✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tambaya da Amsa: Sakonnin tes daga masu karatu (6)

Tambaya: Assalamu alaikum da fatan kana lafiya, Baban Sadik. Don Allah ka taimaka min da dabarun yadda zan iya hawa profile dina na N-Power. Kuma…

Tambaya: Assalamu alaikum da fatan kana lafiya, Baban Sadik. Don Allah ka taimaka min da dabarun yadda zan iya hawa profile dina na N-Power. Kuma sai da waya kirar Android ne kadai ake iya shiga Profile din ko duk Smart Phone mai browser? Ka taimaka min, na gode. Daga Maman Abdulsamad Gombe.

Amsa: Wa alaikumus salam, barka dai Maman AbdusSamad. Dangane da yadda ake hawa shafin N-Power, duk wayar da ake iya hawa Intanet da ita ana iya isa ga shafinsu, ba dole sai nau’in Android kadai ba. Abin da ke da muhimmanci kadai shi ne, ya zama an samu cikakken adireshin shafin da ake son hawa. Wannan ita ce ka’ida da fatan kin gamsu kuma Allah Ya taimaka, amin.

Tambaya: Assalamu alaikum, da fatan Baban Sadik yana lafiya. Sunana Isma’il Salisu, dalibin Computer Science. Ina aji 3 a Jami’ar Umar Musa ’Yar’aduwa da ke Katsina. Ina godiya gare ka, musamman bisa kokarin da kake yi na ilimantarwa. Ina da sha’awar fannin Networking da Telecoms (rubuce-rubucenka sun kara zaburar da ni da sa mini sha’awa na wannan fage mai fadi) kuma yanzu haka ina fuskantar horarwa ta SIWES ko IT, shi ne nake neman shawararka. Ina ya kamata in je domin samun horarwa ta aiki sosai?  Na gode, bissalam.

Amsa: Wa alaikumus salam, Malam Isma’il. Na yi farin cikin jin cewa kana samun gamsuwa cikin abin da kake karantawa a wannan shafi mai albarka a duk Juma’a.  Dangane da batun tsarin horarwa na SIWES ko IT, kawai ka nemi hukumar da ka san suna da amfani da tsare-tsare da hanyoyi da na’urorin sadarwa na zamani, don yin wannan aiki a tare da ita. Wannan shi ne zai taimaka maka wajen ganin yadda ake tafiyar da na’urorin sadarwa na zamani cikin sauki kuma a aikace. Amma idan hukuma ko kamfani ko ma’aikatar da ka je ba su da wadannan na’urori (irin su kwamfuta da sauransu), to sai dai ka yi ta zama kawai kuna kallon juna kai da sauran ma’aikatan da ke wurin.

In so samu ne, ka samu kamfani ko hukuma ko ma’aikatar da ke aiwatar da aikin a aikace. Irin su gidajen talabijin ko jarida ko kafafen watsa labarai na rediyo na gwamnati ko masu zaman kansu. Hakan idan hukumar gwamnati ce, ya zama suna da wadannan kayayyaki da hanyoyin sadarwa na zamani. Samuwar wadannan kayayyaki ne za ta taimaka maka wajen ganin aikin a aikace, musamman ma a fagen hada alaka tsakanin kwamfutoci (Networking). Duk kamfani ko hukuma ko ofishin da ke da kwamfutoci da ake aiki da su kuma suke hade da juna, to, kana da aikin yi a wurin.

Wanann shi ne dan abin da zan iya ba ka na shawarwari a halin yanzu. Ina kuma yi maka fatan alheri a duk inda za ka samu kanka. Da fatan ka gamsu.

Tambaya: Salamun alaikum Baban Sadik, Allah Ya sa kana nan lafiya tare da iyalanka amin. Don Allah Baban Sadik ina son ka yi mini bayanin yadda zan yi in bude shafin Twitter a wayata. Wassalam ka huta lafiya, ni ne 08056526803.

Amsa: Wa alaikumus salam, barka ka dai. Bayani kan yadda ake budewa ko yin rajistar shafin Twitter ba wani abu ba ne mai tsayi. Ka garzaya shafin Twitter da ke: <http://www.twitter.com> sai ka matsa alama mai take: “Sign Up” da ke can sama daga kuryar dama. Kana matsawa za a budo maka shafin da ke dauke da fom din da ake son ka cike, kafin a yi maka rajista. A yayin da kake cike fom din ne za ka zabi suna (username) da kalmar sirrin (password) da za ka rika amfani da su wajen hawa shafin a duk lokacin da ka tashi hawa.

Bayan haka, idan kana da waya mai dauke da babbar manhajar Android ko Windows Phone ko iOS na kamfanin Apple, kana iya zarcewa cibiyar manhajojin wayar (“Play Store” a Android, ko “Store” a Windows Phone, ko kuma “App Store” a wayar iPhone), don saukar da manhajar Twitter, wadda za ta sauwake maka isa ga shafin a duk lokacin da ka tashi bukata.

Wannan shi ne takaitaccen bayani kan yadda za ka iya mallakar shafi a manhajar Twitter. Da fatan ka gamsu kuma ina yi maka fatan alheri, na gode.

