✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Takaitaccen tarihin sarakunan Haɓe na Kano (5)

A makon jiya mun kawo tarihin Sarki Abdullahi Barja dan Kanajeji da Dakauta dan Abdullahi Barja da Atuma dan Dakauta da Yakubu dan Abdullahi Barja…

A makon jiya mun kawo tarihin Sarki Abdullahi Barja dan Kanajeji da Dakauta dan Abdullahi Barja da Atuma dan Dakauta da Yakubu dan Abdullahi Barja da Muhammadu Rumfa da Abdullahi dan Muhammadu Rumfa da Yakubu dan Kisoke da Dauda Abasama dan Yakubu da Abubakar Kado dan Rumfa. A yau za mu tashi daga kan Sarki Muhammadu Shashiri ɗan Yakubu wanda ya mulki Kano daga 1573 zuwa 1582 Miladiyya.

Muhammadu Shashiri ɗan Yakubu (1573 zuwa 1582 Miladiyya)

Sunan mahafiyarsa Fatsumatu. Sarki ne mai yawan alheri, an ce a dukkan sarakunan da suka gabace shi ba wanda ya kai shi alheri.

A zamaninsa ya yaƙi ƙasar Katsina. Ya fita da nufin ko ya yi nasara ko a kashe shi kamar yadda ya ce, “Idan na fita ba zan dawo ba sai na rinjaye su, ko kuwa in mutu.” Da ya fita Katsinawa sun tare shi a Kankiya, a nan aka gwabza yaƙi, Katsinawa suka fatattaki Kanawa saboda sun fi su yawa. Amma shi da Santurakin Manya Narai da Santuraki Kuka-Zuga, da Ɗandunki ba su gudu ba. Sarki ya yi matuƙar baƙin cinki da aukuwar wannan lamari, amma su Santuraki suka lallashe shi suka ce “Kada ka yi fushi, ma rinjaye su shekara mai zuwa idan Allah Ya yarda.”

Bayan dawowarsa daga yaƙin Katsina, sai ’yan uwansa suka shirya za su kashe shi. Da Santurakin Manyan Narai ya samu labari sai ya ce Sarki, “Kada ka fita da kai da limaminka yau, in ka fita za a kashe ka”. Sarki ya zauna a gida. Santurakin Manya Narai ya je ya zauna a wurin da Sarki ke zama, masu kisa suka zaci Sarki ne, suka kashe shi tare da ’ya’yan Sarki goma sha biyu. Sauran shida kuma daga cikin ’ya’yan Sarki goma sha takwas aka kama su. Muhammadu Zaki ya yi nufin kashe su suka ce da shi, “Kada ka kashe mu, mu jikokinka ne, ka maishe mu bayinka.” Sarki Muhammadu ya yi sarautar Kano na tsawon shekara bakwai da wata huɗu da kwana ashirin da huɗu.

Muhammadu Zaki ɗan Kisoke (1582 zuwa 1618 Miladiyya)

Sunan mahaifiyarsa Hafsatu. Shi ne Sarkin da ya ci Katsina da yaƙi. Bayan hawansa karagar mulki, ya yi ɗamarar yaƙi ya fita zuwa Daura. Katsinawa suka rika kai hari duk faɗin ƙasar Kano, sannan kuma ga matsananciyar yunwa. An shiga wannan mayuwacin hali har tsawon shekara goma sha ɗaya.

Da Sarki ya ga haka sai ya tara malamai ya ce da su, “Ban tara ku domin komai ba sai domin mu yi shawara a kan abin da za mu yi mu kawar da wannan masifa.” Shehu Abubakar Bayammi ya ce da shi, “Idan kana so ka rinjayi Katsinawa, zan ba ka abin da za ka rinjaye su da shi. In har ka rinjaye su kada ka komo wannan alƙarya.” Ya ce, “Na yarda.” Ya kawo dukiya mai yawa ya bai wa Shehu Abubakar Bayammi. Shi kuma ya ba shi abin da ya ba shi. Sarki ya yi ɗamara ya fita a ranar 22 ga watan Ramalana. Ya isa Katsina ranar Idi, suna shirin fita Idi abin ya koma yaƙi. Sarkin Kano ya fattattaki Katsinawa suka watse. Kanawa suka samu ganima mai tarin yawa. Daga ciki akwai dawaki arbamiya (400) da lifida sittin da tarin dukiya da bayi. Babu wanda zai iya ƙiyasta adadin mutanen da aka kashe. Daga nan Sarki ya dawo Ƙaraye ya zauna ya rasu a can. Ya mulki Kano tsawon shekara 37 da wata biyar.

