Search
Subscribe
Tambayoyi da amsoshi 100 domin mata (4)

Tambayoyi da amsoshi 100 domin mata (4)

Tambaya ta 16: Kashi nawa ne mata suka kasu dangane da haila?

Amsa: Mata sun kasu kashi uku: (1) Wacce ta fara (2) Wacce ta saba (3) Mai ciki.

 

Tambaya ta 17: Nawa ne mafi yawan kwanakin haila ga wacce ta fara?

Amsa: Mafi yawan kwanakin haila ga wacce ta fara kwana goma sha biyar (15) ne.

 

Tambaya ta 18: Mene ne hukuncin wacce ta saba yin haila?

Amsa: Wacce ta saba al’ada ta san kwanakinta

Amma idan jinin ya wuce mata ya karu a kan kwanakin da ta saba, to sai ta kara kwana uku matukar karin kada ya wuce kwana goma sha biyar. Kuma na yi bayanin yadda za ta yi karin kwanaki a kowane wata. Na yi bayani a baya.

 

Tambaya ta 19: Mene ne hukuncin mai ciki?

Amsa: Hailar mai ciki bayan ya yi wata uku to hailar ta kwana goma sha biyar ko kafin sha biyar.

Amma bayan ciki ya yi wata shida kwana ashirin ne, wato mafi yawan kwanakin hailar. Amma in ya wuce hakan, to ya zama jinin ciwo, sai ta yi wanka ta ci gaba da ibadarta kamar yadda bayani ya gabata a baya.

 

Tambaya ta 20: Mene ne hukuncin mata idan jinin ya dauke?

Amsa: Idan jinin ya dauke sai ta kirga kwanakinsa har sai ta cika aI’adarta kamar yadda ta saba wato idan jini ya dauke kafin ya kai kwanakin da ya saba yi mata sai kuma ya dawo, to sai ta rika kirga kwanakin har sai ya kai iya kwanakin da ta saba yi. Kamar jinin ya zo yau sai ya dauke gobe sai kuma ya dawo jibi, to sai ta hada na yau da na jibin ya zama kwana biyu ke nan, to haka za ta yi ta lissafi har sai ya cika kwannakin da ta saba.

 

Tambaya ta 21: Shin yana halatta ga mai haila ta yi Sallah da makamantan Sallar?

Amsa: Ba ya halatta ga mai haila ta yi Sallah da Azumi da Dawafi da shafar Alkur’ani da shiga masallaci.

 

Tambaya ta 22: Shin za ta rama daga cikin Sallah ko a Azumi?

Amsa: Za ta rama Azumi amma ban da Sallah.

 

Tambaya ta 23 : Shin karatunta wato (mai haila) ya halatta?

Amsa: Eh, karatunta ya halatta.

 

Tambaya ta 24: Mene ne a jikinta ba ya halatta ga mijinta a lokacin da take haila?

Amsa: Farjinta ne ba ya halatta ga mijinta, kuma abin da yake tsakanin cibiyarta zuwa gwiwoyinta a lokacin da take haila, har sai ta yi wankan tsarki, wato wankan daukewar jinin haila.

Mu kwana nan

Za a iya samun Ahmad Adamu Kutubi (SP) ta 08036095723

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin