✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Takobi ne asalin sarautar ‘Kanwa’ a Masarautar Katsina – Kanwan Katsina na III

Mafi yawan taken wasu masarautu a kasashen Hausa sukan samo asalin sunansu ta sanadiyar yaki ko wata jarumta da makamantansu. Sarautar Kan-Wa a Masarautar Katsina…

Mafi yawan taken wasu masarautu a kasashen Hausa sukan samo asalin sunansu ta sanadiyar yaki ko wata jarumta da makamantansu. Sarautar Kan-Wa a Masarautar Katsina na cikin sarautun da suka samu ta irin wannan  hanya inda aka ba ta hakimi a dalilin jarumta:

 

Kanwan Katsina na daga cikin sarautu na hakimci. Sarauta ce wadda ta samo asali daga wani jarumi a fagen fama ta kuma sanadiyyar takobin da yake yaki da shi. Kanwan Katsina na III wanda kuma tsohon Kwanturolan Hukumar Kwastam ne da ke rike da wannan sarauta ta Hakimi tun kafin ajiye aikinsa, Alhaji Usman Bello Kankara MNI ya yi wa Aminiya cikakken bayanin yadda wannan sarauta ta Kanwa take da kuma gidan Kanwa na Farko da ke Kofar ’Yandakan Lantarkin Malam Mudi a cikin garin Katsina. “Kamar yadda muka samu tarihin ita wannan sarauta, ta samo asali ne daga kakanmu Nuhu Nadabo.  Nuhu Nadabo yana daga cikin mayakan da ake ji da su  a lokacin da ake yaki. Sun fita yake-yake da su Danwaire da Kaura da sauransu. Shaharar Kanwa Nuhu Nadabo a fagen yaki ta fara fitowa ce a lokacin mamayar da ’Yandoton Tsafe da ke Jihar Zamfara a yanzu ya yi wa kasar Pauwa wadda take Ketare, alhali wannan yanki yana karkashin masarautar Katsina ce. Mutanen yankin suka zamo ba su biyayya ga masarautar Katsina, wato suka bijire har lokacin da Sarki Dikko yake sarauta. To ganin irin taurin kai da bijirewar da Sarki Dikko ya lura da ita ga wadannan mutane wadanda ’Yandoton Tsafen ya mamaye, sai Sarki Dikko ya kira  Kanwa Nuhu ya ce, yana so ya je ya maido wadannan mutane bisa hanya, ya gyara musu zama tare da karbo kudaden haraji da jangali da suka ki biya a can baya. Haka kuwa aka yi, Kanwa ya je ya aiwatar da umarnin sarki ya kuma zo da kudaden,” inji Kanwa Usman Bello.

Alhaji Usman Bello Kankara MNI Kanwan Katsina III

To ko ina wannan suna na Kanwa ya fito har ya zama sarauta? Kanwa Usman Bello ya yi karin bayani cewa: “Shi wannan suna ya fito ne ta dalilin takobin Nuhu Nadabo. A wancan lokaci in an je fagen daga, yana amfani da wannan takobi domin fille kawunan abokan gaba. To idan suka yi nasarar wannan yaki, yakan daga wannan takobi sama ya yi tambaya, ‘Kan Wa?’ Ma’ ana, yanzu ‘Kan-Wa’ yake so a sauke masa shi kasa, ba kanwa da ake jikawa don yin magani ko zuba ruwanta don dama garin danwake da sauran girki ba. To daga nan ne wannan suna ya samo asali. Kuma kamar yadda muka samu labari, idan yaki ya yi zafi, Kanwa Nuhu bai damu da harbin kibiya ba domin ko an harbe shi da ita zai zare ta ce ya ci gaba da sarar kawunan abokan gaba da wannan takobi nasa mai baki biyu da kuma tsini biyu.”

Ya kara da cewa: “Idan muka koma ga batun mutanen Pauwa, bayan Kanwa Nuhu ya ci su da yaki ya kori mutanen ’Yandoton Tsafe ya kuma kawo wa Sarki kudaden da suka ki biya, sai Sarki Dikko ya ce, yana so Kanwa Nuhu ya tashi daga wannan gida da ke nan Lantarkin Malam Mudi ya koma kasar Pauwa ya zauna don ya shugabance su, sannan  zai hana sake dawowar mutanen Tsafe da sake bijirewar mutanen. Kanwa ya tafi Pauwa kamar yadda aka umarce shi. Kuma zuwansa can ne ya assasa wannan gari na Kankara na yanzu.”

