✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tambaya Da Amsa: Sakonnin tes daga masu karatu (1)

Tambaya: Assalamu alaikum Baban Sadik, sunana Mukhtar Ibrahim. Don Allah ina so ka ba ni shawara a kan littafin da zan nema wanda zai taimaka…

Tambaya: Assalamu alaikum Baban Sadik, sunana Mukhtar Ibrahim. Don Allah ina so ka ba ni shawara a kan littafin da zan nema wanda zai taimaka mini don koyon “Programing” ta yaren Jaba. Kuma da me da me ya kamata in nema?  Na gode.

Amsa: Wa alaikumus salam, Malam Mukhtar.  Koyon “Programming” abin so ne, domin fanni ne mai kayatarwa cikin fannonin kimiyya da fasahar sadarwa.  Ilimin “Programming” ya dada kayatarwa tare da habbaka na’urorin wayar salula da kwamfuta da kuma gidajen yanar sadarwa. Koyon wannan ilimi yana bukatar hakuri da juriya da jajircewa da kuma sadaukar da kai da lokacinka. Dangane da wane littafi za ka nema don koyon dabarun gina manhaja na “Jaba” yana da kyau da farko ka san cewa, koyon wannan ilimi yana da matakai. Na farko shi ne ya zama ka iya sarrafa kwamfuta wajen kunnawa da kashewa da rubuta bayanai da taskance su da nemo su da kuma iya mu’amala da shafukan intanet wajen neman bayanai.

Yunqurin koyon qirqira manhaja a intanet

Mataki na biyu shi ne ilimi kan “Programming” me yake nufi, mene ne tarihinsa, nau’ukan dabarun gina manhaja nawa ake da su, wanne ne ya kamata ka fara da shi? Sannan, idan ka samu kwarewa a fannin gina manhaja ko “Programming” din, me kake son yi da ilimin? Amsa wadannan tambayoyi daga zuciyarka, ba daga kwakwalwarka ba, shi zai taimaka maka wajen samar da tsari cikin abin da kake son aiwatarwa da ilimin. Amma idan kawai kana son koyon “Jaba” ne don ka ji sunan ya shahara a bakin mutane, ko don ka ga wani ya yi, ko don ka ji an ce da wannan yaren ne ake iya kera manhajojin wayar salula da ke “Play Store” sai kawai ka dauka kai ma bari ka koya don ka iya kera manhajoji, to, wannan zai zama kuskure. Kuma koyon yaren ta wannan dalili ba zai sa ka fahimci komai a lamarin ba.

Mataki na uku shi ne, idan ka gama sanin wadannan abubuwa da ke matakai na farko da na biyu da bayaninsu da ya gabata, sai ka je matakin koyon harshe ko dabara ta musamman daga cikin dabarun gina manhajar kwamfuta. Na ji ka ambaci yaren “Jaba,” tabbas yare ne mai kyau kuma kashi 40 cikin 100 na manhajojin da ake amfani da su a na’urorin sadarwa da intanet a yau, duk an gina su ne da wannan yare. To amma ba nan gizo ke sakar ba, ga dan koyo wanda bai taba sanin me ake nufi da “Programming” ba, wannan zai zama tsallen-badake. Don haka ni shawarata ita ce, ka fara da kananan dabarun gina manhaja masu sauki, musamman wadanda ake amfani da su wajen gina gidajen yanar sadarwa.

Misali, kana iya farawa da yaren “HTML” da “CSS” da kuma “JabaScript.” Wadannan su ne manyan yarukan da ake amfani da su wajen gina yanar sadarwa na kwamfuta ko na wayar salula.  Idan ka mallaki kwarewa a wadannan fannoni ko yaruka uku, koyon kowane irin yaren gina manhajar kwamfuta ko na intanet ba zai maka wahala ba. Idan kuma ka dage kana son lallai ka fara gina manhajar kwamfuta ce kai tsaye, kana iya farawa da yaruka masu sauki irin su “Python.”  Yare ne mai sauki, wanda ke amfani da karancin kalamai wajen bai wa kwamfuta umarni don gina manhaja. Koyon “Python” zai taimaka maka kwarai musamman wajen kara cusa maka sha’awa da son fannin gina manhajar kwamfuta, wato: “Programming.”  Ba don komai ba sai don saukinsa da kuma nishadin da ke dauke dashi.

Ala ayyi halin, idan ma ka zabi ka koyi “Jaba” din ne kai tsaye, to, dole ne ka sadaukar da kanka da kuma lokacinka, tare da karfafa zuciyarka wajen soyar da abin da kake yi gare ta. Da wannan ne za ka samu cin ma nasara. Ina yi maka fatan alheri, tare da rokon Allah Ya taimaka maka cikin dukkan abin da ka sa gaba na alheri.

Tambaya: Assalamu alaikum, Abban Sadik, tare da fatan kana lafiya. Don Allah ta yaya ake bude sabon gidan yanar sadarwa? Na jima ina so in koya amma har yanzu Allah bai yi ba. Daga Abbati Yaya!

Amsa: Wa alaikumus salam, Malam Abbati.  Barkanka dai. Abin da nake iya fahimta daga tambayarka shi ne, kana so ne ka mallaki gidan yanar sadarwa, ta hanyar ginawa da hannunka ko kanka, kamar yadda a al’ada Bahaushe ke fada. Idan wannan ce manufarka, ga matakan hanyoyin nan.

Mataki na farko shi ne mallakar ilimin yin hakan, in dai da kanka kake son ginawa ba wai ka bai wa wani ya gina maka ba. Amma idan kana son mallaka ne ta hanyar wani ya gina maka, kana iya tuntuba ta don tauttaunawa kan haka din. Idan ka mallaki ilimin gina gidan yanar sadarwa, sai ka gina naka da kanka. Shi ilimin gina gidan yanar sadarwa ya kasu kashi biyu. Kana iya ginawa ta amfani da dabarun gina shafukan intanet, irin su: “HTML” da “CSS” da kuma “JabaScript.” Wadannan su ne yaruka uku da ke bai wa mutum damar ginda shafin intanet mai inganci, iya kwarewarsa. Kashi na biyu kuma shi ne, kana iya amfani da ginannun kwarangwal din gidan yanar sadarwa na zamani da ake samunsu kyauta ko ta hanyar saya a intanet, don kayatar da su iya yadda kake so.  Wadannan kwarangwal dai madaukai ne da ake amfani da su wajen tsarawa da kuma dora bayanan da ake son dorawa (zallan rubutu da hotuna da bidiyo da sauransu). Kuma su ake kira: “Content Management System” ko “CMS” a gajarce.  Shahararru daga cikinsu sun hada da “Bootstrap” da “Wordpress” da “Joomla” da dai sauran makamantansu.

Kana iya mallakar wadannan kwarangwal kyauta daga shafukansu (misali: www.wordpress.org/download) sannan ka tsara shafin a kan kwamfutarka. Da zarar ka gama, sai mataki na gaba.

Mataki na biyu shi ne, mallakar adireshi, wato: “Domain” ke nan. Wannan adireshi ne masu neman shafinka za su rika shigarwa cikin rariyar lilo (Browser) don isa ga bayanan da ke shafinka na intanet. Za ka yi rajistar wannan adireshi ne daga kamfanonin da ke aikin rajistar adireshin yanar gizo a intanet.

Sai mataki na uku, wato mallakar ma’adanar shafin gaba daya. Wannan shi ake kira: “Web Hosting” kuma shi ne tsarin da ke dauke da dukkan bayanan da kowane gidan yanar sadarwa ke dauke da shi. Da zarar ka mallaki wadannan abubuwa biyu, sai ka dora shafin da ka gina a mahallin da aka ba ka na “Hosting,” sannan ka nuna wancan adireshi da ka yi rajistarsa a farko, zuwa ga mahallin da bayanan gidan yanar sadarwan ke dauke da su.  Wannan, a takaice ita ce hanyar da ake bi wajen mallakar gidan yanar sadarwa.

Tambaya: Assalamu alaikun Baban Sadik, na ji dadin tambayoyin da aka yi kan Tsibirin Bamuda da kuma tekuna; kamar don ni aka yi su. Ina godiya da amsoshin da aka bayar da kuma saukaka mana da aka yi. Fatan Allah Ya kara yassare mini waya mai hawa yanar gizo.  Allah Ya saka da alheri, Ya kuma kara basira, amin. Daga Sammani Shu’aibu.

Amsa: Wa alaikumus salam, Malam Sammani. Ina godiya matuka, tare da farin cikin jin ka samu gamsuwa cikin dan abin da na gabatar na bayanai. Da fatan za a ci gaba da kasancewa tare da jaridar AMINIYA, wacce a koyaushe take dauke da amintattun bayanai don fadakar da masu karatu. A duk sadda aka ga kuskure kuma cikin abin da nake gabatarwa, sai a nusar da ni.  Ina kara godiya matuka. Allah bar zumunci. Na gode.

Tambaya: Salam Baban Sadik, ni dai mai bibiyar filinka ne na AMINIYA kuma ina gaishe ka bisa himma da kokarinka a wannan fage da ya shafi kimiyya. Wallahi kana matukar burge ni da ba ni sha’awa. Don Allah ka isar da gaisuwata ga Sadik danka. Na gode. Daga Basiru Danbazazzagi.

Amsa: Wa alaikumus salam, Malam Basiru ina godiya matuka da fatan alheri da kake mana baki daya.  Sannan na yi farin cikin jin cewa kana samun gamsuwa da irin bayanan da kake karantawa masu dauke da binciken da nake gabatarwa iya gwargwadon hali da sani. Sadik zai ji gaisuwarka in sha Allah. Ina kuma rokon Allah da Ya albarkaci rayuwarka, tare da ci gaba da kasancewa tare da mu a jaridar AMINIYA. Na gode,  na gode, na gode.

Za mu ci gaba