Da Dumi Dumi

Takaitaccen tarihin sarakunan Haɓe na Kano (1)

A wannan mako Aminiya ta yi ninkaya ce a cikin tafkin tarihin sarakunan habe a Masarautar Kano. Mun kawo kadan daga cikin binciken masana game da tarihin sarakunan da suka mulki kasar Kano a lokacin mulkin Habe. Kano gari ne mai daɗaɗɗen tarihi, kuma akwai ra’ayoyi mabambanta dangane da asalin wanda ya kafa garin Kano da kuma ƙarnin da aka kafa ta. Amma zance mafi shahara shi ne cewa an kafa Kano ne a ƙarni na tara. (Dokaji 1958 da Ashiwaju da Enem da Abalogu, babu shekarar bugawa). Dangane da mutanen da suka kafa garin Kano, Dokaji (1958), ya tafi a kan cewa wadansu maharba waɗanda ba a san ko su wane ne ba, kuma ba a tabbatar daga ina suka fito ba, sai dai cewa ana ganin daga Arewaci suka zo yankin da nufin farauta, su suka fara zama a wannan yanki. Daga cikin irin waɗannan mutane akwai wanda ake ganin shi ya fara zama a wani dutse da daga baya aka riƙa kiran dutsen da sunansa. Sunan wannan mutumin shi ne Dala. Saboda haka sai aka riƙa kiran dutsen da “Dutsen Dala.” Shi kuma Dala mutum ne mafaruci kuma yana da ’ya’ya:

Sarki Bagauda Ɗan-Bawo 999-1063, Miladiyya

Bagauda sunan mahaifinsa Bayajidda shi kuma Bayajidda ɗan  Sarkin Bagadaza (Baghdad) ce; da take kasar Iraƙ a yau.

Shi ne mutumin da masana tarihi suke fara lissafin sarautar Kano daga kansa; wato ke nan shi ne Sarkin Kano na farko. Bagauda ya je garin Kano sanadiyar gudunmawa da jama’ar yankin Kano suka nema daga wurin sarauniya Daurama saboda adabbarsu da mahara suka yi.

ADVERTISEMENT

Kafin zuwan Bagauda ya mulki Kano dukkan yankunan nan ba a matsayin abu guda suke ba. A’a, akwai rukunin jama’ar da ke zaune a kan Dutsen Dala waɗanda suke ƙarƙashin shugabancin Barbushe da sauran jama’ar da ta ƙunshi manoma, mafarauta da sauransu da ke zaune a Maɗatai. Abin da ya raba tsakanin waɗannan al’umomi biyu kuma shi ne kogin jakara. Haɗewar waɗannan jama’a biyu ƙarƙashin mulkin Sarki guda wato Bagauda, shi ne tushen masarautar Kano.

Babbar nasarar farko da Sarki Bagauda ya samu a Kano ita ce ta ganin bayan shugabannin jama’ar Dala masu bautar Tsimburbura, daga cikin waɗanda Bagauda ya hallaka akwai Jankare da Biju da Bodari da Ribau. Kisan waɗannan manyan matsafa kuma jarumai ya girgiza duk wani mai bautar Tsimburbura da haka suka sallama suka bi shi. Sannan a ɗaya ɓangaren ya tsorata waɗancan baƙin mahara masu zuwa suna yaƙar mazauna yankin Maɗatai saboda haka ƙasa ta zauna lafiya abubuwa suka ci gaba da tafiya yadda ake so.

Samuwar wannan zaman lafiya ta bai wa Sarki Bagauda cikakkiyar damar ɗaura ɗamarar fita wajen don faɗaɗa gari ta yankin Arewa. Tunda ya tashi daga wurin da ya zauna na ƙarshe wanda kuma a nan ya fi daɗewa, wato Gazarzawa, yake ta fafatawa har sai da ya dangana da Sheme wacce ita ce Kazaure a yau. Tun kafin nan, Sarki Bagauda ya fara zama a Durami sannan ya koma Talautawa sannan daga ƙarshe ya koma Gazarzawa kafin barinsa garin. Saboda haka babu wani takamaiman wuri wanda Bagauda ya zauna ya kafa fadar mulkinsa a Kano.

Saukar Sarki Bagauda a wannan gari na Sheme, sai ya dira a kan manyan gari, waɗanda suka yi taurin kai kamar Gubusani da Bauri da Gazawuri da Ɗangefe da Fasa-taro da Baƙin-bunu duk ya markaɗe su. Saura kuma da suka ga haka ta faru da manyan jarumai sai suka miƙa wuya suka bi shi.  Sarki Bagauda wannan sabon zango a wurinsa ya dace saboda ya koma kusa da mahaifiyarsa inda masana tarihi ke ganin ma cewa ya riƙa samun tallafin mayaƙa daga hannun mahafinsa don haka ya gagari kowa. Su kuma jama’ar Kano musamman attajirai, manoma, maƙera da sauransu da ke zaune a yankin Maɗatai suna ganin Sarki ya yi musu nisa saboda haka suka aika masa ya taimaka ya dawo gare su duk da cewa ba sa samun wata barazana daga ciki ko wajen gida.

Wannan gari na Sheme a nan Bagauda ya zauna ya ci gaba da hayayyafa har zuwa ƙarshen rayuwarsa.

