✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Takaitaccen tarihin sarakunan Haɓe na Kano (6)

A makon jiya mun kawo tarihin Sarki Muhammadu Shashiri dan Yakubu da Muhammadu Zaki dan Kisoke da Muhammadu Nazaki dan Zaki da Kutumbi dan Muhammadu…

A makon jiya mun kawo tarihin Sarki Muhammadu Shashiri dan Yakubu da Muhammadu Zaki dan Kisoke da Muhammadu Nazaki dan Zaki da Kutumbi dan Muhammadu Nazaki da Alhaji dan Kutumbi da Shekarau dan Alhaji da Kukuna dan Alhaji da So-yaki dan Shekarau da Bawa dan Muhammadu Kukuna da Dadi dan Bawa. A yau za mu tashi daga kan Sarki Muhammadu Sharif dan Dadi wanda ya mulki Kano daga 1703 zuwa 1731 Miladiyya.

 

Muhammadu Sharif  dan Daɗi (1703 – 1731Miladiyya)

Sunan mahaifiyarsa Maryam ’yar Sarkin Gaya Farin Dutse. A lokacinsa Gayawa suka samu ɗaukaka.

Sarki Muhammadu shi ne Sarkin da ya fara karɓar harajin wata-wata a Kasuwar Kurmi. Shi ne Sarkin da ya yaƙi Ƙiru. An ce ya tura Wambai Duba ne shi kuma da ya je ya maida Ƙiru toka, ya kwashi ganimar bayi da dawaki da sauran nau’o’in dukiya. Sannan a lokacin Sarki Muhammadu ne Zamfarawa suka ci Kano da yaƙi. An gwabza wannan yaƙi a ’Yargaya, Zamfarawa suka fatattaki Kanawa.

Sarki Muhammadu shi ne Sarkin da ya gina birnin Gaya ta hannun Sarkin Gaya Janhazo. Shi ne ya gina birnin Takai da Tsakuwa da Dawaki. Sarki Muhammadu ya mulki Kano tsawon shekara ashirin da takwas da wata goma.

Alhaji Kabi dan Kumbari (1743 – 1752 Miladiyya)

Sunan mahaifiyarsa Zainabu. Sarki Alhaji Kabi Sarki ne mai kwarjini da son yaƙi. Tunda ya hau gadon sarauta bai taɓa zama gida na tsawon wata biyar ba, kullum yana fagen fama.

A zamanin Sarki Kabi ne Gobir ta sake cin Kano da yaƙi. Saboda tsananin son yaƙinsa an yi ittifaƙi cewa ba wanda ya san adadin yaƙuƙuwan da ya yi. An ce shi ne Sarkin da ya fi kowa yawan yaƙe-yaƙe a sarakunan Kano. Sarki Kabi ya mulki Kano tsawon shekara tara da wata bakwai kafin Gobirawa su kashe shi a fagen yaƙi.

Yaji dan Daɗi (1753 – 1768 Miladiyya)

Sunan mahaifiyarsa Maryam. Sarki Yaji dan Daɗi Sarki ne mai adalci da nagarta. Saboda wannan dalili ne ma ya sa matansa suke kiransa da “Malam Lafiya.” Iya tsawon mulkinsa ƙasar Kano ta zauna cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali. Ba yaƙe-yaƙe, ba takurawa. An samu yawaitar mutane masu yin hijira zuwa birnin Kano a zamaninsa. Har ya yi sarauta tsawon shekara goma sha biyar da wata goma Kano ba ta taɓa yaƙi ba.

Babba Zaki dan Yaji (1768-1776 Miladiyya)

Shi kuma Sarki ne mai hikima da sanin tarihi. Sannan fasihi mai kula da jama’a.

