✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tambaya da Amsa: Sakonnin tes daga masu karatu (4)

  Wayoyi samfurin kirar Android Tambaya: Assalamu alaikum, muna nan biye da Baban Sadik a kowane mako kuma muna kara mika godiya ta musamman a…

 

Wayoyi samfurin kirar Android

Tambaya: Assalamu alaikum, muna nan biye da Baban Sadik a kowane mako kuma muna kara mika godiya ta musamman a gare ka akan wannan shafi na Kimiyya da Kere-Kere. Fatanmu Allah Ya kara tsawon kwana, Ya kara maka kwarin gwiwa, amin-summa-amin.  DagaAbdullahi Bello Anka, 08060809091.

Amsa: Wa alaikumus salam, barka dai Malam Abdullahi. Ina godiya matuka kuma Allah saka da alheri. Na gode, na gode.

Tambaya: Assalamu alaikum, da fatan Baban Sadik yana nan lafiya. Tambayata ita ce, don Allah Malam a taimake ni da hanyoyin da zan bi in fahimci “Programming” cikin sauki. Na gode. Daga Iro Manu, [email protected]

Amsa: Wa alaikumus salam, Malam Iro. Kalmar “Programming” na ishara ne ga ilimin gina manhajar kwamfuta ko ta wayar salula. Kamar sauran nau’ukan ilimi, yana bukatar sha’awa, wato ya zama kana son abin a ranka, wannan zai taimaka wajen sa ka sadaukar da lokacinka wajen koyo, tare da hakuri da jajircewa.  Wadannan duk dabi’u ne da dole ka sifatu da su idan kana bukatar kwarewa a wannan fanni. Bayan haka, idan ba ka taba mu’amala da kwamfuta ba, ma’ana ba ka iya sarrafata ba, dole ne ka fara koyon wannan bangare tukun, kafin ka je bangaren “Programming.” Domin idan ba ka san matakin farko ba, ba ka tsallakawa zuwa matakin karshe.

Ilimin “Programming” ilimi ne mai matukar fadi da kuma sarkakiya. Daga cikin abin da ke taimakawa wajen sawwake tsauri da sarkakiyarsa shi ne ya zama kana da matakin farko na ilimin kwamfuta a aikace.  Wato ya zama ka iya sarrafa kwamfuta wajen kunnawa, da kashewa da iya sarrafa manhajoji daban-daban a kanta. Daga cikin abubuwan da suka fi komai muhimmanci wajen koyon ilimin kwamfuta a matakin farko shi ne, ka iya sarrafa kwamfuta wajen rubutu.  Ma’ana ya zama ka iya amfani da kwamfuta wajen rubutu sosai. Domin duk wani fanni na ilimin kwamfuta da za ka koya ko kware a kansa daga baya, ya ta’allaka ne kan wannan bangare na matakin farko, wato” iya rubutu.

Wadannan kadan ne cikin abin da zan iya rubutawa, da fatan ka gamsu.

Tambaya: Assalamu alaikum, don Allah Baban Sadik ina da tambaya, da fatan za a ba ni amsarta. Tambayar ita ce, ina da waya kirar “Infinid Hot 4-Lite.” Idan ina so in tura wa wani bidiyo yaya zan yi? Ba wai in tura ya je “Home” ba. Daga dalibinka Suraj Idriss, kasar Ghana.

Amsa: Wa alaikumus salam, Malam Suraj barka kadai. Aikawa da bidiyo ta amfani da wayar salula nau’in “Infinid Hot 4-Lite” na wahala. Idan ka je manhajar da ke dauke da dukkan sakonninka na bidiyo, kana iya latsa wanda kake son aikawa da shi, sai ka latsa ka rike na tsawon dakika daya zuwa biyu, sai ka daga yatsanka. Da zarar ka daga, za ka ga wayar ta sanya wa bidiyon alamar maki kore karami. A can kasa kuma daga bangaren hagu, za ka ga tambayar yada sakonni mai suna: “Share.” Kana matsawa za a budo maka hanyoyin da za ka iya aikawa da wannan sako na bidiyo kai tsaye.

