✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Takara Haram ga talaka

A halin yanzu dai jam’iyyun siyasa a kasar nan sun fara sayar da takardun tsayawa takarar mukamai daban-daban, sai dai kuma ga dukan alamu ba…

A halin yanzu dai jam’iyyun siyasa a kasar nan sun fara sayar da takardun tsayawa takarar mukamai daban-daban, sai dai kuma ga dukan alamu ba a bukatar talaka ya shiga sahun masu son takarar saboda tsawwala kudin fom din da suka yi.

Jam’iyyar APC dai ta sanya fom din takarar Shugaban kasa a kan Naira miliyan 45, masu son tsayawa takarar Gwamna kuma za su biya Naira miliyan 25 da dubu 500, su kuma masu son tsayawa takarar Sanata za su biya Naira miliyan 7,  na Majalisar Wakilai kuma za su biya Naira miliyan 3 da rabi, masu son takarar majalisun dokoki na jihohi kuma za su biya Naira dubu 750 su karbi fom din.

Ita kuma Jam’iyyar PDP ta sanya Naira miliyan 12 ne a matsayin kudin fom din dan takarar Shugaban kasa, Naira miliyan 6 kuma na Gwamna, kujerar Sanata kuma Naira miliyan 3 da rabi, ta Majalisar Wakilai kuma Naira miliyan 2 da rabi, sannan ta majalisun  jihohi kuma za a biya Naira dubu 600.

A zaben shekarar 2015 APC ta karbi Naira miliyan 27 da rabi ne daga dan takarar Shugaban kasa, Naira miliyan 10 kuma a wurin dan takarar Sanata. Ita kuma PDP ta karbi Naira miliyan 22 ne a wancan lokacin daga dan takarar Shugaban kasa, a yayin da dan takarar Gwamna ya biya Naira miliyan 11 aka ba shi fom din takara.

A cewar Kakakin Jam’iyyar APC Yekini Nabena lokacin da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labarai na AFP, jam’iyyarsu ta tsauwala kudin ne domin ta samu damar gudanar da yakin neman zabe ba tare ta yi maula a wurin masu hannu da shuni ba. Ya kara da cewa, “Siyasa harka ce mai matukar muhimmanci da bai kamata a yi sakaci da ita ba, idan dan takara ba ya da kudin sayen fom idan har yana da farin jinin magoya bayansa za su tattara kudi su saya masa.”

Haka kuwa aka yi, domin kuwa an wayi gari wata kungiya mai suna “Nigerian Consolidation Ambassadors Network (NCAN), ta bayyana cewa ta saya wa Shugaba Buhari fom din takara na Naira miliyan 45, inda Shugabanta Sanusi Musa ya ce sun samu kudin ne ta hanyar karo-karo a tsakanin ’ya’yan kungiyar tasu.

Ya kamata Shugaba Buhari ya sanya a kama shugabannin wannan kungiya domin a tuhume su, su yi bayanin shin kungiyar tasu tana da rajista, kuma su wanne ne da wane ne ’ya’yanta, kuma wane aiki suke yi, ta yaya suke samun kudinsu? Yin haka ya zama wajibi ga Shugaba Buhari domin ya nuna wa duniya cewa yakin da yake yi da cin hanci da rashawa da gaske ne kuma ba sani, ba sabo, kamar yadda ya bayyana a jawabinsa na ranar 29 ga watan Mayun 2015 bayan an  rantsar da shi. A lokacin ya bayyana  cewa “Kowa nawa ne, amma ni ba na kowa ba ne.” Domin wannan fom din da aka saya masa ya yi kama da toshiyar baki, wato akwai wata manufa ta boye.

