✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Talauci shi ne babban abin da ya haddasa Boko Haram – Nyako

Dan Takarar Gwamnan Jihar Adamawa a karkashin Jam’iyyar  ADC, Sanata Abdul’azeez Nyako ya ce talauci ne babban abin da ya haddasa bullowar Boko Haram wadda…

Dan Takarar Gwamnan Jihar Adamawa a karkashin Jam’iyyar  ADC, Sanata Abdul’azeez Nyako ya ce talauci ne babban abin da ya haddasa bullowar Boko Haram wadda ta zame wa Arewa maso Gabas kalubale a tsawon lokaci.

Ya ce ban da haifar da Boko Haram da talauci ya yi, akwai kuma wasu matsaloli na fadace-fadace a tsakanin manoma da makiyaya da fashi da makami da garkuwa da mutane a kasar nan baki daya.

“Idan har matasa za su samu abin yi da za su iya magance kananan matsalolinsu, ba za a fuskanci matsalolin da ake fuskanta a halin yanzu a kasar nan ba,” inji shi.

Dan takarar Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Litinin da ta gabata, lokacin da yake zantawa da matasa a Yola game  alkawuran da ya dauka idan har ya ci zaben Gwamna a jihar.

Ya ce in har ba a magance matsalolin matasa ba a kasar nan, to lallai ba za a daina samun kalubale ba. “An lissafa Arewa maso Gabas ada cewa yankin ne ya fi ko’ina fama da da talauci da rashin sanya yara a makaranta, wannan duk dalilin matsalolin da kasar ke fuskanta ne na tsaro,” inji shi