Idan kana da manhajar Imel na Gmail ko manhajar Whatsapp ko manhajar sakon tes (Message), ko manhajar Twitter, duk za ka gan su a wurin. Sai ka zabi manhajar da kake son amfani da ita wajen aikawa da bidiyo din, kai tsaye za a aika. Sannan za ka ga manhajar fasahar “Bluetooth” a cikinsu; ita ma duk kana iya amfani da ita wajen aikawa da sakon bidiyon.  Sai dai dole ne ka lura, idan manhajar da ka zabi amfani da ita wajen aika sakon bidiyon tana amfani ne da fasahar intanet, to a nan kam dole ne ka tabbatar ka kunna “data” din wayarka, don samun siginar intanet kafin aikawa da sakon.

Wannan shi ne bayani a gajarce, kan yadda za ka iya amfani da wannan waya wajen aikawa da sakon bidiyo, ta la’akari da irin manhaja ko fasahar da ke dauke kan wayarka. Da fatan ka gamsu.

Tambaya: Salamun alaikum Baban Sadik, don Allah me ya sa idan aka canza wa waya “file” ko “flashing” take kin yi? Domin ina da waya Samsung GLD4-Lite, idan na kunna ta sai ta rubuta: “Samsung gld4-lite” amma daga nan ba ta sake nuno komai. Na kai ta wajen mai gyara an canza mata “file” ko “flashing” har sau uku amma ba canji. Daga Mukhtar I. Ya’u.

Amsa: Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Mukhtar. Daga bayanan da ka yi zan iya fahimtar cewa matsala ce wayar ta samu a karon farko, daga baya aka kai wajen mai gyara aka mata filashin amma har yanzu ta kasa tashi. A ka’ida, matsalolin wayoyin salula suna samuwa ne daga manyan bangarori guda biyu; da bangaren ruhi ko manhajarta da kuma matsala ta bangaren gangar jikinta. Matsalolin da suke da alaka da manhajar waya, musamman ma babbar manhajarta, wato: “Operating System,” ana iya gyara su ta la’akari da manhajar. Idan komai ta ki, da zarar an mata filashin shi ke nan, dole ta koma yadda take kamar ran da aka kera ta, domin shi filashin tsari ne da ke kawar da dukkan wasu bayanai da ke manhajar wayar gaba, ya mayar da hakikanin bayanan da wayar ta zo da su, a farkon lamari.

Bangaren matsalar waya na biyu kuma kan samu ne daga gangar jikin  wayar, kamar maballanta (Keypads), ko sifika, ko batir, ko kuma fuskarta, wato: “Screen” ke nan. Dukkan matsalolin da ke da alaka da gangar jikin waya ana iya kawar da su ne ta hanyar gyara gabar da ke da matsalar. Idan komai ya ci tura, sai a cire (idan zai yiwu) a sa mata sabuwar gaba, don ba ta damar ci gaba da rayuwa. Misali, idan wayar salula ta fada cikin ruwan zafi, mai zafi sosai, da wahala ta rayu. Ma’ana, wannan larurar na iya kona hakikanin “shimfidar” injin wayar baki daya, wato: “Motherboard” ke nan. Idan kuwa haka ta faru, to zai yi wahala wayar ta sake farfadowa.

Don haka, shawarata ita ce, ka canza mai gyara ko kuma akalla ka shawarci mai gyara maka wayar da ya duba dukkan bangarorin gangar jikinta, don tabbatar da lafiyarsu baki daya. Kada ya dogara ga filashin dinta kadai, domin ba dukkan matsalolin waya ba ne ake iya magance su ta hanyar filashin. Sai in sun danganci matsala ce da ta samo asali daga daya daga cikin manhajojin da ke wayar.

Wannan ita ce shawarar da zan iya bayarwa. Ina kuma yi maka fatan Allah sa a dace, amin.

Tambaya: Assalam Baban Sadik, an yini lafiya? Da fatan Allah Ya sa haka amin. Kafin tambayata Baban Sadik, na saba rubuto tambayata amma ba ka taba ba ni amsata ba. Shin ko ana wariya ne? Baban Sadik ana iya gina manhajar kwamfuta ba tare da ka dora na’urar kwamfutar a yanar gizo (internet) ba? Daga Saminu Artillery Yelwan Shendam.

