✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tambaya Da Amsa: Sakonnin tes daga masu karatu (2)

Tambaya: Assalamu Alaikum Baban Sadik, muna son don Allah ka yi mana bayani a kan tsawa da ke faruwa a lokacin da ake ruwa. Menene…

Tambaya: Assalamu Alaikum Baban Sadik, muna son don Allah ka yi mana bayani a kan tsawa da ke faruwa a lokacin da ake ruwa. Menene ke fadowa kuma me ke haddasa ta a kimiyyance? Daga Aminu M. Mai’aduwa.

Amsa: Wa alaikumus salam, barkanka dai Malam Aminu da fatan an wuni lafiya. Dangane da iya binciken malaman kimiyya, sun nuna kafin samuwar tsawa, akwai haske da ke bayyana, wato walkiya ke nan kamar yadda muke cewa, daga nan sai samuwar rugugi mai karfi, mai girgiza da muke kira cida a harshen Hausa. Bayan cida ne kuma sai sautin tsawa ya biyo baya a karshe. Haka abin ke biye, kamar yadda muke ji ko gani amma a hakika lokaci guda duk suke samuwa.  Mene ne dalilin samuwar tsawa, yaya walkiya da rugugin cida ke rigayar sautin tsawa?

Wannan tambaya da ka yi mini, irinta aka yi wa Farfesa Richard Brill da ke Kwalejin Honolulu (Honolulu Community College) a kasar Amurka, cikin shekarar 2000, wadda kuma Mujallar “The Scientific American” ta buga a shafinta a watan Disamba na shekarar 2002.  Ga nassin amsar da ya bayar nan kai tsaye na fassaro maka:

“Abin da ke haddasa samuwar tsawa shi ne walkiya, wanda asali yake dauke da cunkoson sinadaran “Electron” da ke makare a cikinsa ko a tsakanin giza-gizai ko kuma tsakanin giza-gizai da muhallin da muke rayuwa a ciki a wannan duniya tamu. Nau’in iskar da ke gewaye da wadannan sinadaran “Electron” kan yi zafi (sanadiyyar zafin rana), zafi mai tsananin da ya kai kimanin digiri 50,000 a ma’aunin zafi na Faranhait (50,000F), daidai da zafin rana ninki uku ke nan. Da zarar wannan iska mai dan karen zafi ta fara hucewa, sai ta samar da wata jakar iska a gewaye da titin da iskar ke bi. Nan take sai iskar da ke makwabtaka da wannan jakar iska ta rika fadada tana tsukewa, tana fadada tana tsukewa, lokaci-lokaci. Wannan ke sa jakar iskar da ke gefe ta rika girgiza cikin batsewa, hakan kuma yana haifar da sautin tsagewa. Da zarar wannan girgiza ta fara lafawa, sai ta haifar da wani sauti mai tsananin kara da muke kira “Tsawa.”

Muna iya jin masifaffen sautin tsawa da bugawarsa daga tazarar mil goma (kilomita 13) ko sama da haka daga hasken da ke haddasa tsawar. Sannan idan walkiya ta auku a iya tazarar da ake iya ganinta, ita muke fara gani (ba sautin rugugin cida ko tsawar ba), domin gudun sauti a cikin haske bai kai gudun sinadaran “Electron” da gudanuwarsa ba. Shi ya sa ma sautin tsawar ke aukuwa kamar sautin hatsarin wutar lantarki, ba kamar sauti irin wanda da aka sani na al’ada ba. Shi wannan sauti mai kama da sautin hatsarin wutar lantarki yana bibiyar titin wannan sinadarin “Electron” ne (a yayin da yake aukuwa), kamar yadda dunkulen yatsu ke tasiri a jiki yayin da aka naushi mutum.

