✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tambayoyi da amsoshi daban-daban kan kiwon lafiya 1

Ina fama da larura tsawon shekara 20, ko yaya na wahala sai in ji kamar raina zai fita ko kuma kamar mai jin yunwa; na…

Taswirar makogwaro da tumbi da hanjin Dan AdamIna fama da larura tsawon shekara 20, ko yaya na wahala sai in ji kamar raina zai fita ko kuma kamar mai jin yunwa; na yi ta tuka kamar zan yi amai. Na je asibiti a kan wannan matsala amma ina so likita ya yi man karin bayani.
Daga Isah Mai Atamfa Katsina
Amsa: E, wannan alamu naka suna nuni da irin alamun cututtukan ciki irin na olsa da dangoginta. Ka san ba gyambon ciki kawai akan samu a ciki ba, mun sha bayani cewa wasu ba gyambo ba ne a cikin, wasu miki ne kawai, wasu kuma ba ma a cikin tumbi matsalar take ba, wasu a karshen makogwaro wasu kuma a farkon hanji ake samun matsalar. Yawanci masu wannan matsala suna rasa inda za su sa ransu don zafi idan suka ji yunwa (gyambon hanji), wasu kuma sai sun ci abinci abin yake motsawa (gyambon ciki), su rika jin tashin amai. Wasu sai sun ci sun koshi sun kwanta barci idan abinci bai narke ba.
Idan aka yi sa’a, akan samu wasu su warke idan an sha magunguna yadda likita ya zayyana kuma na tsawon watanni, wasu kuma sai an yi aikin tiyata, wasu ma babu tabbacin warkewa.
Yawanci ba a bambancewa sai an shiga cikin naka da wata ’yar kyamara an haska an ga wane irin ciwon olsar ne da kai. Don haka idan ka sake komawa za ka iya yi wa likitan maganar wannan gwajin.
Me ke kawo mikin nan na baki, wato kawai ka ji ’yar karamar tsaga daga ciki, daga bisani a ga ya zama ciwo, har ta kai ga ko ruwa ya taba wurin, za ka ji da zafi?
Daga Adam Gobir, Wuse
Amsa: Shi kuma irin wannan miki rashin sinadaran karin karkon jiki ne ke samar da su, wato sinadarai irinsu bitaman na rukunin B da C, da sinadarin Folic Acid. Idan suka yi karanci a abinci, to za su iya yin karanci a cikin jini ma. Da wuya a same su a yawa-yawan abincin da muka fi ci, wato irinsu tuwo ko shinkafa ko wake. Kayan marmari na itatuwa da ganyayyaki su ne suke dauke da wadannan sinadarai. kwayoyin cuta sukan iya shiga mikin su sa wurin ya fara zogi.
A irin wannan lokaci na azumi ma mutane da yawa sukan samu irin mikin saboda karancin sinadaran da muka lissafa. Idan mutum yana zazzabi ma zai iya samu, abin da ake kira huciyar zazzabi, kuma duk kwayoyin cutar da kan sa zazzabi za su iya shanye sinadaran a jini, a samu mikin. Idan ma lafiyar mutum kalau wato ba zazzabi yake ba, idan yana da karancin sinadaran, aka mauje masa baki ko ya buge ta hanyar hadari to zai yi saurin samun tsagewar cikin bakin.
A ina zan samu asibitin kunne? Kuma yaya zan yi, ka ba ni shawara.
Daga A. Kurma I.N.E.C. Kaduna
Amsa: Abu ne mai sauki tun da kuwa a nan cikin garin Kaduna akwai babban asibitin kunne da ma na ido. To idan kana so a duba lafiyar kunnen naka, can ya kamata ka je ka yanki kati. Ban san yadda tsarinsu yake ba, amma yawancin manyan asibitoci ko ka yanki kati idan dai ba wani aikin gaggawa ba ne da za a ceto kunnen naka a take, ba za a ganka ranar da ka yanki katin ba sai dai a rubuta maka ’yan kwanaki ko makonni na dawowa ganin likita. Don haka hakan din za ka yi.
Me ke kawo rashin barci da kuma yawan tunani?
Daga D. Y. Funtuwa
Amsa: Akwai abubuwa da dama masu sa irin wannan alamu da ka zayyana, sai dai kuma su kansu alamun da ka lissafa, daya kan iya haifar da daya, wato rashin barci kan iya haifar da yawan tunani kuma yawan tunani kan iya haifar da rashin barci. Kusan duka biyun dai idan aka hada su aka samu ana fama da su a lokaci guda, alamu ne na ciwon kwakwalwa amma a daidaikunsu wasu abubuwa daban kan iya haifar da su. Mai irin wadannan alamu su biyu sai ya tuntubi asibiti inda za a hada shi da likitan kwakwalwa.
Ni dai ina yawan mafarkai ne cikin dare saboda kashi 2 bisa 3 na barcina duk mafarki ne kuma hakan yakan haddasa min ciwon kai da safe.
Daga Zainab A. Sakkwato
Amsa: E, kwarai kuwa yawan mafarki a barci kan iya sa barci ya rika yankewa kuma idan rashin barci ya taru a jiki sai a rika jin ciwon kai. Yawan mafarki da dare na nufin akwai wata matsala a rayuwar mutum da rana ke nan, ko dai ta zamantakewar aure ko iyaye ko matsala ta abin hannu ko ta rashin kwanciyar hankali a garuruwan da ake dauki-ba-dadi saboda zullumi da tsoro, da dai sauran matsalolin rayuwa.
Ke ma ya kamata ki je babban asibiti bangaren da ake duba kwakwalwa wato sakatiri a bincike ki.
Wani lokaci zan ji fitsari amma sai na rike a lokacin da ya matsa ni ban je na yi ba, lokacin da zan je na yi kuma kafin na shiga bandaki ya fara zubowa. Ko hakan yana nuni ina tare da wata matsala?
Daga M. B.
Amsa: E, idan ke mace ce wannan ba matsala ba ce, tunda sai kin tara shi a mara ya cika sosai. Marar mata ba ta iya rike fitsari kamar ta maza. Idan kuma kai namiji ne kuma musamman ma idan ka manyanta, dole ka je a bincike ka.

