✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Takaitaccen tarihin sarakunan Haɓe na Kano (2)

Yau za mu ci gaba da kawo tarihin sarakunan Habe a Masarautar Kano, kamar yadda binciken masana game da tarihin sarakunan da suka mulki kasar…

Yau za mu ci gaba da kawo tarihin sarakunan Habe a Masarautar Kano, kamar yadda binciken masana game da tarihin sarakunan da suka mulki kasar Kano ya nuna. A makon jiya mun ce akwai ra’ayoyi mabambanta game da asalin wanda ya kafa garin Kano da ƙarnin da aka kafa ta. Amma zance mafi shahara shi ne cewa an kafa Kano a ƙarni na tara (Dokaji 1958 da Ashiwaju, Enem da Abalogu, babu shekarar bugu). Kuma mun ambaci mutanen da suka fara zama a garin Kano, inda daga cikinsu muka ce akwai wanda ake ganin shi ya fara zama a wani dutse wanda daga baya aka riƙa kiran dutsen da sunansa. Sunan mutumin shi Dala inda aka rika kiran dutsen da Dutsen Dala:

 

Nawata da Gawata

Bayan rasuwar Sarki Giji-Masu dan Warisi, sai wadansu tagwayen ’ya’yansa Nawata da Gawata suka gaje shi. Suna da wata bakwai a kan karagar mulki sai ɗaya daga cikinsu ya rasu ɗayan kuma ya ɗora inda shi ma bayan shekara ɗaya da wata biyar,  ya rasu. Sun yi sarautar Kano ta tsawon shekara biyu cur.

 

Yusa dan Giji-Masu 1136 – 1194M

Sarki Yusa wanda ake kira da Ɗariƙi, shi ne Sarki na biyar a jerin sarakunan Kano. Ya hau karagar mulkin Kano bayan rasuwar yayyensa. Shi ɗan Sarkin Kano na uku. Wato Sarki Giji-Masu, shi kuma ɗan sarkin Kano Warisi, shi kuma ɗan Sarki Bagauda.

Marubuta tarihin Kano sun rinjaya a kan cewa shi ne Sarkin da ya faɗaɗa Kano ya mai da ta babbar ƙasa. Shi ya ci garuruwa irin su Ƙaraye da yaƙi har sai da ya dangana Kano da ƙasar Katsina da kuma Zariya. Sannan shi ya ɗora wa mabiya Tsimburbura biyan haraji na sumunin duk abin da suka noma.

 

Naguji dan Ɗariƙi 1194 – 1247M

Wannan shi ne Sarki na shida a jerin sarakunan Kano. Sunan mahaifiyarsa Yankuma ko Muntaras. Sarki Naguji ɗan Sarkin Kano Yusa ne, ɗan Sarki Giji-Masu ɗan Sarkin Kano Warisi ɗan Sarki Bagauda.

Shi ma ya ci gaba da faɗaɗa masarautarsa ta gefen da mahaifinsa ya mutu ya bari. Ya yaƙi mutane tun daga Kura har zuwa Tsangaya. Daga nan ya ɗora zuwa yaƙin Santolo wanda ya ɗauke shi tsawon shekara biyu amma abu ya gagara. Dole Sarkin ya karkata akalar dokinsa zuwa gida saboda barin baya da ƙura da ya yi. Abin kuwa da ya faru shi ne cewa ganin ya ɗauki lokaci bai dawo gida ba, sai dangin Tsumburbura suka fara yunƙurin yi masa tawaye, saboda haka da isowarsa garinsa sai kawai ya kama manyan cikinsu ya yayyanka. Daga cikin waɗanda ya yanka akwai Samagi dan Mazauda da Doriyi ɗan Bugazau da Burdarganguta ɗan Doron-Maje, da kuma Buzuzu ɗan Jandodo. Sauran mabiyansu kuma ya ɗora musu haraji na sumuni (kashi ɗaya cikin takwas) na abin da suka noma. Wannan kuma shi ne asalin fara karɓar haraji a hannun talakawa a ƙasar Kano.  Ya mulki Kano na tsawon shekara hamsin da biyar sannan ya mutu.

 

Guguwa dan Giji-Masu 1247 – 1290 Miladiyya

Shi ne Sarki na bakwai a jerin sarakunan Kano. Sunan mahaifiyarsa Munsada. Sarki Guguwa ɗan Sarkin Kano Giji-Masu ɗan Sarkin Kano Warisi ɗan Sarki Bagauda.

Sarki Guguwa mutum ne mai karimci. Ya kasance mai kyautata wa talakawansa. Shi ne Sarkin da ya samu lalura ta makanta a lokacin da yake kan karagar mulki. Ya mulki Kano na tsawon shekara arba’in da huɗu. Shekara ashirin da biyu yana gani, ashirin da biyu kuma yana makance. Daga baya aka cire shi aka maye gurbinsa.

 

Shekarau dan Ɗariƙi 1290 – 1307 Miladiyya

Sarki Shekarau shi ne Sarkin Kano na takwas. Sarkin Kano Shekarau ɗan Sarkin Kano Yusa wanda ake kira Ɗariƙi ɗan Sarki Giji-Masu ɗan Sarkin Kano Warisi ɗan Sarki Bagauda.

