✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tallafin gwamnatin Yobe ba ya isa ga al’ummar Kare-Kare – Mahadi

Alhaji Abubakar Garba Mahadi dan asalin Jihar Yobe ne mazaunin Kano da ya shahara a kasuwanci. Ya taba aikin gwamnati a gidan rediyon Jihar Borno…

Alhaji Abubakar Garba Mahadi dan asalin Jihar Yobe ne mazaunin Kano da ya shahara a kasuwanci. Ya taba aikin gwamnati a gidan rediyon Jihar Borno a fannin tallace-tallace. Daga nan ya koma wani kamfanin gine-gine na ABC a Abuja. A tattaunawarsa da Aminiya ya ce: tallafin da gwamnatin Jihar Yobe ke badawa ga al’ummarsa ta Kare-Kare ba ya isa gare su:

 

 Alhaji Abubakar G. MahadiAminiya: A matsayinka na tsohon ma’aikacin gidan rediyon bangaren kasuwanci, yaya za ka kwatanta aikin jarida a wancan lokaci da yanzu?
Mahadi: Eh, gaskiya yanzu ka san komai ya zama na zamani, an kawata abubuwa an samu na’u’rori wadda aka inganta aikinAmma mu da ai namu mun yi dakake ne ko ci-da-karfi, don babu isassun kayan aiki irin na zamanin yanzu da suka saukaka abubuwa. Sannan kuma a da ma’aikatan kadan ne ba su da yawa, yanzu kuma saboda an samu kayayyakin aikin, aikin ya fi kyau fiye da da.
Aminiya: A da yaya kuke samo tallace-tallace ga gidan rediyo kuma yaya kuke tsara su ta wajen yi musu taken tallar da kade-kaden da kuke sakawa?
Mahadi: Fita muke yi mu nemo ko mu je Legas tunda akwai kamfanoni kuma za mu samo mai saka talla ya zo wajenmu ya fadi ko sakawa nawa yake so, sai a yi lissafin kudin a fada masa ya biya. Daga nan kuma mu nemi makadanmu na gargajiya da yara kanana mu zo muzauna mu shirya yadda tallar za ta kasance.
Aminiya: Me ya ja hankalinka ka dawo Kano da zama kuma da ka dawo me ka mayar da hankali a kansa?
Mahadi: Eh, dama ina sha’awar zaman Kano a rayuwata kuma da na dawo na kafa gidajen mai a nan Kano da Potiskum na ci gaba da kasuwancina.
Aminiya: Mene ne alakarka da wasu masarautu da suka ba ka mukamai?
Mahadi: kwarai na shafi sarauta domin iyayena sarakuna ne kuma da Ubangiji Ya yi zuwana Kano sai na samu alaka da fada saboda ayyukan taimakon al’umma da nake yi da suka hada da gyara makarantu, har ma na gyara wata makaranta da ke cikin fadar Mai martaba Sarkin Kano, na sa kayan koyo da koyar da karatu da sauransu. Ganin gyare gyraen da na yi a makarantun ne ya sa aka ba ni sarautar Jarman San Turakin Kano. Haka a can yankin Nangere na Jihar Yobe na yi aikace-aikacen da suka hada da bayar da ruywan sha. Haka na samu sarautar Matawallen Dokan Zazzau, abin da ya jawo haka na je Zariya ne sai na ga ana ta wahalar neman ruwa sai na nemi a fada min abubuwan da suka lalace, na sayo aka yi mako biyu ana gyara har ruwa ya zo, na gyara famfunan, shi ke nan jama’a suka ci gaba da dibar ruwa, to, jin dadin haka ne ya saka suka ba ni wannan sarautar.
Haka ma a Nasarawa, shi ma wahalar ruwa ta saka idan yara suna dibar ruwa suna wahala, har mutane suka taru suka kawo min kukan halin da suke ciki. To shi ne sai na je na ga wurin sai na sa aka yi musu burtsatse mai aiki da hasken rana na soja kuma yanzu suna amfani da shi. Wannan ne ya sa suka ba ni sarautar Sardaunan Nasarawa.
Aminiya: Me za ka ce game da jiharka ta asali Jihar Yobe ke ciki?
Mahadi: A can Yobe ni ne shugaban al’ummar Kare-Kare da Benu kuma ba wani abu ya saka suka zabe ni ba sai rashin samun jagoranci na kirki a baya. Na san gwamnati tana bayar da abubuwa don isarwa ga al’ummarmu ta Kare-Kare a can Yobe, amma kuma kwadayin musu jagorancin ya sa ba sa kaiwa ga talakawa, sai a handame a bar na kasa suna fama da tsananin bukata. Su talakawa suna jin haushin gwamnati, ita kuma gwamnati tana ganin ta tallafa musu. Abubuwan taimako kamar takin zamani da sauransu, su ne su talakawa ke bukata amma ba sa kaiwa gare su. Shawarata ita ce su rika yi wa talakawa abu saboda Allah, su rika kwatanta gaskiya. Shi kuma Gwamna ya mai da hankali ga mutanen kirki ba masu kwadayi ba.
Aminiya: Me kake so gwamnati ta yi wa mutanen yankinku?
Mahadi: Akwai abubuwa da yawa da suka kamata a yi wa al’ummar Kare-Kare a jihar Yobe. Yanzu haka muna tattara abubuwan da suke so da za mu kai gaban Gwamna wadanda muke ganin ya kamata a taimaka musu.
Aminiya: Me kake fata ga Jihar Yobe musamman a yanzu da take cikin yanayin tashin hankali?
Mahadi: Eh, yanayin tashin hankali na Yobe da Borno za mu iya cewa Ubangiji ne Ya jarrabe mu da shi kuma Shi zai kawo saukinsa. Ba za mu ce wane ne ya yi mana kaza ko wane ne ya yi mana kaza ba, daga Ubangiji ne sai dai Ya kawo mana saukinsa kawai.