✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Takaddamar Soyayya: Tsakanin maza da mata, wa ya fi rikon alkawarin soyayya?

Kaka-kara-kaka! A yau mun shiga fagen babbar takaddama tsakanin maza da mata. Ni dai FDK (Filfilon Dausayin Kauna) zaune nake abina a gefe, ina kallon…

Kaka-kara-kaka! A yau mun shiga fagen babbar takaddama tsakanin maza da mata. Ni dai FDK (Filfilon Dausayin Kauna) zaune nake abina a gefe, ina kallon yadda hujjoji keta antayowa cikin kogina. Shin tsakanin maza da mata, wa ya fi rikon alkawarin soyayya?

Dahiru Dauda (KGY) Bindawa (08030693021) ne ya fara aiko da nasa batun a kan wannan maudu’in, inda yake cewa: “FDK, da fatan kai da iyali hadi da abokan aiki duk kuna lafiya. Ni kam sai dai a yi mani uzuri game da rashin jin tarin hujjojina dangane da fahimtata a kan wannan maudu’i, domin na yi amanna cewa shafin ba zai dauke dukkan hujjoji hadi da misalai hatta na karan kaina ba. A takaice abin da zan iya cewa shi ne; idan ana dara fidda uwa ake. Batun wa ya fi rike alkawarin soyayya tsakanin maza da mata, jawabin gaskiya ba tare da kishiyarta ba, ai tuni na gaba ya yi gaba. FDK, kalubalenmu!”

Nan take sai ga sakon Fateema ‘Yar Lajawa (08112538490), wacce ta kare mata da cewa: “Ai ko musu babu, mata mu muka fi rike alkawarin soyayya. Mace ce fa suna tare da mijinta, wata lalura ko nakasa ta same shi amma haka za ta jure ta zauna da shi amma namiji ko bai sake ta ba zai karo wata. Ko ka ga budurwa saurayinta ya yi tafiya amma ta jira shi har ya dawo amma namiji fa?”

Sirajo Muhammad Alwasa (08060557963) sai ya taho da nasa batun, yana cewa: “Ya ku ma’abuta wannan filin na Dausayin Kauna, ina yi maku fatan alheri. Bayan haka, don Allah FDK ka isar mani da tawa gudunmowa ga ma’abuta wannan fili maza da mata. Gaskiya mata suna da rike alkawain soyayya amma maza sun fi saboda duk wani saba alkawarin da maza ke yi mata ne ke sanya su yin haka. Dalili kuwa shi ne, ‘yan matan wannan zamani, idan har kana son su to dole ne sai ka yi masu karya idan kana son su karbi soyayyarka saboda tsananin son abin duniya, irin na matan wannan zamani.”

Abdullahi Sa’id Danhausa, Miltara Kano (07031658197), shi ma maza ya kambama da cewa: “FDK, magana ta gaskiya idan ana maganar rikon amana da alkwawarin soyayya, to idan aka samu maza sai a shafa Fatiha. Maza suna da rikon alkawari a soyayya da tsananin juriya duk rintsi duk wuya. Ruwan da ya dake ka shi ne ruwa, ni ganau ne ba jiyau ba a lokacin da muka kulla alkawarin soyayya da ni da Dokta NSB. Ta yi alkawarin cewa tana tare da ni, na amince da ita na rike alkawarinta, na manta da kowace mace sai ita. Son ta da kaunar ta suka yi katutu a cikin zuciyata, son ta ya zamo jina da ganina, tunaninta ya zama sinadarin farin cikin ruhina. Na manta da kowace mace sai ita amma saboda tsananin yaudara irin ta ‘ya’ya mata, yaudara ta yankan kauna, ta saba alkawarin soyayya, ta rataya linzamin kiyayya a zuciyarta, ta saba alkawari haka siddan da ranta da lafiyarta. Son ta da kauntarta suka dinga ruruta zuciyata, ta juya mini baya, ta nuna mini halinsu na mata saboda rashin sanin muhimmancin alkawari. Kai, mata, mata ba su san muhimmancin alkawari a soyayya ba kuma duk haka suke, kowane gauta ja ne. Ko mace ta ce ta rike maka alkawari to a kwana a tashi za ta saba.”

Shi ma Abdullahi Wayris Giro (08032624432) maza ya goya wa baya. A cewarsa: “Muna maraba da wannan fili mai albarka da kuma raya sunnar Manzon Allah (SAW). Gaskiya maza sun fi mata rikon alkawari, domin kuwa za ka yi shekara uku da budurwa kuna soyayya amma sai cikin karamin lokaci ta juya maka baya amma wani lokaci mata sun fi maza rikon alkawarin soyayya gaskiya. Allah Ya sa mu dace.”

Sai kuma Ummulkhair Kaduna (08169733818), wacce ta nuna goyon bayanta ga maza, inda take cewa: “Ina yi wa dukkan masoya Dausayin Kauna fatan alheri. Uncle FDK, ai ko ba a fada ba, maza sun fi rike alkawarin soyayya.”

Yusuf Yusuf Dantsoho (08079901259) ya zabi maza kuma ga hujjojinsa: “Maza sun fi rike alkawarin soyayya, ga dalilai na:  1-A addinance, namiji aka ba karfi fiye da mace, su ke jagorancin al’amuransu a zamantakewar aure. 2-Za ka ga kana soyayya da mace da niyyar aure amma tana hango wani mai danshi sai ta nemi bijirewa. 3-Maza na juriya cikin soyayya domin kokarin kyautatawa amma matan ba sa godiya. 4-Ba ka sanin mace sai an yi aure, daka nan halayya na rashin kirki sai su fara. 5-Ba namijin da zai so ya wahala don gina soyayya daka baya ya watsar sai da dalili.”