Bayan haka, gudun sauti ba komai ba ne idan aka kwatanta shi da gudun haske. Hasken da ke samuwa a yayin walkiya na riskar mu ne (a wannan duniya) cikin kasa da dakikaguda, a yayin da sautin ke biye da shi cikin saibi da nawa, kai ka ce dodon kodi ne ke biye da jirgi nau’in roket da ke shawagi a tsakanin duniyoyi.  Don haka, yanayin sauti da haske da ke samuwa a lokacin walkiya da tsawa hadaka ne na abin da ke samuwa sanadiyyar girgizar da sinadaran iska ke yi wajen hargitsa karfin sinadaran lantarki. Wannan wani al’amari ne mai matukar ban mamaki hakika, kuma wannan ke dada tunatar da mu duka cewa mu ba komai ba ne idan aka gwama halittarmu da ta sararin samaniya.”

Wanda ya yi wannan fatawa dai malamin jami’a ne, ba Musulmi ba ne kuma. Amma ka ga yadda ya kare fatawar da jawo hankali zuwa ga girma da karfin kudurar Ubangiji a kaikaice. Da fatan ka gamsu da dan abin da ya samu na bayani.

Tambaya: Assalamu alaikum Baban Sadik, barka da warhaka kuma barka da dawainiya da jama’a. Ina yi maka fatan alheri da Allah Ya kara fahimta, amin. Baban Sadik, a shafina na Facebook idan na yi ‘Log In’ sai in dinga ganin “comment” wanda ni ba ni na rubuta da kaina ba. Ko kuma in dinga ganin an rubuta cewa: “Your rekuest is accepted” ba tare da ni na yi rekuest ba. Don Allah ina neman mafita. Allah Ya kara fahimta. Daga Sunusi Muhammad, [email protected]

Amsa: Wa alaikumus salam Malam Sanusi da fatan kana lafiya. Daga bayaninka kamar kana nufin ba kai ba ne ka yi wadannan “ta’aliki” (Comments); kawai ka ga abin ne. A iya sani na dai, ba zan iya tuna wani al’amari da zai iya haddasa hakan ba sai dalilai uku, ko dayan uku. Na farko shi ne, watakila kai ne ka yi amma ka mance. Na biyu, ko dai ta’alikin da kake ganin wasu ne suka yi a kasan sakon (Post) da ka rubuta a baya.  In har babu dayan biyun nan, to ta yiwu, Allah sawwake, watakila wani ne ya kutsa cikin shafin naka yake wakiltarka ba tare da izininka ba. Amma in ba haka ba, ba abin da zai iya sa hakan ta faru. Don haka, kana iya bincika shafin naka ka gani, don tabbatar da hakikanin abin da ya faru ko yake faruwa da shafin naka.

Ka kuma nuna cewa wasu lokuta kana ganin sakonni da ke cewa: “Your Rekuest is accepted.” Wannan sako na bayyana ne bayan wani ya karbi bukatarka ta yin abota da shi, wanda ka aika masa a baya. Muddin ka ga wannan sako, to lallai a baya ka taba aikawa da sakon neman abota (Friend Rekuest) ga wani kuma amincewarsa ce ta haddasa samuwar wannan sako da ka ci karo da shi. Don haka, sai ka duba ka gani, shin wanda ya karbi bukatarka ta abotan nan, ka san shi? Ko za ka iya tuna sadda ka aika masa bukatar neman abota?  In har ba ka san shi ba kuma ba za ka taba iya tuna sadda ka aika masa da wannan sako na neman abota ba, to lallai akwai abin da ke faruwa. Sai ka duba tsare-tsaren shafin naka sosai ka gani. Tabbas ba za a rasa dayan biyu ba, ko dai kai ne ka aika amma ka mance, watakila saboda tsawon lokacin da aka dauka bai amince maka ba, ko kuma wani yana hawa shafin naka yana wakiltarka ba tare da izininka ba. Wannan dalili na biyu shi ake kira: “Identity Theft” (Satar Zati).

Wannan shi ne dan abin da zan ba ka na shawara. Ina maka fatan alheri da rokon Allah Ya sa ka samu hanyar warware wannan matsala cikin sauki.