Wannan fom din yana iya jawo wa Shugaba Buhari matsala, domin ana iya kai shi kotu bisa zargin ya saba wa dokar zabe wadda ta ce kada dan takara ya karbi taimakon fiye da Naira miliyan daya daga mutum guda. Idan aka yi ta tafka shari’a har zuwa Kotun koli kuma kotun ta tabbatar da cewa an saba doka, shi ke nan za a rusa zabensa, ko da ya dade da cin zaben. Saboda haka da muguwar rawa gara kin tashi, zai fi kyau Shugaba Buhari ya guji duk wani abu da zai haifar masa da matsala a yayin da yake kokarin sake tsayawa takara karo na biyu.

Haka kuma barin wadansu su rika saya wa dan takara fom alhali yana kan kujerar gwamnati zai sanya a yi zargin cewa wata dabara ce aka shirya domin a yi amfani da kudin gwamnati a saya wa dan takara fom ta hanyar amfani da sunan wasu kungiyoyi.

Bayan Shugaba Buhari da wata kungiya ta ce ta hada kudi Naira miliyan 45 ta saya masa fom, an kuma samu wasu kungiyoyi a Jihar Kaduna da suka ce sun hadu sun saya wa Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i fom domin ya tsaya takarar Gwamnan Jihar. Matukar ba a dauki mataki ba kafin a rufe karbar fom din, Allah ne kadai Ya san yawan masu manyan mukaman gwamnati da wadansu za su ce sun saya musu fom.

Wani abin mamaki kuma shi ne yadda Jam’iyyar APC ta tsauwala kudin fom din tsayawa takara a wannan karo, alhali jam’iyya ce da ke nuna cewa ta kowa da kowa ce, “All People Congress.” Amma sai gashi tana bai wa masu kudi fifiko fiye da talaka.

Sanin kowa ne cewa babu yadda za a yi ma’aikacin gwamnati ko mai karamin karfi ya iya hada wannan kudin cikin sauki, sai dai wanda ya kauce wa hanya, wato mara gaskiya. Yanzu Jam’iyyar APC ta toshe wa mutane masu gaskiya da rikon amana kofar samun damar bayar da gundunmawarsu, sai wadanda suke da karfi ne kawai za su iya tsayawa takara.

Hujjar da Kakakin Jam’iyyar ya bayar cewa idan dan takara yana da farin jini magoya bayansa za su taimaka masa da kudi ya sayi fom din ba mai gamsarwa ba ce, domin hakan zai bayar da dama ga wadansu masu hannu da shuni ne su mallake dan takarar, ta yadda idan ya ci zabe zai zama sai yadda suka yi da shi, wato su ne za su rika juya shi. Shi kansa dole ya rika raga musu, domin Hausawa na cewa ‘Idan baki ya ci, dole ido ya ji kunya.”

Kamata ya yi Jam’iyyar APC ta zama kowa nata ne, mai rauni da mai karfi. Amma wannan kudi da ta tsuga ya nuna cewa tara makudan kudi ne ta sanya a gaba, ba samar da shugabanci nagari ba.

Ya kamata Jam’iyyar APC da sauran jam’iyyun  kasar nan su fi mayar da hankali wajen samun dan takara da yake da gaskiya da rikon amana kuma mai mutunci da sanin ya kamata ga kuma ilimi, maimakon su mayar da hankali ga masu karfin aljihu kawai. 

A zaben shekarar 2015 Jam’iyyar PDP ta yafe wa mata da ke son tsayawa takara kudin sayen fom, inda ta rika ba su fom din kyauta. Nakasassu kuma aka yi musu ragi. Kamata ya yi yanzu a kara jawo talaka a jika ta yadda zai iya neman kowane irin mukami a kasar nan tunda a kullum dimokuradiyyar kasar kara bunkasa take yi. 

A halin yanzu dai saboda tsauwala kudin fom din takara da manyan jam’yyu suka yi sun haramta wa talaka mai karamin karfi tsayawa takara ke nan, sai dai ya mara wa mai kudi baya koda ba mai gaskiya da rikon amana ba ne, wato dai lamarin ya zama jari hujja tsantsa ke nan.