“To lokacin da ya koma garin Pauwa ya samu ana matsalar ruwan sha a garin wanda hakan yana sa mutanen garin da dabbobinsu shiga cikin wani hali. Bayan ganin halin da ake ciki sai ya dawo wajen Sarki domin neman izinin baro garin Pauwa zuwa Kankara domin nan ya fi ruwa. Sarki Dikko ya amince ya kuma dawo Kankara. A nan kuma aka sake wa sarautar suna, ya koma Sarkin Pauwan Katsina Hakimin Kankara, aka baro Ketare,” inji shi.

Ya kara da cewa: “Shi Kanwa Mudi a baya, Sarkin Pauwa a yanzu yana da ’ya’ya. Abdullahi shi ne babban dansa, akwai Malam Mudi wanda aka sanya wa waccan unguwa sunansa, wato Lantarkin Malam Mudi. An ce ko don yana zama a wajen turken lantarkin ne in ya dawo daga aiki ya sa aka yi wa wurin suna da shi. Shi Abdullahi shi ne mahaifin Babana Bello. Shi Kakana Abdullahi bai yi sarautar Pauwa ba sai dai wakilci har na tsawon shekara 11, amma Allah bai ba shi sarautar ba sai aka ba, Mudi, domin a lokacin Mudi yana aiki da Turawa a Ma’aikatar Safiyo kuma yana jin Ingilishi amma kuma bai dade ba aka cire shi. Ana nan, har aka kirkiro Jihar Katsina a 1987 zamanin marigayi Sarki Kabir Usman Nagogo. Sai aka kara yin wadansu hakimai a Masarautar Katsina domin kara matso da talakawa ga shugabanninsu. A nan ne aka raba Kankara gida biyu, wato ita Kanƙarar da kuma Ketare.”

Basaraken ya tuno cewa mahaifinsa Alkali Bello ya taba neman wannan sarauta ta Sarkin Pauwa amma Allah bai sa ya samu ba. To ganin cewa, ga wata damar ta sake samuwa sai ya sake neman wannan sarautar. “Suna da yawa wadanda suka nemi wannan sarauta ta Gundumar Ketare, don sun kai wajen mutum 14, kuma aka yi sa’a a lokacin mahaifina ya riga ya ajiye aiki ya dawo gida Kanƙara da zama. Allah da naSa ikon sai aka ba shi wannan sarauta ta Ketare amma da sunan, “Ɓinonin Katsina,” kamar yadda aka rubuto masa daga fada.  To ka san sarakuna ko hakiman da suka fito daga gidanmu sun hada da na Bakori da Ɗanja da Tsiga da Kankara da  Ketare, dukkansu ciki daya. Shi Nuhu Nadabo wa ne ga Makaman Bakori Idris Nadabo,”  inji Kanwan na III.

Kanwan ya bayyana yadda aka yi sunan sarautar ta Kanwa ta sake dawowa daga sunan Ɓinoni. “To bayan an bayar da waccan sarauta a nan Ketare da wancan suna ga mahaifina, sai ’yan uwa aka hadu aka taho Katsina don yi wa Sarki godiya. Sun samu marigayi Sarki Kabir a can gonarsa da ke Kurmiyal bisa hanyar Batsari. Bayan sun yi godiyar sai Sarki Kabir ya ce, shi ma yana yi musu godiya a kan damar da suka ba shi ya sauke wani nauyi da mahaifinsa Sarki Usman ya dauka. Saboda mahaifin Alkali Bello ya taba nuna wa Sarki Kabir wata takarda da shi Sarki Usman ya rubuta ya ba shi a lokacin da ya nemi waccan sarauta ta farko. Sarki Usman ya ba shi hakuri kan cewa akwai gaba na nan zuwa, to yau kuma ga wannan gaba ta zo, shi ne kuma Allah Ya ba damar sauke wancan nauyi. Bayan an gama wannan godiya har ila yau, sai ’yan uwan suka sake mika  kokon bararsu a nan take, suka ce ba su raina sunan waccan sarauta ta Ɓinoni ba, amma suna rokon Sarki a maido musu da sunan waccan sarauta ta kakanmu Kanwa. Nan take Sarki ya amince. Aka sa Sakataren Majalisa ya sake rubuta wata takardar da sunan ‘Kanwan Katsina Hakimin Ketare’ an yi haka a 1992. Kaga ke nan mahaifina ya zamo Kanwa na II baya ga na 1 Kanwa Nuhu.”

