Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Tambaya da Amsa: Sakonnin tes daga masu karatu (5)

Configure:

Kalmar “Configure” asalinta daga kalmar “Configuration” ne, wadda ke nufin “tsara hanyoyin mu’amala da waya ko kwamfuta ko wata manhaja ko tsarin sadarwa.” Duk wata kwamfuta ko wayar salula ko manhajar sadarwa tana zuwa ne da wani tsari da kamfani ko maginin ya dora ta a kai. Wannan tsari shi ake kira: “Default Settings.” Tsarin canja wadannan tsare-tsare da waya ko kwamfutar ta zo da su, shi ake kira “Configure.”

ADVERTISEMENT

Compress: Wannan kalma an samo ta ce daga asalin kalmar “Compression” wadda ke nufin tsarin nadewa da takura bayanai, don adana mizanin bayani mai girma a muhalli ko ma’adana takaitacciya. Wannan kalma ta sha bamban da kalmar “Decryption,” wacce ke nufin tsarin layance ko asirta bayanai. Ita wannan kalma tana nufin takura bayanai ne masu yawa, don adana su a ma’adana takaitacciya ko mara girma. Mu kaddara kana da bayani mai girman mizani 10GB. Ana iya takura wannan bayani ya zaman mizani 5GB ko kasa da haka.  Akwai manhajojin kwamfuta da wayar salula da yawa wadanda za a iya amfani da su don takura bayanai. Shahararru daga cikinsu su ne: “Windows Zip” da “7-Zip File Manager” da sauransu. Ana amfani da kalmar “Zip” don nufin “Compressing” bayanai zuwa muhalli takaitacce.

Debug: Kalmar “Debug” daga asalin kalmar “Bug” ne, wanda ke nufin wani kwaro, ko wata matsala da ke cikin wani abu. A fannin fasahar sadarwar zamani, kalmar “Debugging” na ishara ne ga tsarin gano kura-kuran da ke cikin bayanan gina manhajar kwamfuta.  Idan maginin manhajar kwamfuta ya gama rubuta umarnin da zai bai wa kwamfuta don aiwatar da su, a wasu lokuta akan samu matsala wajen kuskuren kalma ko harafi ko wani digo ko aya, wanda kwamfuta ke kasa fahimtarsa. Wannan zai sa da zarar an shigar mata, sai ta kasa aiwatar da umarnin da aka ba ta. Wadannan kura-kurai da ke cikin umarni, su ake kira: “Bugs.”  Tsarin nemo su da tantance su don cire su ko gyara su kuma, shi ake kira: “Debugging.” Kalma ce shahararriya a wajen magina manhajar kwamfuta, wato: “Prgrammers.”

ADVERTISEMENT

Wadannan a takaice su ne ma’anonin kalmomin da ka bukata. Da fatan ka gamsu.

Tambaya: Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuh. Ranka ya dade, gaskiya muna jin dadin yadda kake kara mana karfin gwiwa ta hanyar ilimantar da mu. Don Allah ina bukatar a fahimtar da ni yadda zan saita manhajar Android Studio da kuma hanya mafi sauki da zan fara kirkirar Android App. Na gode.

 

Amsa: Wa’alaikumus salam, barka dai. Bayani kan wannan maudu’i abu ne mai fadi, takaita bayani ba zai gamsar da kai ba. Don haka, ga dan abin da ya sauwaka nan na kalato maka.

Dabaru da kayan aikin gina Manhajar Android:

Bayan littattafai da kwarewa da kuma manhajoji, mai karatu na bukatar abubuwa guda uku muhimmai kafin ya gwanance wajen tsarawa da gina ingantattun manhajojin Android. Idan ba mu mance darasin makon jiya ba, mun yi bayani ne kan matakan ilimi ko kwarewa da a halin yanzu ake bi wajen gina wadannan manhajoji, tare da nuna cewa matakin karatu da kwatanta abin da aka karanta a aikace, su ne manyan tubali wajen gwanancewa a wannan sana’a. A wannan mako za mu karkare wannan doguwar kasida ce da bibiyar hanyoyi uku na karshe, don cimma burin mai buri a wannan fage.

