✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Takaitaccen tarihin marigayi Sarkin Musulmi Maccido (2)

A wannan mako za mu kawo muku karashen  tarihin marigayi Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Macciɗo. A makon jiya mun bayyana irin gudunmawar da ya bayar…

A wannan mako za mu kawo muku karashen  tarihin marigayi Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Macciɗo. A makon jiya mun bayyana irin gudunmawar da ya bayar a rayuwarsa a aikin gwamnati da harkokin sarauta; tun daga Hukumar En’e a matsayin mai bayar da taimako a ofishin kansila Sa Ahmadu Bello Sardauna har zuwa matsayin kansila zuwa lokacin da ya yi ritaya ya shiga siyasa:

Zamowarsa Sarkin Musulmi

Bayan rasuwar Sarkin Musulmi Abubakar III. Gadon wannan kujera ya zo da tangarɗa, inda da farko gidan radiyon Rima ya bayar da sanarwar naɗa Alhaji Muhammadu Maciɗɗo a matsayin wanda zai gaji mahaifinsa. Sanarwar da ta haifar da murna daga dubban mutanen Sakkwato, har ta saka ’yan kasuwa rufe rumfunansu, don murna haka sauran jama’a, amma wannan murna tasu daga baya ta koma ciki, inda aka sanar da naɗa marigayi Alhaji Ibrahim Dasuƙi a matsayin Sarkin Musulmi. Hakan ya haifar da tarzoma mai muni wacce ta jawo rasa rayukan jama’a da dama.

A 1996, Gwamnan Jihar Sakkwato na wancan lokaci (Kanar Yakubu Mu’azu)  ya bayar da sanarwar tsige Alhaji Ibrahim Dasuƙi daga wannan kujera da kuma naɗa Alhaji Muhammadu Macciɗo a madadinsa. Wannan shi ne abin da ya kawo zamowar Alhaji Muhammadu Macciɗo Sarkin Musulmi na 19 a Daular Usmaniyya mai daɗaɗɗen tarihi.

Gudunmawarsa

Sarkin Musulmi Muhammadu Maciɗɗo, ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen ɗaukaka wannan daula ta Musulunci. Kama tun daga gina masallatan da suka haɗa  da na salloli biyar da kuma na Juma’a, zuwa makarantu, taimakon ɗaiɗaikun jama’a, kyautata danganta tsakanin Musulunci da sauran addinai, da kuma samar da tsaro da zaman lafiya da sauran abubuwa masu yawa.

Ayyukan yau-da-kullum

A cikin rayuwarsa ta yau da kullum, Mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo, yakan tashi da safe kullum a tsakanin  karfe 4:30 zuwa 5:00 na asubahin kowace rana don shirya zuwa masallaci Sallar Asuba wacce ya ke yi a masallacin da ke cikin gidan Sarki. Bayan ƙare Sallar Asuba, yakan zauna yana addu’o’i har zuwa fitowar rana kimanin 7:30 na safe.

Daga nan kuma sai ya shiga wajensa na musamman ya yi karin kumallo, sannan ya samu ganin duk wanda ke da buƙatar ganinsa daga ɓangaren iyali da ’yan uwansa har zuwa karfe 10: na safe.

Da misalin 10:00 na kowace safiya kuma, matuƙar yana gari, akan ɗauki Mai alfarma Sarkin Musulmi zuwa Masallacin Juma’a, inda ake gudanar da karatun Alkur’ani, bayan an ƙare kuma a yi addu’ar zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa da kuma neman rahama ga magabatansa, shi kansa, iyalansa, daular Musulunci, Jihar Sakkwato, ƙasa baki ɗaya da sauransu.

Daga karef 10:30 kuma, yakan koma fada don sauraren jama’a. A wannan lokaci ne talakawa ke zuwa suna gaishe shi da kuma hakimansa ko wakilansu. Haka nan ma Gwaggon Kano, matar marigayi Ahmadu Bello Sardauna, kan tura wakilanta su gaishe da Sarki.

Bayan dukkan sauran jama’a da wakilan masu riƙe da sarautu na wannan masarauta sun gama gaisuwa, sai kuma manyan mashawarta su shigo inda Wazirin Sakkwato Alhaji Usman Junaidu ke wucewa gaba saura na biye da shi. Bayan duk sun shiga sun zauna, sai kuma zaman majalisa na safe ya fara. Kaɗan daga cikin abubuwan da suka fiye faruwa a wannan majalisa akwai Musuluntar da waɗanda ba Musulmi ba, bayar da takardar shaidar canjin suna, tallafa wa waɗanda suka Musulunta da kuɗi dan gudanar da kasuwanci da sauransu.

Da misalin karfe 1:00 na rana kuma, sai majalisa ta tashi. Mai alfarma Sarkin Musulmi ya yi shirin Sallar Azahar har zuwa Sallar La’asar. A wannan tsakanin ne Sarki ke cin abinci, sannan kuma ya samu ya huta.

Karfe 4:00 na yamma, bayan Sallar La’asar, shi kuma wannan lokaci ne na sauraron karatuttukan da malamai ke gudanarwa wadanda ake kama-kama daga wannan malami zuwa wancan a fannoni ilimin addini daban-daban, kama daga fassarar Alkur’ani, hadisai da sauransu. Wannan kuma ana yi ne a ranakun Asabar zuwa Laraba.

Daga karfe 4:30 zuwa 6:00 na yamma kuma, lokaci ne da Sarkin Musulmi Muhammadu Maciɗɗo yake sake sauraron koken jama’a da sauran bayanai daga gare su.

Daga karfe 6:30 zuwa 8:00 na dare, Sarkin Musulmi yakan zauna a cikin masallacin fada don yin Sallar Magariba, sannan ya jirayi Sallar Isha’i. Daga karfe 8:00 zuwa 9:00, sai ya sake sauraron jama’arsa. Da zarar ƙarfe 9:00 ta yi, sai kuma ya koma wajen iyalansa.

A ranakun Talata kuma, Sarkin Musulmi Muhammadu Maciɗɗo yakan je gidan gwamnatin jihar Sakkwato don halartar zaman tattaunawa kan harkar tsaro.

Larabar ƙarshen kowane wata, ita kuma rana ce ta zaman Majalisar Sarki, inda yake zama da dukkan hakimansa da masu naɗin Sarki. A ƙarshen wannan zama ne ake sanar da faruwar abubuwan da suka haɗa da rasuwar wani mai sarauta, sabon naɗin sarauta, umarnin da ya fito daga gidan gwamnati, sanar da aukuwar wata annoba da kuma matakin da za a ɗauka game da ita da sauran abubuwa da suka shafi wannan.

Rasuwarsa

Mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammadu Maciɗɗo Abubakar, ya rasu shi da ɗansa Badamasi Maciɗɗo a ranar 29 ga Oktoban shekarar 2006 a wani hadarin jirgin sama ƙirar Boing 737 na Kamfanin Sufurin Jiragen Sama na ADC, jim kaɗan bayan tashin jirgin daga filin jirgin sama na Abuja, a tazarar da ba ta wuce kilomita biyu ba a wata unguwa da ke kusa da filin jirgin mai suna Tungar Madaki.

Sarkin Musulmi Muhammadu Maciɗɗo ya rasu yana da shekara 80 a duniya, bayan ya riƙe wannan kujera mai daraja na tsawon shekara 10.

An yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, aka kuma binne shi bisa Sunnah a Hubbaren Shehu da ke Sakkwato.

Mun ciro wannan tarihi ne daga Kundin Sani na Britannica (2006). Muhammadu Maciɗɗo Sultan of Sokoto Nigeria. https://www.britannica.com/biography/Muhammadu-Maccido da kuma Rumbun Ilimi.