Muhammadu Nazaki ɗan Zaki (1618  zuwa 1623 Miladiyya)

Bayan hawansa karagar mulki ya aike wa Sarkin Katsina neman sulhu. Sarkin Katsina ya ƙi. Katsinawa suka fito zuwa Kano. Sarki ya tare su a Ƙaraye, ya yaƙe su suka tarwatse. Kanawa suka kwashi ganima suka koma gida.

Da shekara ta juyo, sai Sarki Muhammadu ya sake ɗaura ɗamarar yaƙi ya fita zuwa Kalam. Ya bar Wambai Giwa a gida don tsaron gari. Da Sarki ya fita sai Wambai Giwa ya ce, “Me zan yi wa sarkina domin zuciyarsa ta yi fari?” Sai aka ce da shi, “Ai sai fa ka ƙara wannan alƙarya.” Ya ce, “To”. Ya ƙara ta tun daga Ƙofar Dogo har zuwa Ƙofar Gadon Kaya, daga Ƙofar Duka-Wuya zuwa Ƙofar Kabuga, har zuwa Ƙofar Kansakali. An ce duk ranar da za a yi wannan aiki yakan fito da kaɓakin abinci dubu da shanu hamsin. Saboda haka duk jama’ar gari ke zuwa wannan aiki. Bayan an gama aikin ya zaɓi mutane alfaaini (dubu biyu) ya ba su tufafi, ya yanka shanu 300 a Ƙofar Kansakali. Sannan ya ba wa malamai sadaka mai yawa.

Bayan dawowar Sarki daga yaƙi, ya tarar da wannan aiki da Wambai Giwa ya yi. Sarki ya yi matuƙar farin ciki da wannan ci gaba da aka samu. Saboda haka sai Sarki ya ce, “Wane abu zan ba wannan mutum domin in faranta masa zuciyarsa?” Mutane suka ce, “Ai sai ka ba shi gari”. Sai ya ba shi Ƙaraye. Wambai Giwa ya tafi Ƙaraye ya yi ta yaƙar Katsinawa, ya tara dukiya mai tarin yawa da dawakai dubu da bayi ɗari. Sarki Muhammadu Nazaki dan Zaki ya yi sarautar Kano tsawon shekara biyar da wata ɗaya.

Kutumbi dan Muhammadu Nazaki (1623 zuwa 1648 Miladiyya)

Asalin sunansa shi ne Muhammadu Auwalu. Akwai matuƙar himma tare da wannan Sarki. Shi ne Sarkin da ya fara karɓar jangali (kuɗin harajin dabbobi) a hannun Fulani. Sannan kuma shi ne Sarkin da ya fara naɗa sarautar Barde Ƙerarriya.

Kasancewarsa mutum mai himma da jarumtaka, Sarki Kutumbi ya shimfiɗa mulki a ƙasar Hausa Bakwai (Kano da Daura da Rano da Katsina da Gobir da Zazzau da kuma Biram (Garun Gabas). Shi ne Sarkin da ya gina gida a Gunduwawa, saboda duk lokacin da zai fita yaƙi yakan je can ya haɗa ayarinsa, haka idan ya dawo yakan je can ya yada zango ya huta. Sarki Kutumbi ya yi yaƙi  da Bauchi sannan Katsina, amma Katsina ta gagare shi. A ƙarshe ya rasu sakamakon sukan mashi da ya samu a lokacin yaƙinsu da Katsina. Sarki Kutumbi ya mulki Kano tsawon shekara ashirin da shida.

Alhaji dan Kutumbi (1648 zuwa 1649 Miladiyya)

Sarautarsa ba ta yi tsawo ba. Ya mulki Kano na tsawon wata takwas da kwana ashirin da huɗu. Ya bar kujerar mulki saboda tuɓe shi da aka yi. Da aka tuɓe shi sai ya ƙaura zuwa Ɗanzaki. Can ya yi rayuwarsa.

