✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Takurar wuri ta tilasta dauke kasuwar timatir daga Tambuga

An dauke kasuwar tumatir ta Benin daga inda aka san ta a Tambuga zuwa unguwar Aduwawa saboda matsi da takurar wuri da kuma amincewar shugabanni…

Wani yanki na sabuwar kasuwar tumatir da aka bude a Aduwawa ta garin Benin  An dauke kasuwar tumatir ta Benin daga inda aka san ta a Tambuga zuwa unguwar Aduwawa saboda matsi da takurar wuri da kuma amincewar shugabanni da sauran ’yan kasuwa.
’Yan kasuwa masu saye da sayar da timatir da sauran wadansu kayayyakin lambu,  wadanda suke Hausawa ne ’yan asalin Arewa mazauna garin Benin, wadanda kuma su ne kashin bayan kasuwar, sun amince da wannan sabon canji.
Alhaji Sani Abdullahi, shugaban ’yan kasuwar ya fadi cewa, “sama da shekaru talatin muke gudanar da wannan sana’ar ta kasuwar timatir a nan cikin garin Benin, amma da wuri ya kure ya takura, sai aka tashe mu muka dawo kasuwar Tambuga cikin yankin Ute, inda mun yi kusan shekaru biyar muna kasuwa a wurin. A nan ma sai muka ga filin ya matse muna a takure, lamarin da shi ne babban dalilin tashin da muka yi daga kasuwar ta Tambuga muka dawo nan Aduwawa. Alhamdulillahi kuma alal hakika, mun fara ganin hasken wurin domin mun samu hadin kai daga shugabannin wurin”.       
Alhaji Sani ya yi godiya ga shugabannin jihar ta Edo kan yadda suke mutunta wa ’yan Arewa mazauna jihar.