Tambaya: Salam, a cikin wata kasidarka da na karanta a baya, na ga ka rubuta cewa duk kwakwalwarmu iri daya ce. Sai dai kuma ni na kasa samun natsuwa da hakan, domin kuwa kai da kanka ka san cewa akwai ire-irenku (gifted); akwai kuma ire-irenmu (ordinary). Bayan haka, don Allah ina so in san tarihi na hakikanin abin da ya faru a Yakin Duniya na 1 da na 2. Wadanne kasashe ne suka fafata kuma mene ne sila? Sunana Junaidu Sakkwato, 09035907765.

Amsa: Wa alaikumus salam, barka kadai Malam Junaidu. Dangane da bayanin da na yi cewa duk kwakwalwarmu iri daya ce, ina kokarin tabbatar da cewa babu wani bambanci tsakanin kwakwalwarmu da ta Turawa da suke ta kirkirar abubuwa masu ban sha’awa da ban mamaki a fagen sadarwa. Ma’ana, wani abu ne da Allah Ya bai wa kowane jinsin dan Adam, ba wai Turawa kadai aka kebe da wannan baiwa ba. Idan muka dage, tare da samun yanayi irin wadanda suka samu kansu a ciki da tsari irin wanda kasashensu suke ciki, muna iya kera abin da ya fi wannan ma. Wadannan su ne bambance-bambancen da ke tsakaninmu da su. Don haka mu daina ganin cewa mu ba kowa ba ne, Turawa ne kadai masu hazaka ko kokari.

Wani abin sha’awa ma shi ne, galibin kamfanonin waya na duniya suna da ma’aikata bakaken fata, musamman ’yan Najeriya da sauran kasashen Afirka. Kuma da yawa cikin abubuwan da muke gani a wayoyin salularmu, kusan su suke kirkirarsu. Wannan ke nuna ashe dama ce kawai ba mu samu ba.

A daya bangaren kuma, bayani kan Yakin Duniya na Daya da na Biyu, ba ya cikin maudu’in wannan shafi nawa kuma a gaskiya ba ni da wata cikakkiyar masaniya a kai. Wannan shafi, kamar yadda ka fi kowa sani, ya mayar da hankalinsa ne ga bincike kan Kimiyya da Kere-Kere. A karshe, ina fata za ka yi hakurin rashin samun amsar tambayarka kan wannan maudu’i.  Allah Ya sa mu dace, Ya kuma kara mana ilimi da fahimta, amin. Na gode.

Tambaya: Salamun alaikum, da fatan alheri a gare mu baki daya. Kwamfutata ce kirar “DELL” kwana biyu take min wani abin da ba na ganewa. Idan na kunna ta da safe ba za ta kawo ba sai ta dauki lokaci kamar wajen awa daya ko fiye da haka kafin ta kawo. Sannan ta sake daukar lokaci kafin ta bude. Na kai wajen gyara aka ce mini wai “Processor” ne ya lalace. Aka canja shi amma duk da haka ba ta daina ba. Na koma aka sake cewa wai “Power Pack” ne ya samu matsala, shi ma aka canja amma duk da haka ba ta daina ba.  Mene ne abin yi?

Amsa: Wa alaikumus salam, barka dai. Daga bayananka, akwai alamar kwamfutarka ta kusan kwantawa dama, ma’ana ta kusa mutuwa murus. A ka’ida, bai kamata a ce kwamfuta na daukar kusan awa guda ba, kafin ta gama kunnuwa. Kamar yadda ka ce, a karon farko masu gyara sun ce laifin “Processor” ne, daga baya kuma suka ce laifin “Power Pack” (ko kuma “Power Supply Unit” – PSU), hakan na nuna cewa matsalar da kwamfutar ke fuskanta ba daya ba ce; matsaloli ne masu dimbin yawa. Kasancewar ba ka yi min bayani nau’in kwamfutar ba da nau’in babbar manhajarta ba da kuma tun yaushe ta fara wannan dabi’a ba, ba zan iya cewa ga hakikanin abin da ke damunta ba.

Zai iya yiwuwa tsohuwar kwamfuta ce da zamaninta ya shude amma aka dora mata babbar manhajar kwamfuta ta zamanin yau. Wannan zai iya jefa ta cikin wannan yanayi. Zai iya yiwuwa kuma ka yi ’yan shige-shige ne da ita a Intanet, ko ka jojjona mata ma’adanar Filash ko babbar ma’adanar kwamfuta ta waje (Edternal Hard Dribe) masu dauke da kwayar cutar kwamfuta (Computer Birus) har suka cakume ta; wannan na iya jefa ta cikin wannan yanayi. Har wa yau zai iya yiwuwa kuma duk ba dayan wadannan dalilai, tana dai fama ne da karancin ma’adanar wucin-gadi (RAM), shi ma yana iya jefa ta yanayi makamancin wannan. Wadannan kari ne kan wadancan dalilai guda biyu da mai gyara ya ba ka.

Ni dai shawarata ita ce, in dai tsohuwar kwamfuta ce wacce ta ji jiki, to canja ta kawai shi ya fi zama lafiya. Amma idan ba tsohuwa ba ce can, kana iya canja wajen mai gyara, ka samu wani kwararre wanda ya san kan kwamfuta, ba wanda zai rika kirdadon matsalarta ba, don gano hakikanin abin da ke damunta, ko kuma, a karshe, ya ba ka shawarar kan abin da ya kamata ka yi.

Wannan shi ne abin da zan iya cewa. Ina yi maka fatan alheri da dacewa wajen samun maslaha ga wannan baiwar Allah mai fama da cututtuka iri-iri. Da fatan ka gamsu da gajeren jawabina, na gode.