LAFIYAR MATA DA YARA

Mene ne amfanin ba jariri nonon uwa zalla na wata shida? Mu na da yaro da ya fara cin abinci tun bai kai wata shida ba za mu ci gaba da ba shi.
Daga dayyabu, Kano
Amsa: Nonon uwa na da amfani ga jariri kwarai da gaske kuma yana dauke da ruwa da abinci da sinadarai da dama wadanda jariri yake bukata a watanni biyar zuwa shida na farkon rayuwarsa.
Akwai bambanci a lafiyar jaririn da aka ba nonon uwa da wanda aka ba shi nonon saniya (ko na akuya ko rakumi a wasu kasashen). Koda an ga jaririn da aka ba madarar shanu ya yi kato, sinadaran da ya sha a madarar ba daya suke da na nonon uwa ba. Yawancin akan samu sinadaran da suke karanci a madarar shanu, a samu wasu kuma sun yi yawa. A na uwa kuwa komai na nan daidai da bukatar jariri.
Ruwan madarar uwa da abin da ke ciki canzawa yake idan jariri na girma. Kalar madarar a kwanakin jariri na farko ba fara bace, za a gan ta dorawa-dorawa, wanda ba madara kawai ba ne a ciki, sinadaran sa wa jariri kwayoyin garkuwar jiki don hana kamuwa da cututtukan jarirai. Bayan wadannan kwanaki sai ruwan ya canza kala, ya kara komawa fari, ya kara suga da sinadarai masu gina jiki, haka har yaro ya kai wata shida, kafin ya sake canza dandano, ya kara yawan suga har ila yau da sinadarai daidai bukatar jariri. Haka dai har a yaye jariri. Sai an tabbatar uwar ba ta da isasshen ruwan madara ne ake hakura a kara da madarar shanu. Ko kuma idan uwar tagwaye ko ’yan uku ta haifa, wanda a wannan yanayi zai wuya nonon uwa zalla ya ishe su.
Ba a hada ruwa da ruwan nono tunda shi nonon yana dauke da iyakacin ruwan da jariri yake so. Manufar hana jariri ruwa a watannin farko ba wai mugunta ba ce irin ta likitoci kamar yadda wasu suke fada, a’a ana jiye wa jariri shan kwayoyin cuta da ke cikin ruwan ne. Da yaro ya fara girma, kwayoyin garkuwar jikinsa sun yi karfi a wata biyar ko shida, to za a iya fara ba shi ruwa tsabtatacce, wato wanda aka tace aka tafasa. Ko ruwan roba ne ko na leda, an dai fi so a tafasa. Kayan ba da ruwan ma kamar bulunboti, ana so duk bayan kwana biyu a tafasa.
A wadannan watanni ne kuma akan iya fara ba yaro dan abinci mai ruwa-ruwa, yawanci irin abincin gwangwani wadanda aka sa wa sinadarai na kara kuzari da lafiya, wanda ba zai iya samu a nonon uwa ba.
An yi amanna yaron da aka yi wa irin wannan gatan da wuya ya samu matsalar gudawa ko ta ciwon ciki ko mura da tari, wadanda cututtuka ne da jarirai suka fi samu ta hanyar shan ruwa da kayan ba da ruwan irinsu cokali da kofuna. Ko ya samu ciwon ma nan da nan zai tafi, domin kwayoyin cutar ’yan kadan zai samu ba kamar wanda aka ba ruwa marar tsabta ba.
Ban da karin lafiya, shan nonon uwa na da muhimmmanci wajen kara soyayyar uwa da jariri. An yi amanna cewa jariri na son uwarsa fiye da kowace mace a duniya saboda shayar da shi da take yi. Ba a taba ganin jariri ya yi wa mamansa kyuya, duk saboda shayarwa.