✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Talaka bawan Allah 

Ni tunanina shi ne, tunanin dan siyasa inda ya tsaya shi ne ya ci gaba da mulkar talaka har mutuwarsa, amma wani taro da wata…

Ni tunanina shi ne, tunanin dan siyasa inda ya tsaya shi ne ya ci gaba da mulkar talaka har mutuwarsa, amma wani taro da wata kungiya me suna “Kano Youth Political Forum” ta yi a dakin taro na Mambayya dake nan Kano ya chanza min tunina gaba daya.

Taro ne da manyan ’yan siyasa na Jihar Kano har ma da Jihar Kaduna suka samu damar halarta. Ni dai da wayona ko a labari ban taba ji ko ganin inda wata kungiyar matasa ta tara ’yan siyasa haka ba, kuma na duka manyan jam’iyun kasar nan sai wannan rana.

Amma watakila ko domin saboda ‘ya’yansu suka hada taron? Kaso 90 na shugabannin wannan kungiyar ’ya’yan manyan ’yan siyasa ne a wannan jiha tamu ta Kano, har a dan binciken da na yi na gano cewa idan mahaifinka ko mahaifinki bai taba rike wani madafin iko ba, ba ka ko ba ki chanchanci zama shugaba ko mamba na wannan kungiya ba.

Ba na so in shiga cikin dalilinsu na hada wannan taron a wannan rubutu nawa, sai dai ina so in yi jan hankali ga ’yan uwana ‘ya’yan talakawa, wannan taron da ‘ya’yan shafaffu da mai suka yi kadai ya isa mu shiga hankalinmu idan muna da shi, sannan mu kuma farga mu tashi tsaye mu nema wa kawunanmu mafita.

Ba ma sai na fada ba, mun jiyo daya daga cikinsu yana cewa su kansu a hade yake, idan ma bai fada ba, mun gane wa idanuwanmu cewa ba sa fada da junansu saboda sabanin jam’iyya.

Ko muna so ko ba ma so, abin da taronsu yake fada mana shi ne sun fara shirin gadon iyayensu, mu kuma muna gefe muna fada da ‘yan uwanmu talakawa.

Lokaci ya yi da ya kamata dan talaka ya fara nema wa kansa mafita. Dan talaka ya fara tunanin shi ma ya shiga a dama da shi ba wai ya zama dan kallo ba.

Daga Dan’uwanku dan talaka, Ila bawan Allah. (08065895152)