Sadaukar da lokaci: Dayan biyu ne, ko dai ya zama ka dauki wannan fage ne don sha’awa kawai (hobby), don ka rika gina manhajoji kana amfani da su ko raba wa mutane suna amfani da su, ko kuma ya zama kana son daukar wannan fage ne a masayin sana’a. Zai iya yiwuwa kuma kana son farawa da matakin farko ne, daga baya, iya gwargwadon yadda ka ga ka kware, ka nausa zuwa mataki na biyu. Ko ma dai mene ne, dole sai ka sadaukar da kanka wajen wannan aiki. Domin fannin gina manhajar kwamfuta (Programming) ba fannin ’yan kailula ba ne, a yi yau, ba za a sake dawowa ba sai bayan wata ko watanni. Idan ka fara karatu (a aji ne ko ta hanyar littattafai), dole ne ka ciyar da lokacinka a kowane lokaci, dare da rana safe da yamma. Karatu ne da ya shafi karantawa da kwatantawa. Duk abin da ka karanta, to dole ne ka kwatanta shi, don ilimin da fasahar da hikimar su tabbata a kwakwalwarka. Hakan kuwa ba zai yiwu ta dadi ba, sai ka sadaukar da kanka.

Da yawa cikin masu karatu sun sha turo mini tambayoyi cewa wadanne hanyoyi za su bi wajen koyon ilimin gina manhajar kwamfuta? Wato “Computer Programming.” Ga wadanda na samu damar ba su amsa, nakan shawarce su da su tanadi lokaci ne, a karon farko, domin sai ka bai wa karatu lokacinka, sannan zai ba ka kansa, ka kwashi abin da kake so.  Amma idan dabi’arka ita ce kailula, ka je ka nemi wani fannin daban ba wannan ba. Wannan ita ce gaskiya mai daci da ta kamata mai karatu ya san ta, ya fahimce ta, sannan ya hakikance samuwarta don cin nasara.

Kayan Aiki: Kayayyakin aikin da kake bukata sun kai biyar zuwa shida. Abu na farko dai shi ne, dole ka mallaki kwamfuta, nau’in tafi-da-gidanka (Laptop) ko ta kan tebur (Desktop), wacce za ka iya jona ta da Intanet lokaci zuwa lokaci. Sannan dole ne ya zama tana dauke da manhajar da za ta iya riskar da kai zuwa Intanet, wato Manhajar Lilo ke nan (Internet Browser).  Amfanin mallakar kwamfuta kuwa shi ne, duk abin da za ka gabatar a kanta zai gudana; daga farko har karshe.  Sannan dukan manhajojin da za ka yi amfani da su wajen wannan aiki, daga Intanet za ka saukar da su. Wani abin sha’awa ma shi ne, dukan wadannan manhajoji da tsare-tsare kyauta ne, ba za ka kashe ko kwandala ba.

Bayan mallakar kwamfuta da karikitanta, sai manhajoji guda hudu da za ka saukar daga gidajen yanar sadarwa daban-daban. Kamar yadda na fada a baya ne, dukan wadannan manhajoji kyauta ake bayar da su.

Manhajar farko ita ce manhajar JABA. Za ka samu wannan manhaja mai dauke da tubalin gina manhajar kwamfuta da yaren Jaba ne a http://jaba.oracle.com/downloads Duk da cewa zubin Jaba a halin yanzu yana kan na takwas ne (Bersion 9 – Jaba 1.9), har yanzu ba a fara gina manhajar Android da zubin Jaba na bakwai ma ba, sosai, balle na takwas.  Idan ka je za ka saukar da zubin Jaba na shida ne (Jaba 6, ko Jaba 1.6). Bayan haka, akwai nau’uka wajen uku ne – Jaba Runtime Enbironment, da Jaba EE, da Jaba SE. Sai ka saukar da Jaba SE, wato “Standard Edition” ke nan. Bayan ka gama saukarwa sai ka loda (Install) wa kwamfutarka.