Tambaya: Assalamu Alaikum Baban Sadik, da fatan kana lafiya. Tambayata a nan ita ce, me wadannan kalmomi suke nufi a fannin kwamfuta, “Archibe” da “Encrypt” da “Synchronize” da “Configure” da “Compress” da kuma “Debug?” Ka huta lafiya, daga Idris Hamza.

Amsa: Wa alaikumus salam Malam Idris Hamza, barka kadai. Wadannan kalmomi dai da kake son sanin ma’anoninsu a takaice, kalmomi ne da suka shafi fanni da harkar sadarwar wayar salula da kwamfua da kuma tsarin sadarwa na zamani. Ga ma’anoninsu nan a takaice.

Archibe: Kalmar “Archibe” kalma ce da ke nufin “matattara” ko “taska” ko wata ma’adanar bayanai, amma ta manhajar sadarwa, ba ma’adana irin wacce ake jona wa kwamfuta don zuba bayanai a ciki ba. Sannan kalmar na iya daukar ma’anar aiki ko “fi’ili.”

Encrypt: Kalmar “Encrypt” an samo ta ne daga kalma mai suna “Encryption” wadda ke nufin tsarin “boyewa ko layance bayanai, don tabbatar da ingancinsu da kamalarsu.” Wannan tana da kishiyarta mai suna “Decrypt” wacce aka samo asalinta daga kalmar “Decryption.” Ita kuma tana ishara ne ga tsarin “warware bayanan da aka layance su, don mayar da su zuwa asalinsu.” Wannan tsari ilimi ne mai zaman kansa a fannin sadarwar zamani. Shi ne bangaren da ke lura da tsarin tsaro da kariyar bayanai, wato: “Information Security.” Idan ka je shafin kamfanin Imel dinka (Yahoo, ko Gmail, ko Hotmail), bayan ka shigar da sunanka (username), kana fara rubuta kalmar sirrinka (password), nan take za ka ga dunkulallun bakake ne ke bayyana, ba hakikanin kalmomi ko haruffa ko lambobin da kake rubutawa ba. Wannan fanni na “Encryption” shi ne ke tabbatar da yiwuwar haka a aikace. Ilimi ne mai fadin gaske kuma wanda ya samar da asalinsa shi ne Sheikh Muhammad bin Musa Alkhawaarizmi, daya daga cikin shaharrun malaman Musulunci.

Synchronize: Kalmar “Synchrinize” kuma na nufin tsarin musayar bayanai ne tsakanin ma’adanan bayanai biyu, kai tsaye. Ka lura, na ce kai tsaye domin tabbatar da hakan na faruwa ne a lokaci guda. Misali, idan ka taskance lambobin wayarka nau’in Android gaba a kan manhajar taskance lambobin waya na Google mai suna “Google Contact,” a duk sadda ka sake shigar da wata sabuwar lamba kan wayarka, muddin wayar a jone take da intanet, nan take wannan manhaja ta “Google Contact” za ta aiwatar da musayar bayanai tsakaninta da wayarka, ta hanyar duba canjin da aka samu tsakanin yawar lambobin da ke kanta da wadanda ke kan wayarka. Da zarar ta lura akwai sauyi, sai ta duba, shin sauyin ta bangaren wayarka ne ko ta bangarenta?  Ma’ana, karuwa lambobin suka yi ko raguwa? Idan karuwa suka yi, sai ta loda wadanda ba ta da su daga wayarka. Idan kuma raguwa suka yi, sai ta sauko da wadanda aka cire daga kanta zuwa kan wayarka.  Wannan na faruwa ne ba tare da saninka ba. Haka ma idan sakonnin Imel ne aka aiko maka, da zarar sakon ya diro cikin jakar Imel dinka da ke kamfanin Imel din, nan take manhajar Imel da ke wayarka za ta lalubo sakonnin Imel da ke kan wayarka ta gwama su da wadanda ke kan kwamfutar Imel na kamfanin. Idan t aga da bambancin adadi, sai ta aiwatar da musayar bayanai tsakaninta da wadanda ke kan kwamfutar kamfanin Imel dinka.  Wannan, a takaice shi ne abin da ake kira “Synchronize.”