Sarki Warisi dan Bagauda 1063-1095 Miladiyya

Warisi, shi ne Sarkin Kano na biyu wanda ya gaji mahaifinsa Bagauda. Sunan mahafiyarsa Saju. Tun barin Bagauda Kano, gari ya ci gaba da bunƙasa ta kowace fuska; ƙaruwar arziki, yawan jama’a, faɗaɗar gari da ma kafuwar wasu sababbin yankuna. Saboda haka sai Kanawa suka sake aikewa da wakilansu zuwa gare shi suna roƙonsa da ya daure ya ƙaurato zuwa gare su. Amma dai shi ma kamar mahaifin nasa a Sheme ya yi mulkinsa har ya gama. Amsar da sabon Sarki ya bai wa jama’arsa da ke zaune a Kano ita ce cewa, gaskiya shi shekaru sun riga sun cim masa, saboda haka ba zai samu dawowa nan ba.

 

Sarki Giji-Masu dan Warisi 1095 -1134 Miladiyya

Giji-Masu shi ne Sarkin Kano na uku, ya gaji mahaifinsa Warisi dan Bagauda dan Bayajidda. Sunan mahaifiyarsa Yanas.

Da hawan wannan sabon Sarki sai Kanawa suka yi wuf, suka sake tura buƙatarsu ta ya baro Sheme ya dawo ya zauna tare da su a Kano, kuma Kanon ma a yankin Gazarzawa. A wannan karo Kanawa suka dace haƙa ta cimma ruwa, Sarki ya amince. Sai dai da Sarki Giji-Masu ya shigo Kano, bai sauka a ko’ina ba sai yankin Dutsen Dala, wurin da cibiyar masu bautar Tsimburbura take.

Saukarsa a wannan wuri ya tayar wa sauran magadan shugabannin masu bautar Tsimburbura hankali, inda sai da ta kai ga sun yi taron tattaunawar gaggawa a wajen shugabansu na yankin Jakara suka cimma matsaya cewa ba za su yarda ya rushe musu gunkin Tsimburbura ba matuƙar suna raye.  Saboda su a zatonsu ya zaɓi ya zauna a nan ne don ya kawo ƙarshen bautar Tsimburbura.

Da Sarki Giji-Masu ya samu labarin wannan tattaunawa tasu, sai ya aike musu cewa yana roƙonsu su zo su haɗa kai su kafa al’umma ɗaya ƙarƙashin sarautarsa. Su yarda su bi shi a matsayin Sarki. Jin wannan gayyata sai ya ba waɗannan mutane mamaki inda aka ce har sai da shi shugaban nasu ya yi yunƙurin aurar da ’yarsa ga ɗan Sarki Giji-Masu amma wani babban Galadiman shugaban masu bautar Tsimburbura ya hana shi. Saboda shi a tasa fahimtar in har haka ta ƙullu to idan tafiya-ta-yi-tafiya su za su koma ba komai ba. Jin wannan ta sa jama’ar Dala suka yarda suka miƙa wuya cikin sauƙi. Wannan kuma shi ne Sarki na farko da ya yi nasarar haɗe waɗannan jama’a biyu waɗanda suka daɗe suna cin gashin kansu ƙarƙashin inuwa ɗaya, suka zama ƙasa ɗaya, al’umma ɗaya.

Wannan nasara da Sarki Giji-Masu ya samu ta haɗe dukkan kewayen Kano ta wancan zamani ya zama abu guda, sai kuma ya sake gayyatar waɗannan jama’a ta Dala cewa su zo su haɗa ƙarfi waje guda su gina ganuwar da za ta zagaye garin don samun kariya daga abokan gaba da kuma miyagun dabbobi. Wanda kuma hakan aka yi. Wannan shi ne farkon ginin ganuwa da ƙofofi da aka yi a Kano.

An fara wannan gini daga Ƙofar Rariya; wacce gurbinta yana tsakanin Ƙofar Ɗan Agundi da Ƙofar Na’isa. Daga nan gini ya ci gaba zuwa Ƙofar Mazugal, zuwa Kofar Ruwa, sannan sai Ƙofar Adama. A kwana a tashi gini yana ci gaba har sai da ya kawo Ƙofar Adama, daga nan ya shige zuwa Ƙofar Gudan. Kama-kama gini ya ci gaba zuwa Ƙofar Waika, daga nan ya zarce zuwa Ƙofar Kansakali, daga nan sai Ƙofar Kawun-Gari inda daga ƙarshe ya ƙare a Ƙofar Tuji.

Da Sarki ya samu nasarar yin wannan jan aiki, sai kuma ya ɗora a kan faɗaɗa ƙasa, inda ya runtuma zuwa Kudanci wanda sai da ta kai shi har wajen su Gano. Tarihi ya nuna cewa da masarauta ta faɗaɗa sai Sarki Giji-Masu ya fara bada wasu yankuna a kula masa da su daga cikin wuraren da ya bayar akwai Gano, wadda aka ba Sarkin Rano ya kula da su.

Bayan dogon zamani yana mulki, shi ma Sarki Giji-Masu kamar kowane mai rai sai ya koma ga mahaliccinsa.

Mun ciro wani sashi na wannan rubutu daga: Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri, Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Gobernment Press, Kano.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Wallafar The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Dab’in Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna. Da kuma shafin intanet. Za mu ci gaba.

 

Share