi rike alkawarin soyayya, domin kana ganin kana da budurwa ita kadai ka sa a zuciya. Kuna nan wata rana ka je wurinta kana iya samunta da wani. To ka ga ka rike soyayyarta amma kuma ita a zuciyarta abin ba haka yake ba. Kai, maza sun fi mata alkawari. Na gode, Filfilon Dausayin Kauna.”

Daga C. Boy Suleja (08036160154), yana cewa: “FDK, da fatan kana cikin koshin lafiya, kai da daukacin jama’ar wannan zauren. To fa, tsakanin maza da mata su wa suka fi rike alkawarin soyayya? Wane kare ne ba bare ba?”

A sakon Abdurrahman Gumel (07032877083), ya bayyana cewa: “FDK, ina mika gaisuwata ga ’yan uwana na majalisar FDK. Gaskiya maza sun fi mata rike alkawarin soyayya. Dalilina shi ne, namiji sai ya rike budurwa guda daya amma mace kuwa sai ka gan ta da samari da yawa kuma dukkansu sonsu take yi. Ka ga  maza sun fi wadansu mata rike alkawari. Matan ma akwai masu rike alkawarin fiye da wadansu mazan, za ka ga mace ta rike saurayi guda daya. Duka maza da matan akwai masu rike alkawari, akwai marasa rike alkawari.”

Sai kuma Abdurra’uf Abdul Charanchi (07061385930), ya zo da nasa batun da ke cewa: “FDK, da fatan kana cikin koshin lafiya. Hahahahahaha! FDK, ai ba sai an sha wahala ba. Ni a ganina, ai babu wanda ya fi kowa rikon alkawari sai namiji saboda kowa ya san abubuwa uku ba a ba su alkawari. Na farko doki, na biyu kogi, na uku mace. Doki dai duk yadda kake sonsa, ka ba shi abinci, ka gyara masa wurin kwanciya, sai ya kada kai. Kogi kuwa sai ka wuce shi ba ruwa amma in ka dawo sai ka ga ya kawo ruwa ba ta inda za ka wuce. Ita kuwa mace alkawarinta na kwana arba’in ne, in ya wuce kuwa shi ke nan ta manta da kai!”

Maryam Garba Sakkwato (08160516384), ta ce: “Shi dama dan Adam butulu ne. Ka yarje wa mutum ya cuce ka. Hakan ta faru da ni har karo biyu. Rashin rike alkawari ai jini ne a jikin kowane namiji, sai dai Allah Ya kyauta, domin ko matan akwai marasa cika alkawari, sai dai a ganina maza su ne shugabannin saba alkawarin soyayya.”

Daga nan kuma sai Mista Tsari (08143853321), shi ma daga Sakkwato ya turo da nasa dogon sharhin, kamar haka: “Dubun gaisuwa gare ka FDK, tare da fatan kana cikin koshin lafiya. Haka kuma nake yi wa mabiya Dausayin Kaunar fatan alheri, tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. FDK, bari ni ma in tofa albarkacin bakina game da wannan babbar muhawara da ake yi, inda kake cewa tsakanin maza da mata su wane ne suka fi rike alkawarin soyayya? To a gaskiya kowa na iya kokarinsa amma tunda ka yi magana a kan wadanda suka fi, to ni a wurina, mata ne suka fi rike alkawari; duk da yake cewa ni ba ma’abuci soyayya ba ne amma ina kula da hakan. Hujjata kuwa a nan ita ce, abu na farko da za ka gane cewa mata sun fi rike alkawari shi ne; idan har mace tana sonka, to fa za ta iya batawa da kowa in dai a kanka ne, hatta ma iyayenta; sabanin mu maza. Abu na biyu kuwa shi ne, idan har mace ta furta maka cewa wane ina sonka da gaske kuma na yi maka alkawarin zan rike maka amana har karshen rayuwata, to tabbas za ta iya. Amma gaskiya mu maza muna da akasin haka saboda kuwa sau da yawa za ka ga saurayi yana soyayayya da budurwa amma da zarar ya hango wadda ta fi ta, sai ka ga kawai ya fara juya mata baya. ’Yan samari, kada dai ku ce Mista Tsari ya yi son rai. To babu son rai a cikin wannan maganar saboda magana ce ta gaskiya. Sannan abu na uku shi ne, idan har kuna zaune da mace a matsayin ma’arauta, to a gaskiya yana da wuya ka ga mace ta rabu da kai komai talaucinka, koda kai dutse ne saboda talauci. Abu na karshe kuwa, mace za ta iya zama da mijinta ko saurayinta duk runtsi ko wuya, haka kuma za ta iya zama da shi a lokacin da yake cikin halin kunci ko rashin lafiya. Za ta kuma iya tarairayarsa har zuwa lokacin da zai samu sauki, sabanin mu maza. Saboda wani lokaci za ka ga namiji a lokacin da matarsa take cikin mawuyacin hali, sannan ne yake kara tsanarta. Idan rashin lafiya ne, za ka ji ya ce a mayar da ita gidansu, har sai ta ji sauki.”