✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Talle: Mace mai noman shinkafa da daddare

Hajiya Talle Adha ita ce Shugabar kungiyar manoma ta Najeriya reshen Jihar Jigawa, kuma mamba ce a Hukumar Noma da Bunkasa Karkara ta Jihar Jigawa…

Hajiya Talle Adha ita ce Shugabar kungiyar manoma ta Najeriya reshen Jihar Jigawa, kuma mamba ce a Hukumar Noma da Bunkasa Karkara ta Jihar Jigawa (JARDA), ta yi bayanin yadda ta fara noman shinkafa da daddare.

Hajiya Talle wacce ta ba wa shekara 50 baya takan dauki fitila da daddare bayan ’ya’yan sun yi barci , sannan ta je gona ta yi noma. Ta ce ta fara noma fiye da shekara 30 da ta gabata, ba wani sihiri ko tsatsuba take yi kafin ta je gona da daddare a lokacin da sauran manoma suke barci a gida ba.
 “Mijina ya rasu kimanin shekara 35 da ta gabata, ya mutu ya bar ni da ’ya’ya 6, babu wanda yake daukar nauyinmu, bayan na yi takaba, sai muka daina samun taimako, sannan mun cinye dukkan abincin da aka taimaka mana da shi, sai na rasa inda zan tunkara don in samu taimako, bayan na rasa sai na ce babban abin da zai fisshe mu shi ne in fara noma.
 “Daga nan ne na yi amfani da kudin da ya rage mana na sayi irin shinkafa, sannan kai-tsaye na wuce gona na fara nomanta. Aikin gona babu sauki, nakan je gona da daddare ne bayan ’ya’yana sun yi barci. Ba ni da kudin da zan dauki ’yan barema, a lokacin kuma ’ya’yana kanana ne, ba su da karfin yin noma, ba su yi wayon da zan iya tafiya da su gona ba. Babu kuma wanda zai lura mini da su, hakan ya sanya zan lura da su da safe, idan sun yi barci da daddare kuma sai in tafi gona. Nakan je da fitila ne, kasancewar ko’ina duhu ne.
Talle ta ce lokacin da ta fara noma a farko-farkon shekarun 1980, takan samu buhu biyu zuwa uku na shinkafa, amma a yanzu takan samu buhu 1,500 duk shekara. “Alhamdulillah, yanzu zan iya kiran kaina babbar mai noma. Allah (SWT) Ya taimake ni sosai. Na dauki nauyin ’ya’yana ta hanyar noman shinkafa. Hudu daga cikinsu sun yi digiri a Jami’ar Bayero ta Kano. daya yana aiki, sauransu kuma muna harkar noma tare.”
 “A yanzu na raba kafa domin ina kiwon kifi da kuma na kaji, ina da gonar kiwon kaji a Auyo, ban dade da sayar da kifi na Naira dubu 750 ba. Ina sayar da kajin Turawa, ina da garken shanu. Yawan shanuna sun kai 20. A bangaren noman shinkafa ina da ma’aikata 200 har da mata. Ina da na’urar zazzaba shinkafa a kusa da gidana, ina ba ’yan mata da masu aure, na kauyuka da na birane shawara don su fara noma da kiwo.
Ta yi korafin Gwamnatin Tarayya ba ta taimakon mata manoma: “Ministan Ayyukan gona da albarkatun kasa Dokta Akinwumi Adesina ya gayyace ni Abuja watanni biyar da suka wuce, ya gayyace ni ne bayan ya kawo ziyarar aiki Jihar Jigawa, sai ya ziyarci gonata, yadda nake tafiyar da ayyukan gonata ya ba shi sha’awa, ya ce ya yaba yadda mata suke noman shinkafa a jihar Jigawa.
“Hakan ya sanya ya gayyace ni da wadansu mambobin kungiyar AFAN zuwa Abuja, mun gana da shugaba Goodluck Jonathan sau uku, inda ya ce ministan ya ba mu (bangaren mata) motar noma da hilud da takin zamani. Yanzu fiye da wata biyar ke nan ba mu ga komai a kasa ba.”
Ta ce ta zauna da sauran mambobin kungiyarsu don tattauna yadda za su rika amfani da motar noma a gonakinsu da yadda za su rika amfani da hilud wajen kai amfanin gonarsu kasuwanni, duk da haka minsita bai cika umarnin da shugaban kasa ya ba shi ba.
Ta ce lokacin da ministan ya je gonakai a kauyen Adha da ke karamar Hukumar Auyo, ya ga yadda hanyar ta lalace, don hakan manoma suna shan wahala wajen kai amfanin gonarsu kasuwanni, ya yi alkawari zai gyara hanyar, amma har yanzu kamar an shuka dusa.