Sarkin Kano Shekara ɗan Sarki Ɗariƙi ya yi sarautar Kano tsawon shekara goma sha bakwai. Masu bautar Tsumburbura sun bi shi har gida suka yi sulhu da shi. Sarki ne da ya kasance mai son zaman lafiya. Saboda kyakkyawar dangantakar da ke tsakaninsa da masu bautar Tsumburbura har sai da suka kusan sanar da shi sirrin bautar, amma babbansu Samagi ya ƙi fir! Yana cewa in suka yi haka za su koma ba komai ba a mance da ƙabilarsu. Har ya mutu bai yi yaƙi da su ba.

 

Tsamiya ɗan Shekarau 1307 – 1343,Miladiyya

Sarkin Kano Tsamiya shi ne Sarki na tara a jerin sarakunan Kano. Shi ɗan Sarkin Kano Shekarau ne ɗan Sarkin Kano Yusa wanda ake kira Ɗariƙi ɗan Sarki Gijimasu ɗan Sarkin Kano Warisi ɗan Sarki Bagauda. Sunan mahaifiyarsa Sajamta.

Sarki Tsamiya shi ne Sarkin da ya fatattaki masu bautar Tsumburbura. Mutum ne da ya yi fice wajen gwarzantaka, sadaukantaka da kwarjini, ga shi kuma da tsananin fushi da ƙarfi. Da hawansa gadon mulki ya sanar da Maguzawa cewa “Ana gadon soyayya, haka kuma ana gadon ƙiyayya. Ba komai tsakanina da ku sai yaƙi.” Ya ce da su gaskiya ba zai yaudare su ba, saboda matsoraci ne ke yaudara. Jin waɗannan maganganu na Sarki ya tayar da hankalin Maguzawa. Suka koma suka tattauna suka cimma matsaya cewa su ba shi dukiya mai tarin yawa. Daga cikin abubuwan da suka kai masa akwai bayi har ɗari biyu. Amma ya yi fatali da wannan ta yi nasu. A wata ranar Asabar Sarki ya aike Marukashi gare su da saƙon cewa su shirya Sarki na tafe ranar Alhamis. Ga abin da saƙon ke cewa, “Ranar Alhamis ina zuwa Ƙaguwa in Allah Ya so, in shiga cikin gininta, in ga abin da yake cikinsa, in rushe ginin, in ƙone itaciyar.”

Lokacin da Maguzawa suka ji faɗar Sarki sai hankalinsu ya tashi. Saboda haka duk wurin da suke a wannan yanki sai suka riƙa tururuwa zuwa gindin wannan gunki nasu. Suka yi dandazo da kayan yaƙinsu a wurin har zuwa hudowar alfijir na ranar Alhamis. Alfijir na hudowa Sarki ya fito da jama’arsa suka nufi gindin gunki. Da sarki ya kai wajen sai suka hana shi shiga. Sai Sarki ya waiga ya kira sunan ɗaya daga cikin gagararrun mayaƙansa ya ce, “Ina Bajere?” Yayin da Bajere ya ji haka sai ya fito da mashinsa ya rika sukar kafirai yana kai su ƙasa. Wuri ya hautsine, yaƙi ya kai yaƙi, har sai da Bajere ya samu shiga ɗakin da gunkin yake, yana shiga ya tarar da wani mutum ya jingina a jikin gunkin yana riƙe da wata jar macijiya. Yana sukarsa da mashi sai ya rusa wani ihu wuta ta riƙa fita daga bakinsa, hayaƙi ya turnuƙe gari, ya fito daga ɗakin da gudu. Yana fitowa sauran jaruman Sarki da ke waje su bi shi da gudu tare da Sarki. Sai ya ruga ya yi wajen Ƙofar Ruwa. Can ya je ya faɗa wani kududdufi, Sarki ya tsaya bakin wurin har sai da ya kai wani lokaci. Da suka ga bai fito ba sai suka dawo. Ko kafin su dawo dukkan sauran Maguzawan sun gudu sun bar wurin, sai wadansu jarumai ’yan kaɗan da suka miƙa wuya. Sarki ya shiga ɗakin gunki, ya ga abin da ya gani. Da ya fito ya ce da su, “Me ya hana ku gudu?” suka amsa da cewa, “Ina za mu gudu?” Sai ya ce da su “To, madalla.” Sannan ya ce ku sanar da ni abin da ke cikin gunkinku. Suka sanar da shi. Yayin da suka sanar da shi sai ya ce da Dunguzu, “Kai ne Sarkin Cibiri”. Ya kuma ce da Makare, “Kai ne Sarkin Gazarzawa”. Ya ce da Gamazu, “Kai ne Sarkin Kurmi.”

A zamanin Sarki Shekarau ne aka fara busa kaho ana yi masa kirari kamar haka:  “Zauna daidai, Kano garinka ce.” Ya yi mulki na tsawon shekara talatin da bakwai.

 

Mun ciro wani sashi na wannan rubutu daga: Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri, Littafi na Ɗaya. Da Kano Daga Dutsen Dala. Kano Gobernment Press, Kano.Da Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna. Da kuma shafin Intanet..