✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Talauci ya sa na shiga satar mutane – Wanda ya sace dan shekara 7

Wani matashi dan shekara 19 mai suna Muhammad Sani Ahmed da ke Unguwar Gabukka a Gombe a Jihar Gombe wanda ake zargi da yin garkuwa…

Wani matashi dan shekara 19 mai suna Muhammad Sani Ahmed da ke Unguwar Gabukka a Gombe a Jihar Gombe wanda ake zargi da yin garkuwa da dan shekara 7 mai suna Hassan Abubakar Sarki da ke Unguwar Kumbiya-Kumbiya, ya ce talauci ne ya sa shi aikata haka, inda ya ce ana mako guda ba a dora abinci a gidansu ba, kuma hakan ne ya sa ya fara satar yara don karbar kudin fansa.

Da yake zantawa da Aminiya lokacin da ’yan sanda suka gabatar da shi ga manema labarai, Muhammad Ahmed Sani, ya ce ya sace yaron ne ya bukaci a ba shi kudin fansa Naira miliyan uku da rabi don ceto rayuwar iyayensa da kannensa daga kangin talaucin da suke ciki na rashin cin abinci kullum.

Ya ce son zuciya ta sa shi shiga wannan harkar ta satar mutane inda ya samu yaron a tsohuwar unguwarsu.

Ganin an taba sace wata ’yar uwarsa inda aka biya kudin fansa masu yawa, sannan ake zargin ya san wani abu, shi kuma ya ce shi bai san komai ba kuma babu hannunsa a ciki.

“Dalilin shigata wannan harka shi ne wani lokaci ana shafe mako guda ba a dora abinci a gidanmu kuma babban yayanmu ba ya nan, ni nake tafiyar da harkokin gidan, mamarmu da ni ta dogara kuma maigidana da nake aiki a wajensa muna tura wakoki a kwamfuta ina samun Naira 500 kullum ya  kore ni kuma ban iya wata sana’a ba, kuma ina da kanne biyu, ganin kuncin rayuwa da muke ciki sai son zuciya ya debe ni ya kai ni ga hallaka,” inji shi.

“Bayan yaron ya kwana daya ni da kaina na ce zan sa a mayar da shi gidansu, sai ya ce a’a ba zai koma ba in bar shi a wajena ya fi jin dadin wasa da ni,” inji Sani.

Ya kara da cewa ya dauke shi zai mayar da shi gidansu, sai wani ya gansu ya ce masa dama yaron ya bata kuma ana nemansa, ya kawo shi ya kai shi gidansu, shi ne ya kira kawun yaron ya zo ya dauke shi, a nan ne ’yan sanda suka kama shi.

Muhammad Sani ya ce saboda bai saba aikata laifi ba ko lokacin da ya kira baban yaron ya ce ya kawo Naira miliyan uku da rabi da ya ce ba ya da kudi sai ya kashe wayar jikinsa yana rawa saboda tsoron kada asirinsa ya tonu.

Mahaifin Hassan , Abubakar Sarki cewa ya yi ya kai iyalansa Unguwar Kumbiya-Kumbiya ne gaisuwar rasuwa a kan zai koma da dare ya dauko su sai aka kira shi aka ce Hassan ya bata ba a gan shi ba, inda nan take suka tafi ofishin ’yan sanda suka yi rahoton batarsa.

Ya ce washegari sai aka turo sako ta wayar yayan matarsa cewa, “Mu muka dauke yaron nan da ake nema idan kuna sonsa ku tura mana lambar wayar mahaifinsa cikin minti 30 in ba haka ba za mu salwantar da shi.”

Ya ce sai suka sake komawa wajen ’yan sanda suka sanar da su, su kuma suka dukufa bincike, ana cikin haka sai shi ma suka tura masa sako cewa yaron yana cikin koshin lafiya daga baya suka sake turo wani sako cewa, “Idan ba mu biya Naira miliyan uku da rabi ba za su salwantar da yaron.”

Mahaifin yaron ya ce, Sani wanda ya sace yaron ya dawo unguwar yana yi musu jaje yana cewa yaron ba zai fito ba, sai an bada kudi domin an taba sace ’yar uwarsa.

Daga nan ya gode wa Allah da kuma jami’an tsaro kan yadda suka kubutar da dansa cikin koshin lafiya.

Yaron da aka sace Hassan Abubakar Sarki ya yi bayanin yadda Sani ya sace shi a lokacin da yake alwala inda ya aike shi ya sayo masa ruwa, da ya tafi sai ya bi shi a baya ya dauke shi ya dora shi a kan babur.

“Kuma ban yi kuka ba a lokacin da ya dauke ni saboda ban san cewa sace ni ya yi ba,” inji Hassan.

Hassan ya ce da ya kwana a gidan su Sani ne ya gane sace shi ya yi. Kuma bai ce masa zai mayar da shi gidansu ya ce masa ba zai koma ba.  Hassan ya ce idan ya girma ya kammala karatu soja zai zama domin ya rika kama masu laifi.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Gombe, DSP Marry Malum, ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce da zarar sun kammala bincike za su tura wanda ake zargin zuwa kotu.