Ga shi yanzu ba lokacin yaki ba ne, ko yaya sarautar ta juya ga al’umma? Kanwa Alhaji Usman ya ce, “Mahaifina Kanwa Bello Abdullahi ya shiga aikin gina kasa inda sarautar ta tashi daga matsayin Magaji zuwa Hakimi. Yayi kokarin kawo asibiti da makaranta da sauransu a wannan yanki na Ketare. Sannan ya yi kokarin hana rikicin makiyaya da manoma ta hanyar fidda wa makiyayan burtali. Zamansa na alkali ya san duk irin wadannan matsaloli.

Ban mantawa, akwai wani manomi a yankin da ya ci burtali, shi da kansa ya zo ya zauna sai da aka fitar da hanyar kamar yadda take. A haka ya ci gada da tafiyar da mulki har Allah Ya karbi abinSa.”

Ke nan ka gaji mahaifinka ne bayan rasuwarsa? Sannan ina batun aikin kayan sarki na Kwastam da kake yi, ko kana cikin aikin aka ba ka sarautar ko sai bayan ka ajiye aiki? Tsohon Kwanturolan Kwastam din ya ce, “An ba ni wannan sarauta ina cikin aiki wadda marigayi Sarki Kabir ya ba ni. A lokacin da aka ba ni sarautar Sarki ya ce in ci gaba da aikina har sai bayan na ajiye. Domin in na ajiye aiki a wancan lokaci tamkar Katsina ce ta yi asara domin gurbinta ne za a saki. Saboda haka na ci gaba da aikina can kuma an sanya wanda zai yi wakilci. Amma duk da haka, aikin bai hana ni zuwa gida domin in duba halin da jama’a suke ciki ba. Kuma duk Hawan Sallah idan ya zo da ni ake yi.” Kanwan na III wanda ya yi digirinsa a fannin siyasa da tarihi a Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya a 1981 kuma hakan ya ba shi damar shiga aikin Kwastam, ya kara haske a kan yadda ya rika gwama aikinsa na gwamnati da kuma na masarauta. “Kamar yadda na shaida maka da farko, duk wata sai na zo gida kuma na zagaya kasata. Sannan na samu kyaututtuka daga Masarautar Katsina a kan irin yadda nake yin tsari mai kyau a lokacin Hawan Sallar. A nan ma nake so in kara yin godiya ga wadannan sarakuna biyu, wato marigayi Sarki Kabir wanda ya daga mini na ci gaba da aikina yayin da wanda ya gaje shi Sarki na yanzu Alhaji Abdulmumini Kabir ya ci gaba da daga mini kamar yadda ya gada har sai da na ajiye aiki, wato na cika shekara 35 ina aiki kuma na ajiye aikin da mukamin Kwantarola. An yi mini nadin sarautar a ranar 4 ga watan Nuwamban 2000,” inji shi.

Bayan zagaye-zagayen aiki da aka yi har zuwa lokacin ajiyewa a dawo gida. Me aka tunkara? Sarauta dai ba aikin gwamnati ba ce. Talakawa na da bukatu da yawa daga wajen masu yi musu mulki musamman na gargajiya domin shi suka fi sani. Mayakin zamani Kanwa na III Alhaji Usman Bello ya ce, “To ka ga dai an fara koyon mulki tun daga makaranta har ta kai ga wajen aiki. Sannan an tashi cikinsa a gida, abin da kawai ya rage shi ne, yaya za a ciyar da al’ummar gaba.” To na dai ajiye aiki a cikin watan Mayun 2017 na dawo gida. Babban abin da na fara yi shi ne, tsara jadawalin yadda zan yi rangadin kasata. A haka ne na gano irin bukatun jama’ata, don wadansu hanya suke bukata wadansu asibiti, wadansu kuma makaranta da sauransu. Bayan na gama rangadi tare da tattara wadannan bayanai, sai na zauna na rubuta abin da duk na gano daki-daki. Sai na fara daukar batun ilimi, na rubuta takarda zuwa ga Ma’aikatar Ilimi ta Jiha da kuma Hukumar Ilimi Bai-Daya ta Jiha, in takaita maka yanzu haka ana can ana aiki a Pauwa da Tsamiyar Jino. Sannan ga firamare ta U. K. Bello da Daneji da Kuka-sheka da sauransu duk ana yi musu gyara. Daga maganar makarantu sai kuma batun ruwan sha. Nan ma na je Hukumar RUWASSA inda na nemo wa jama’a rijiyoyi, an gina wasu wasu kuma an yi masu gyara.”