Sarki Babba Zaki ya yaƙi Auyo a zamanin Sarkin Auyo Abubakar har sai da ya kusa shiga cikin garin Auyo. Sannan ya yaƙi Burumburum har sai da ya shiga cikinta. Ƙi-da-so ya zama jama’ar Burumburm suna yi masa yaƙi yana nan ko baya nan. A dalilin haka ne ma ake yi masa kirari da “Jan-Rina- Gasa-Giwa.”

A zamanin Sarki Babba Zaki aka fara aiki da bindiga a dukkan sarakunan Kano. Yana da ɗabi’un da suka yi kama da na Larabawa.

Sarki Babba Zaki ya gina gida a Takai, har sai da aka zaci kamar ma zai koma can da zama. Amma daga baya Kanawa suka roƙe shi ya dawo cikin gari. Yana da manyan jarumai guda biyar masu ɓarin wuta da suka hada da: Sarkin Sankara Nagarki da Sarkin Bebeji Dambo da Sarkin Majiya Kimfirmi Makaman Baubawa da Sarkin Jarmai Acur da kuma Sarkin Dawaki Maiza. Sarki Babba Zaki ya mulki Kano tsawon shekara takwas kafin ya rasu.

Dawuda Abu-A-Sama dan Yaji (1776 – 1781 Miladiyya)

Shi ne sarki mai kyan hali da kyan fuska. Sarki ne da Allah Ya yi wa kyakkyawar sura ga kuma kyakkyawan hali da kunya ga kuma kawaici da haƙuri da kuma kyauta. Sarki Dawuda Sarki ne abin so ga mutane, ga kuma kyauta da cika alƙawari, sannan ga shi sadauki. Ya mulki Kano tsawon shekara biyar cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma ƙaruwar arziki. Har rayuwarsa ta ƙare duk abin da zai yi sai ya yi shawara.

Muhammadu Alwali dan Yaji (1195 – 1222 Hijira; 1781 – 1807 Miladiyya)

Shi ne Sarki na ƙarshe a jerin sarakunan gidan Rumfa. A hannunsa Fulani suka karɓi sarauta.

Tun kafin Fulani masu jihadi su fatattake shi sai da ya samu yunwa a lokacinsa. Da Fulani suka zo ƙwatar mulki a hannunsa sai ya gudu ya nufi Zazzau. Da ya shiga Zazzau sai Zazzagawa suka tambaye shi, “Me ya rabo ka da Kano?” Sai ya amsa musu da cewa, “Abin da ya fito da ni daga cikinta ku ma ya fisshe ku, idan Allah Ya yarda. Na ga gaskiya da idona, na fito domin tsira da raina, ba domin iyalina da dukiyata ba.” Zazzagawa suka kore shi domin muguwar maganarsa, ya fita ya tafi Rano, Fulani suka bi shi, ya fita zuwa Burumburum suka sake bin sa can suka kashe shi.

Sarki Muahammadu Al-Wali ya mulki Kano tsawon shekara ashirin da bakwai kafin a kashe shi a Burumburum.

 

Sarakunan Habe suka fara gina kasuwa a Kano

Kasuwar Kurmi, kasuwar duniya ce a Kano. Ita ce kasuwa mafi daɗewa a ƙwaryar birnin Kano da kewayenta. Kusan ana iya cewa ita ta haifar da dukkan kasuwannin Kano. Abu ne mai matuƙar wahala a iya iyakance lokacin da aka fara cinikayya a wannan kasuwa.

Sarkin Kano Muhammadu Rumfa ne ya fara kafa rumfuna a kasuwar tare da fara karɓar haraji (Ƙwalli, 1996; tattaunawa da Sarkin Kasuwa, 2019).

Sarkin Kano Abdullahi Bayero (1926 – 1953), shi ya sabunta kasuwar ya zamanantar da ita. Ya yi mata tashar jakuna; wannan tashar jakuna yanzu babu ita sai dai gurbinta da aka gina masallacin da ake kira Masallacin Shabbabu a wurin. Ita kuwa tashar jakai kewaye ne aka yi wanda duk mutumin da ya kawo kayansa a jaki yakan tafi wannan tasha ya ɗaure jakinsa har zuwa lokacin da zai gama cin kasuwarsa ko kuma ya sayi abin da ya kawo shi. Akwai rijiyoyi da aka tottona a cikin wannan tasha domin shayar da jakuna.