Manhaja ta biyu ita ce manhajar “Android SDK,” wato tubalin da ke dauke da tsare-tsaren gina manhajar Android. Cibiyar aikin ke nan, gaba daya. Wannan za ka same ta a gidan yanar sadarwar Android, kai-tsaye.  Sai ka saukar amma bayan ka gama saukarwa (Downloading), ba loda (Install) wa kwamfutarka za ka yi ba, domin ba dunkulalliyar manhaja ba ce irin ta al’ada. Za ka nemi muhalli ne a ma’adanar kwamfutarka (Dribe C:), sai ka bude sabon burgamin adana bayanai (Folder), ka adana a ciki.  Idan ba canja mata suna aka yi ba, za ka ga sunan kamar haka: android-sdk-windows. Da zarar ka adana wannan tubali a muhallinsa, sai ka zarce Intanet don neman makami na uku, wato allon rubutu ke nan.

Manhaja ta uku ita ce allon rubutu, wato “Tedt Editor.” Akwai nau’ukansu da yawa amma wanda ya fi shahara, ya fi sauki, sannan ya fi dacewa da tubalin Jaba SE da ka saukar a fari, shi ne: Eclipse Tedt Editor, wanda ke dauke da abubuwa da dama masu sawwake aikin. Babban aikin wannan allon rubutu, kamar yadda mai karatu zai ga shafinsa a tsakiya, a kansa ne maginin manhajar zai ta tsara yadda yake son manhajar ta kasance, a rubuce. Bayan ya rubuta, ya yi gwaji, sannan ya yi ’yan gyare-gyaren da suka kamata, akwai kwarangwal na wayar salula nau’uka daban-daban a jikin wannan allo, wadanda mai karatu zai rika amfani da su wajen gwaji. Wadannan kwarangwal su ake kira “Mobile Emulator.” Duk abin da ka gina, sai ka kira wannan kwarangwal na wayar salula, ka loda manhajar a ciki, za ta nuna maka yadda manhajarka za ta bayyana a hakikanin wayar salula. Amma kafin ka kai ga wannan mataki na fara gina manhaja, sai ka saukar da makami na karshe.

Wannan makami kuwa ba wata manhaja ba ce mai zaman kanta, a’a, karin tagomashi ne, wato “Plugins.”  Da zarar ka loda wa kwamfutarka waccan manhaja ta allon rubutu mai suna: “Eclipse Tedt Editor,” sai ka budo wannan allo, ka je sashen “Windows” da ke sama ka matsa, sai ka gangara can kasa, ka latsa: “Android SDK Manager,” nan take zai fara saukar maka da wadannan bayanan tagomashi. Wadannan bayanai ana kiransu “Eclipse Android Plugins” ne. Aikinsu kuwa shi ne su tabbatar kana gina manhajar da ta dace da babbar manhajar Android da ke dauke kan wayoyi ne.

Idan mai karatu bai mance ba, a baya mun yi bayani kan nau’in zubin Android, wato “Android Bersions.”  Wadannan nau’uka sun sha bamban, tunda ba lokaci daya aka gina su ba. Don haka, wannan dan aike mai suna “Android SDK Manager” shi zai saukar maka da dukan bayanan da suka dace da kowane irin nau’in Android ne. Domin da zarar ka yi yunkurin kirkirar sunan manhajar, tun kafin ka kai ga samar da sassanta, za a bukaci ka tantance nau’in Android din da kake son manhajar da kake ginawa ta dace da ita. Sai dai kuma idan kana saukar da wadannan bayanai, dole ne ka tanadi “Data” mai dimbin yawa, domin yana daukar lokaci, duk da cewa ya danganci nau’in bayanan da kake bukatar saukarwa. Da zarar ka gama saukarwa kuma, sai ka kama aiki.

Wannan kadan ne cikin abin da ya samu na bayani kan yadda za ka fara aiwatar da wannana aiki. Da fatan ka gamsu, ina yi maka fatan alheri.