✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Talaka jakin gwamnati

Hakika talakan Najeriya, ba zai taba sanin akwai dimokuradiyya a kasar nan ba, idan har gwamnonin kasar nan suka ki amincewa a ba kananan hukumomi…

Hakika talakan Najeriya, ba zai taba sanin akwai dimokuradiyya a kasar nan ba, idan har gwamnonin kasar nan suka ki amincewa a ba kananan hukumomi ’yancin cin gashin kansu ba. Sannan baya ga haka a mayar da zaben shugabannin kananan hukumomi da kansiloli ga Hukumar Zabe ta Kasa (INEC). Idan kuma ba haka ba, to har yanzu talakawan kasar nan, ba su da bambanci da jaki a wajen gwamnati.

Daga Tukur Sani Kwasara Karamar Hukuma Bagudo Jihar Kebbi. 08063365514.

Aminiya giwa ce cikin

jaridun Afirka

Zan so ku dan ba ni fili in dan yi bayani a kan shahararriyar jaridarmu ta AMINIYA abar alfaharinmu. Gaskiya jaridar Aminiya giwa ce, cikin jaridun Afirka saboda abin da na ji kuma na gani. Don haka muna yi wa wannan jarida addu’a Allah Ya kara daukaka ta.

Daga Dokta Mutallab Abdullahi Rapa Funtuwa. 08066458415.

Wa’azin kasa na Hadeja

Alhamdullah! Alhamdullah! Alhamdullah! Allah mun gode maKa. An kammala wa’azin kasa lafiya a garin Hadeja. Baki na kusa da na nesa muna fatan Allah Ya sa kowa ya isa gida lafiya. Mai martaba Sarkin Hadeja Alhaji Adamu Abubukar Maje, Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Jigawa, muna alfahari da kai bisa yadda a kullum kake ba da gudunmawa a al’amuran da suka shafi addini, Allah Ya ja zamanin Sarki. Malamai da suka gabatar da wa’azi, ’yan agaji, jami’an tsaro da duk wanda ya ba da gudunmawa a fili ko a boye muna addu’ar Allah Ya hada fuskokinmu a gidan Aljanna baki daya.

Daga Nasiru Kainuwa Hadeia 08100229688.

Yawaitar aikata fyade

Hukumomin a duk inda kuke ya kamata ku zage damtse sosai wajen yin hukunci mai tsanani ga masu aikata lafin FYADE. Domin yin hukuncin zai iya kawo raguwar masu aikata laifin, ganin yadda lamarin yake kara yawaita a kasashenmu.

Daga Shugaban Kungiyar MURYAR

JAMA’A, Haruna Muhammad Katsina. 07039205659.

Shawara ga Musulmi

Edita, ka taimaka mini in yi tunatarwa tare da ba da shawara ga al’ummar Musulmi.Shawarar kuwa ita ce kada mu zamo masu yin tufka da warwara, don Allah mu zamo mun rabu da dukkan dabi’u marasa kyau har abada tare da gyara tsakaninmu da Ubangijinmu, kamar yadda muka yi a watan Ramadan da ya gabata.

 Daga Murtala Ahmed Abubakar Kwalli Gidan Doki. 07068295953.

Kira ga Hukumar Hajji ta Kasa

Assalam. Muna kira ku taimaka ku isar mana da sakonmu zuwa ga gwamnatin Najeriya cewa, don Allah kada ta yi jinkiri wajen jigilar alhazan bana zuwa Kasa Mai tsarki, saboda wannan jinkirin da ake samu shi ke sa ake samun wasu matsaloli har wadansu alhazan su rasa aikin Hajji.

Daga Abbakar Lawal Gidan Danmaye Jargaba. imel:[email protected]

Tunatarwa ga Gwamna Ganduje

Salam AMINIYA. Don Allah ku mika min sakona zuwa ga Dokta Abdullahi Umar Ganduje, kan maganar hanyarmu wacce ta taso daga Kankare zuwa Kabo da Karaye ta wuce Rogo. Don Allah, Gwamna Abdullah Ganduje a taimaka wa talakawan yankin nan. Gaskiya muna cikin tsaka-mai-wuya na rashin kyan hanyar nan. Allah Ya taimaki Gwamnan Kano.

Daga Auwal M. Yusif 08065834330.

Sabon mulkin Nes Labul

 Salam Edita, Allah Ya kau da bacin rana, Nes Labul idan ba a ga wani sauki ba, to fa Bukola da Dogara za su fita daga zargi. Baba Buhari, kada ka sake yi musu dariya.

Daga Baba Kolawole, Kachallari Malam Madori, Jihar Jigawa. 07035356799.

Shawara ga Gwamnan Jihar Yobe

Zuwa ga Mai girma Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Mai Mala Buni, muna taya ka murna da yi maka fatan alheri. Ga shawara; ba a cimma nasara a mulki sai da daukar shawara domin Manzon Allah (SAW) yana neman shawara wurin sahabbansa saboda haka in ka zo daukar masu ba ka shawara ka dauki mutaen da suka san Yobe ciki da waje masu tsoron Allah masu kaunar Yobe da mutanen Yobe, ba masu kaunar kansu da ’ya’yansu kawai ba. Allah Ya ba mu lafiya da zama lafiya a jiharmu ta Yobe da kasa baki daya.

Daga Tanimu Bulama Wazirin Sarkin Alaba Rago 08034032974.

Musulmi da Kirista mu yi addu’a

Assalam Edita. A ba ni fili in tunatar da ’yan uwana ’yan Najeriya Musulmi da Kirista mu yi wa shugabanninmu da kasarmu addu’a. Allah Ya shirya shugabanninmu kuma Ya ba mu zama lafiya a Najeriya, amin ya Rabbil alamina.