Tambaya: Assalamu alaikum Abban Sadik. A matsayina na dalibinka na yau da kullum, tambayata a nan ita ce, ta yaya tauraron dan Adam yake zama a cikin sararin samaniya, sannan kuma a wace duniya ce aka fi jefa shi? Daga dalibinka, Saminu Artillery Yelwa Shendam Jihar Filato, 08032436477, [email protected]

Amsa: Wa alaikumus salam Malam Saminu da fatan kana cikin koshin lafiya. Wannan tambaya ce mai matukar muhimmanci kuma tana cikin tambayoyin da suke yawan maimaituwa a wannan shafi mai albarka. Don haka na kebance wannan lokaci don fadada bayani iya gwargwado.

Da farko dai, tauraron dan Adam shi ne duk wata na’ura mai cin gashin kanta da ake harbawa zuwa sararin samaniya don mikawa da karbo bayanan yanayi ko dauko hotunan wasu wurare da dan Adam ba ya iya kaiwa gare su ta dadi ko kuma sunsuno irin yanayin da muhalli zai kasance a wasu lokuta na daban ko kuma don yada bayanan sadarwa daga wani bagire na duniya zuwa wani bagiren. Ire-iren wadannan taurari suna shawagi ne a cikin falakin wannan duniya tamu ko duniyar wata da taurarin da Allah Ya halitta, ko kuma cikin falakin wasu duniyoyi makamantan namu. A halin wannan shawagi ne suke gudanar da ayyukansu na nemo bayanai, ko karbowa daga wani bangaren wannan duniya don yada bayanan zuwa wasu bangarorin daban, ko kuma nemo bayanan da ke da nasaba da falakin da suke shawagi a ciki, don aiko sakon da suka taskance zuwa gare mu a wannan duniya, ko kuma a wasu lokutan, su dauko mana hotunan abin da ke faruwa ga manya-manyan tekunan da ke zagaye da mu a duniya gaba daya.

An fara harba ire-iren wadannan taurarin wucin-gadi ne zuwa cikin falaki shekaru kusan hamsin da tara da suka gabata (1957), kuma ya zuwa yanzu, an harba wajen dubunnai masu zuwa don karbowa da aikawa da bayanai ko sunsuno yanayi ko kuma dauko hotunan sararin samaniya, don amfanin dan Adam. A karon farko ana amfani ne da roket ne mai dauke da kumbo, don cilla wani tauraro zuwa sararin samaniya. Daga baya aka zo ana amfani da jiragen sama masu masifar gudu, duk da yake shi ma wannan tsari na bukatar roket wanda ke harba jirgin zuwa wani mizanin nisa cikin samaniya, kafin wannan jirgi ya ingiza tauraron cikin falaki.

Ana cikin haka sai kuma masana kimiyyar sararin samaniyar Amurka suka bullo da wata hanya wacce ta sha bamban da sauran wajen sauki da inganci. Wannan hanya kuwa ita ta cilla tauraron dan Adam daga babbar kumbon tashar binciken sararin samaniya da ke can sararin samaniya, wato US Space Shuttle. Hakan na faruwa ne domin masana na iya kera tauraron dan Adam a halin zamansu cikin wannan kumbo da ke tashar, har su harba shi. Haka idan ya lalace ko ya gama aikinsa, suna iya sanya shi cikin wani kumbo karami don aikowa da shi wannan duniya tamu don a gyara shi yadda ya kamata. Nan gaba, masana harkar falaki a Amurka na tunanin bullo da wani tsari mai suna Single Stage to Orbit, wato “tsalle daya zuwa falaki” a misali.  Wannan tsari zai rage yawan tashoshin da tauraron dan Adam zai bi kafin kaiwa ga falakin da aka tunkuda shi don gudanar da aikinsa. Idan har suka dace, wannan tsari zai zo ne da kumbon sararin samaniya guda daya, tafkeke, mai iya daukar taurarin dan Adam da dama, don aikawa da su zuwa cikin falakin da ya dace da su, cikin harbawa guda!

Za mu ci gaba