Bayan wannan kuma ya gina rumfunan kasuwa na zamani da kotu da ofishin ’yan sanda da ofishin aikewa da sakonni da sauransu. Haka kuma ya gina tashar mota da aka fi sani da Tashar Jakara duk domin wannan kasuwa da kuma walwalar ’yan kasuwa.

Kasuwar tana nan a tsakiyar birnin Kano. Akwai unguwanni da suke zagaye da ita irin su Jakara da Bakin Zuwo da Kwanar Goda da Ƙofar Wambai da sauransu. Dukkan waɗannan unguwanni ana kiransu da Bakin Kasuwa a dunƙule.

Haƙiƙa wannan kasuwa ta bada muhimmiyar gudunmawa wajen ci gaban Kano ta fuskar tattalin arziki da ƙaruwar jama’a. Saboda a kowane lokaci akan samu waɗanda za su zo da nufin kasuwanci amma sai su yi ‘Zuwan Sojan Badakkare.’

Duk da cewa wannan kasuwa har yanzu tana da rumfuna irin na da, to amma tana da zubi mai kyau, sannan a tsare take daki-daki. Misali, akwai rukuni guda na masu sayar da littattafai zalla da ake kira ’Yan Littattafai. Akwai kuma layi guda na masu sayar da kayan adon dawaki, akwai layin masu sayar da turare. Akwai kayayyakin da ake shigowa da su irin su turare da ma wasu kayayyakin mutanen Nijar. Sannan za ka ga namu na gargajiya.

A zamanin Turawa an yi wa wannan kasuwa gyaran fuska daga asalin yadda take. Sannan kamar idan ka zo bakin hanya akwai gini irin na zamani. Musamman ’Yan Littattafa.

Kayayyakin da ake sayarwa

Kusan a dunƙule ana iya cewa da wuya ka nemi wani abin masarufi a wannan kasuwa ka rasa, amma duk da haka kasuwa ce da ta shahara wajen sayar da kayayyakin gargajiya da suka haɗa da saƙe da ake yi wa laƙabi da Farin Kano; kayan adon dawaki, kayan yaji ko kuma kayan ƙanshi da suka haɗa da citta da kanamfari da masoro da sauransu. Suturar gargajiya da suka haɗa da manyan riguna da alkyabba  da wundiya da sauransu; da kayan yaƙi da suka haɗa da takubba da sulke da saurnasu da kayan ado na fata da suka haɗa da matashi da hula da jaka da sauransu da sinadarin haɗa turaren wuta da na ruwa da sauransu; sai kayan adon mata da suka haɗa da yari da tsakiya da murjani da dutsen wuya da sauransu da madubi da tozali da sauransu; sai kuma litattafai waɗanda kana iya cewa kusan yanzu su ne ma mafi rinjaye a hajar kasuwar. Akwai kuma kayayyaki irin su goriba da ɗinya da kanya da zogale da sauransu; sannan akwai kayan ƙere-ƙeren gargajiya irin su fartanya da murhu da wuƙa da sauransu.

Abokan hulɗa

Kasuwar Kurmi kasuwa ce ta duniya. Daga wannan kasuwa akwai cuɗanyar cinkayya da kusan dukkan ƙasashen Afirka. Kaɗan daga ciki akwai Ghana da Burkina Faso da Nijar da Mali da Sudan da Libiya da Kamaru da Chadi da sauransu.

A nan muka kammala kadan daga cikin tarihin sarakunan Habe na Kano.

Mun ciro wani sashi na wannan rubutu ne daga: Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Gobernment Press, Kano.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna. Da kuma shafin intanet.