Daga Bashar Hassan Jabo, Sakkwato 08062200667.

Kira ga Gwamnan Jihar Filato

Assalamu alaikum Edita. Don Allah ka ba ni dama in yi kira ga Gwamnan Jihar Filato Barista Simon Lalong dangane da masu sarauta suna karbe gonakin talakawa a Yelwa Shendam don Allah Ya sa ido.

Daga Ishaka Maidawa, Yelwan Shendam 08064558922.

Kirkiro da ’yan sandan jihohi

Salamun alaikum. Gaskiya ba na goyon bayan kirkiro da ’yan sandan jihohi domin hakan babu abin da zai haifar sai lalacewar al’amura da cin hanci da keta ’yancin dan Adam da amfani da su wurin musguna wa ’yan adawa. Sannan jihohi ba za su iya daukar dawainiyar horarwa da albashinsu ba. A dai inganta wadanda muke da su.

 Daga Jibril Abba Ocal, 08031183731.

Tunatarwa ga mahukuntar  Jihar Katsina

Salm Edita. Don Allah ku sake tunatar da mahukuntan Jihar Katsina kan matsalar zaizayewar kasa da ke neman cinye garin Mazoji a Karamar Hukumar Matazu. A baya majalisar jihar ta kafa kwamiti kan lamarin bisa jagorancin wakilin mazabar Matazu amma shiru. Da fatan wannan koke zai kai kunnuwan da suka kamata.

Daga Umar A. Umar Mazoji. 07054286772.

Kan dokar daure masu fyade a Yobe

Fatan alheri ga Edita. Babu shakka dokar daurin rai-da-rai ga masu aikata fyade da gwamnatin jiharmu ta sanya abin a yaba ne. Domin wallahi matsalar fyade ta dade tana addabar al’ummar jiharmu, Allah ne kadai Ya san yawan yaran da aka lalata wa rayuwa ta hanyar fyade a wannan jiha. To sai dai wani hanzari ba gudu ba muna kira ga lauyoyi da alkalai a fadin jiharmu ta Yobe cewa, su ji tsoron Allah wajen yin hukunci na gaskiya ko kare masu aikata wannan laifi da hujjojin karya. Allah Ka shirya mana al’umma, amin summa amin.

Daga Idriss M. Idriss, Unguwar Lugun Zadawa, Damaturu. 08033775767.

Fatan alheri ga sababbi da tsofaffin shugabanni

Salam Edita. Muna murna da fatan alheri ga sababbi da tsofaffin shugabannin da aka rantsar domin rike madafun iko domin gudanar da mulkin dimokuradiyya  a wannan kasa karo na biyu. Allah Ya ba ku ikon gudanarwa yadda ya kamata, a tuna da halin da halin talakan kasar nan yake ciki don Allah a sassauta. Allah Ya kawo ci gaba a wannan kasa, amin.

Daga Basiru Dan Bazazzagi. 08058591624

Zuwa ga Shugaba Buhari  

Assalamu alaikum Edita da sauran ma’aikata. Don Allah Shugaba Buhari kada ka karya zuciyar ’yan Arewa kamar yadda na karaya, don Allah a dube mu. A huta lafiya.

Daga Muhammad Shamsu Zarewa 08131636862.

Kira ga Gwamna Ganduje  

Gwamna kamar yadda ka sa ni matasan Dawakin Tofa suna cikin wani hali na rashin aikin yi. Da yawansu sun yi karatu a fannoni daban-daban amma babu aikin yi, mun san Gwamna mai aiki da cikawa ne, muna fata za a dubi lamarin matasan Dawakin Tofa.

Daga Aminu Sulaiman Mu’azu Kwa, 07064676135.

’Yan Najeriya a ji tsoron Allah!

Assalam Edita. Alhamdulillahi Allah Ya sa muna cikin ’yantattun bayinsa albarkacin Annabi da Alkur’ani. Saura  me ya kamata mu ji tsoron Allah ba sai a Ramadan ba, kuma shugabannin da aka zaba a kowane mataki su tuna fa sun yi rantsuwa a kan za su yi wa al’umarsu adalci.

Daga Dahiru Kano 08035856904.

Gaisuwa ga jagoran talakawan Najeriya

Aminiya ’yar amana, don Allah ku mika min sakon gaisuwa ga jagoran talakawan Najeriya kuma Shugaba Kasa Muhammadu Buhari da dukkan jama’ar Najeriya.

Daga Musa Unguwar Maiyasin, Danja Jihar Katsina. 08155648155.

Fatan alheri ga Gwamnan Borno

Assalam Aminiya mai albarka da fatar kuna lafiya. Ku ba ni dama in taya sabon Gwamnanmu na Jihar Borno Babagana Umara, da addu’a da fatan alheri. Ya Allah! Ka ba shi ikon da zai yakar mana Boko Haram a jiharmu ta Borno, amin.

Daga Ali Badina 09069158247.

Kira ga Buhari kan sakin

Ibrahim Zakzaky

Salam Edita. Ka ba ni fili in mika sakona ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari. Don Allah yaya matsayin Sheikh Ibrahim Zakzaky a kan rashin lafiyarsa da likitoci suka duba kwanan baya? Ya kamata a sake shi tunda kotu ta ba da umarni a sake shi a kuma biya shi diyya in har ba so Najeriya take ya mutu a hannunta ba.

Daga Baban Iya Kwarin Madaki Hadeja Jihar Jigawa.08146540330