Search
Subscribe
Takai ya zama dan takarar Gwamnan Kano a PRP

Takai ya zama dan takarar Gwamnan Kano a PRP

Jam’iyyar adawa ta PRP ta tsaida Malam Salihu Sagir Takai, a matsayin dan takarar Gwamnan jihar Kano a zaben 2019.

Shugaban jam’iyyar PRP na jihar Alhaji Sammani Shariff ne ya bayyana wa manema labarai cewa, jama’iyyar ta tsaida Sagir Takai a matsayin dan takarar Gwamnan jihar Kano bayan tattaunawar da shugabannin jam’iyyar suka yi ranar Talata.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin