✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Takaitaccen tarihin Sarakunan Fulani na Kano (1)

A yau mu leka rumbun ilimi ne inda muka kawo muku takaitaccen tarihin sarakunan Fulanin da suka mulki Kano tun daga jihadin Shehu Usman Dan…

A yau mu leka rumbun ilimi ne inda muka kawo muku takaitaccen tarihin sarakunan Fulanin da suka mulki Kano tun daga jihadin Shehu Usman Dan Fodiyo. Wadannan sarakuna sun faro ne daga kan Sarki Sulaimanu sai Malam Ibrahim Dabo har zuwa kan Sarki Muhammadu Sanusi II wanda shi ne ke kan karaga a yau:

Malam Sulaimanu dan Abuhama: Ya yi sarautar Kano daga 1807 zuwa 1819, Miladiyya

Sarki Sulaimanu shi ne Sarki na 44  a jerin sarakunan Kano, kuma Sarki na farko a zuriyar Fulani. A farkon sarautarsa Fulani sun hana shi shiga Gidan Rumfa, saboda haka sai ya zauna a gidan Sarkin Dawaki. Yana nan zaune cikin wannan gida sai wani mutum ya ce da shi, “Idan ba ka shiga Gidan Rumfa ba Kanawa ba za su bika ba.” Da ya ji haka sai ya aike wa Fulanin cewa yana nemansu. Su kuma suka amsa masa da cewa, “Ba za mu zo wurinka ba, sai dai kai ka zo wurinmu duk da cewa kai ne Sarki. Idan ka je gidan Malam Jibir ma zo gare ka.” Ya tashi ya je kuma ya kira su suka amsa.

Da suka taru sai ya tambaye su, “Don me kuka hana ni shiga Gidan Rumfa?” Sai Malam Jibir ya ce da shi, “Don kada mu shiga gidajensu mu haifi ’ya’ya su koma ga halayensu.” Da Sarki Sulaimanu ya ji haka sai ya ƙyale su ya tafi zuwa ga Shehu Usmanu ya nemi izini shi kuma ya ba shi takobi da wuƙa da tuta, ya kuma yardar masa ya shiga Gidan Rumfa. Sannan ya shiga ya kuma samu iko a kan Kanawa birni da ƙauye aka bi shi. Sarki Sulaimanu ya mulki Kano tsawon shekara goma kafin ya rasu. Allah Ya jiƙansa da rahama, amin

Ibrahim Dabo dan Mahmudu, 1819 – 1846, Miladiyya

Sarki Ibrahim Dabo shi ne Sarkin Kano na 45 kuma Sarki na biyu a sarakunan Fulani. Sarki Ibrahim Dabo mutum ne adali kuma masanin furu’a (fiƙihu), sannan mutum ne mai taimako.

Sarki Ibrahim Dabo shi ake yi wa laƙabi da “Mai Buɗe Garuruwa”. Sabon Galadima da ya naɗa; wato Malam Sani a matsayin Galadiman Kano, ya yi nufin cin amanarsa amma Allah bai nufa ba.

Bayan zamowar Sani Galadiman Kano sai ya riƙa haɗa munafunci ta ƙarƙashin ƙasa, ya riƙa aika wa sarakuna Kudu da Arewa, Gabas da Yamma kan su haɗu su yaƙi Sarkin. Daga ciki akwai manyan garuruwa irin su Ƙaraye da Ɗambatta da Kazaure da Dutse da Birnin Kudu da Rano da sauransu. Da Sarki ya samu labari sai ya shiga addu’a sai da ya yi kwana arba’in ba ya fita. Da ya fito sai ya haɗa runduna ya je gindin Dala ya yada sansani sai da ya yi wasu kwanaki a wurin. Sa’annan ya koma gida. Sai ya aika Sarkin Dawaki Mai Tuta zuwa Ƙaraye ya je ya yaƙe ta kuma ya yi galaba. Daga nan shi da kansa ya yi shiri ya fita zuwa Jirima ya yaƙe ta ya yi nasara. Haka-haka ya yi ta yi har sai da sauran garuruwa suka tabbatar zai ci su da yaƙi sannan suka zo suka bi shi. Saboda haka ake yi masa kirari da “Mai Buɗe Garuruwa”.

Bayan rasuwar Galadima Sani sai Sarkin Kano Ibrahim Dabo ya sake naɗa wani abokinsa mai suna Ango a matsayin Galadiman Kano.

Sarki Ibrahim Dabo ya mulki Kano tsawon shekara 27 da wata tara. Ya rasu a watan Safar. Allah Ya jiƙansa da rahama.

Usmanu dan Dabo 1846-1855, Miladiyya

Usmanu dan Dabo shi ne Sarki na 46 a jerin sarakunan Kano sannan Sarki na uku a jerin sarakunan Fulani.

Kalmar nan ta “Mai Babban Ɗaki” ta samo asali ne a zamaninsa, saboda ya gina wa mahaifiyarsa babban gida Tafasa sai aka riƙa kiranta da wannan laƙabi.

A lokacinsa ya samu kangara daga Haɗeja. Sannan a zamaninsa Sarkin Dutse Bello ya kangare sai aka hilace shi aka tuɓe shi. Haka  kuma shi ne Sarkin da ya gina garin Gogel, saboda yana da gona a can. Ya mulki Kano tsawon shekara ɗaya da wata goma.

Abdullahi dan Dabo, (1855 zuwa 1882) Miladiyya

Sarki Abdullahi ɗan Dabo shi ne Sarki na 47 a jerin sarakunan Kano. Sannan Sarki na huɗu a jerin sarakunan Fulani.

A zamanin Sarki Abdullahi kasar Kano ta yi yaƙe-yaƙe da dama. Ta yi galaba wasu lokutan, a wasu lokutan kuma an yi galaba a kanta.

Sarki Abdullahi ya kawo abubuwan ci gaba a ƙasar Kano da dama. Daga ciki akwai cewa shi ya sake gina Zauren Turakin Manya bayan ya rushe, sannan ya gina Masallacin Turakin Manya. Sannan a zamaninsa aka fara harba bindiga idan Sarki zai hau, wanda wannan yana ɗaya daga cikin al’adun Masarautar Kano har zuwa yau.

Sarki Abdullahi ɗan Dabo ya yi sarautar Kano tsawon shekara 27 da wata takwas kafin ya rasu a Karofi. Allah Ya jiƙansa da rahama.

Muhammadu Ballo (1882 zuwa 1893) Miladiyya

Sarki Muhammadu Bello shi ne Sarki na 48 a jerin sarakunan Kano, sannan  Sarki na biyar a jerin sarakunan Fulani.

Sarki ne mai yawan alheri. Saboda kyakkyawan hali da yake da shi, bai samu wata matsala daga wajen masarautarsa ba sai wata ’yar tangarɗa da ya samu ta cikin gida kuma ya shawo kanta.

Ya yi sarautar Kano ta tsawon shekara 11 da wata bakwai. Ya rasu a gidan sarauta kuma a nan aka binne shi.

Tukur dan Ballo (1893 zuwa 1894) Miladiyya

Sarki Tukur shi ne Sarki na 49 a jerin sarakunan Kano. Sannan Sarki na shida a jerin sarakunan Fulani.

Sarki Tukur bai samu goyon bayan jama’a ba wajen naɗinsa. Ya shiga gidan sarauta ta Ƙofar Fatalwa. Ya kai kimanin kwana goma sha a cikin rumfar kara da ya yi a gidan sarauta ba tare da an zo an yi masa caffa ba.

Sai daga baya wadansu ’yan tsiraru da suka haɗa da Wamban Kano Shehu da Mamman Mai Lafiya da Galadima Yusufu da wadansu ’yan mutane kaɗan suka yi masa caffa.

Bayan fitowar Galadima Yusufu daga gidan Sarki sai mutane suke yi musu ba’a da cewa, “Mutum biyar sun rinjayi mutum ɗari.”

Bayan Galadima Yusuf ya yi wa Sarki Tukur caffa an yi masa waccan ba’a, sai abun ya ɓata masa rai, saboda haka suka taru shi da sauran ’ya’yan Sarki a gidansa da ke Ciranci, suka yanke shawarar cewa su fice su bar garin. Sun fita ta Ƙofar Nasarawa inda suka tsaya suka kwana da safe suka rankaya zuwa Wudil, daga nan sai Kademi, sai suka zarce zuwa Takai, inda suka je suka yi shirin yaƙi sannan suka koma Kano, suka fara yaƙi har sai da suka kai Ƙofar Mata Gindin Rimi. Da Sarkin Gaya Dabo ya samu labari, sai ya ɗaura ɗamarar yaƙi ya je ya fatattake su. Jama’a suka bi su da ihu suna zaton sun gudu ne ashe sun sake komawa Takai ne suka sake sabon shirin yaƙi.

An kashe Sarki Tukur a garin Tafashiya da ke kusa da garin Ɗanzabuwa.

Mun ciro wannan rubutu daga https://rumbunilimi.com.ng/masarautu.html

Za mu ci gaba