Shekarau dan Alhaji (1649 zuwa 1651 Miladiyya)

Sarki Shekarau shi ne Sarkin da ya kawo ƙarshen yaƙi a tsakanin ƙasar Kano da ƙasar Katsina ta hanyar sulhu. An saka manyan malamai a gaba irin su Shehu Atuman da Malam Bawa da Liman ’Yandoya. A cikin jawabinsa Shehu Atuman ya ce, “Wanda ya fara kisan wani tsakaninku ba zai samu nasara ba in Allah Ya so, har Ranar Kiyama.”  Shi ma sarautarsa ba ta yi tsawo ba, ya yi sarautar Kano tsawon shekara ɗaya da wata bakwai da kwana ashirin da huɗu.

Kukuna dan Alhaji (1651 zuwa 1652 Miladiyya)

Shekararsa ɗaya a kan karagar mulkin Kano. Madawakinsa ne ya tuɓe shi ya naɗa dan shaƙiƙiyarsa Fatsumatu. Ana ce da ɗan nata So-yaƙi. Sarki Kukuna ya bar Kano ya koma Zazzau bayan an tuɓe shi.

So-yaƙi dan Shekarau (652 Miladiyya)

Sunan mahaifiyarsa Fatsumatu kamar yadda aka ambata. Watansa uku kacal a kan karagar mulkin Kano aka tuɓe shi. Bayan tuɓe shi wata ’yar tarzomar yaƙi ta so ta tashi tsakanin mutanen Kano ƙarƙashin jagorancin Madawakin Kano. An gina wa Sarki So-yaƙi gida a Dukurawa ya tare a can.

Bawa dan Muhammadu Kukuna 1660 – 1670 Miladiyya

Sarki Bawa, malami ne, adali kuma mai nagarta. Ya mulki Kano cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali, ba yaƙi a ciki da wajen Kano. Shi ne Sarkin da ya gina Goron Fagaci, shi ya sassaƙa Kujera ya ajiye ta a zauren Turakin Manya, shi ya gina Soron Dikko, duk a cikin gidan Sarki. A zamaninsa wani makarancin Alƙur’ani, Malam Abdullahi ya zo Kano. Kuma Allah Ya yi masa baiwa da murya saboda haka aka gina masa ɗaki a ƙofar zauren Turakin Manya yana ɗebe wa Sarki kewa da karatun Alƙur’ani da daddare sannan yana yi amsa wa’azi a cikin watan azumi har watan ya ƙare. Bayan rasuwar Ɗan Lawan, Sarki ya ce da Malam Abdullahi “Kai ne Ɗan Lawan.” Sannan ya sa shi cikin masu kiran Sallah a birnin Kano. Sarki Bawa ya yi sarauta ta tsawon shekara goma da wata huɗu da kwana ashirin.

Daɗi dan Bawa (1670 – 1703 Miladiyya)

Sarki Daɗi ya yi nufin ƙara faɗin garin Kano a lokacinsa amma mashawartansa suka ce da shi kada ya yi, kuma ya haƙura. Haka nan Sarki Daɗi ya yi nufin fita waje don ya yi yaƙi da Kwararrafawa a nan ma mashawartansa suka hana shi fita. Yana nan zaune cikin gari wata shekara sai Kwararrafawa suka shigo Kano ta Ƙofar Gadon Ƙaya. Suka rika kashe jama’a har sai da suka kai Bakin Ruwa. Da labari ya ishe Sarki maza-maza Sarki ya ɗaura ɗamarar yaƙi ya tare su a Jakara ya yi ta kisansu har sai da ya fatattake su. Daga nan kuma sai ya wuce Daura ’yan sauran Kwararrafawan da suka rage suka bi shi har sai da suka je Jalli sannan suka juyo.

Haka nan a zamanin Sarki Daɗi ne Sarkin Gaya Farin-Dutse ya kangare ya ƙi bada kuɗin haraji har tsawon shekara uku. Daga baya Sarki ya hilace shi ya kama shi ya kashe, sannan ya naɗa Sarkin Dawaki Duba a matsayin Sarkin Aujara. Sarki Daɗi ya yi sarauta na tsawon shekara  talatin da uku da wata takwas sannan ya rasu.

Mun ciro wani sashi na wannan rubutu daga: Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Gobernment Press, Kano.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna. Da kuma shafin intanet. Za mu ci gaba.