✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tambayoyi da amsoshi daga bakin likita

Likita ka ce ina da hawan jini tun da awon jinina ya kai maki 150/100, to ni likitana bai ba ni wani maganin hawan jini…

Taswirar hoton mai cutar Asma yana shakar maganiLikita ka ce ina da hawan jini tun da awon jinina ya kai maki 150/100, to ni likitana bai ba ni wani maganin hawan jini ba, na Maleriya da na barci ya ba ni kuma na samu sauki. Kuma a lokacin mun dan yi sa-in-sa da wani ne, raina ya baci. Kuma ni yanzu ban wuce shekaru 32 ba.
Daga Usman Mu’azu, Funtuwa
Amsa: Ai ba ka ba da wannan bayani ba a tambayarka ta farko, wato cewa an baka maganin barci an sake aunawa an ga ya yi daidai. Ai da ka ba da wannan bayani tun farko ma da ba irin wannan amsa aka ba ka ba, domin lafiyarka kalau.
Na ga irin bayaninka dangane da ciwon sanyin kashi. Amma ina so na san ko akwai maganin da za a warke nan da nan, domin abin na damuna.
Daga Auwalu
Amsa: E, a gaskiya akwai cututtukan da a yanzu a likitance babu maganin warkarwa gaba daya sai dai masu saka ciwo ya lafa. Sanyin kashi yana daya daga ciki. Bamu sani ba dai ko nan gaba idan aka tsananta bincike.
Wai me ke kawo min rashin barci ne da yawan rama? Kuma lafiyata kalau ba na jin wani ciwo na damuna.
Daga Maryam, Fatakwal
A’a, yaya kuwa za ki ce ba ki jin wani ciwo na damunki ga shi kuwa kin lissafo alamun cututtuka biyu? Rama da rashin barci ai alamu ne na cututtuka da dama, wadanda za a iya cewa watakila kina da daya daga ciki. Ba za a lissafo irin cututtuka masu wadannan alamu ba kada ki ta fargaba, ko kuma ki ce likita ya ce kina da ciwo kaza. Ki dai je asibiti a Fatakwal din a samu a yi miki tambayoyi a bincike ki ta hanyar aune-aune da gwaje-gwaje.
Wai me ke sa mutum jin wata ’yar majina da ke makalewa a makoshi, in an yi kakinta ba ta fitowa kuma ba ta komawa ciki. Shin me ke kawo wannan kuma wane irin magani za a sha don samun waraka?
Daga Hussaini Muhammad, Sakkwato da Isah Kwafsi Ba Ka Soyayya
Amsa: To wannan shi muke ce wa ciwon makakin wuya ko sorethroat a turance. Ciwo ne mai yawan kama mutane manya da yara, mata da maza, mai kudi da talaka kuma na kowane sashe na duniya in dai mutum na shakar iska. Sai dai na wani ya fi na wani zafi da makaki. Kusan yana daya daga cikin irin cututtukan mura wadanda kusan kowa ya taba yi, wato da wuya a samu wanda bai taba jin irin wannan ba.
kwayoyin cuta na cikin iska ne ke shiga makoshi su yi zamansu, ta yadda in dai kana numfashi to wata rana sai ka shake su. kwayoyin yawanci na birus ne, akwai kuma na bacteria. Yawanci cikin kwana uku zuwa biyar makakin yake tafiya ko an sha magani ko ba a sha ba.
Idan mutum ya samu irin wannan ba sai ya je asibiti a lokacin ba, ana so ya rika cin abu mai dan yaji kamar farfesu ko alewa mai yaji, wadanda za su sa makakin ya lafa. Sai kuma kayan itatuwa wadanda za su sa garkuwar jiki ta yi kaifi don su yaki kwayoyin cutar, sai kuma kurkure makogwaron da ruwan zafi mai gishiri, shi ma yakan iya kashe kwayoyin cutar. Idan makaki bai tafi ba bayan an yi wadannan to dole a je asibiti.
Yawanci a asibiti idan aka haska makogwaron aka leka, ba a ganin komai wanda ke nufin kwayar cutar birus ce, don haka ba sai an ba da magani ba, da kanta za ta tafi. A wasu lokutan kuma akan ga wani abu kamar majina kamar yadda ka yi bayani a like a jikin bangon makoshi, ko na hagu, ko na dama, ko kuma ma a duka bangon. To idan aka ga wannan ba makawa kwayar cutar bacteria ce kuma sai an ba da magani.
Ina so a yi min bayani, wai me ke sa masu cutar asma zubar da majina ba saurarawa, ga kuma yawan haki?
Daga Ahmad Lawan
Amsa: A’a, masu asma ba sa zubar da majina amma sukan yi haki. Don haka idan ka ga wani yana haki yana kuma zubar da majina, abin da ake kyautata zato shi ne kwayoyin cuta sun shiga huhu ke nan, kamar ciwon numoniya. Yawan haki ko nauyin numfashi ga mai asma kan faru ne saboda tsukewar hanyoyin numfashin.
karin bayani a kan azumi: A makon da ya gabata mun ba da bayani a kan ire-iren mutane marasa lafiya da za su iya yin azumi da wadanda ba za su iya yi ba. Muka ce mai ciwon suga ko hawan jini ko ciwon kiba azumi ya ma fi musu amfani a kan sauran masu lafiya, amma muka ce kowane maras lafiya ya tuntubi likitansa ya ji ko yana da wani zabi. To a wani taron kara wa juna-sani da likita ya halarta a kan azumin masu ciwon suga a cikin makon da ya gabata, masana cututtukan ciwon suga sun kara jaddada mana cewa mu fada wa jama’a masu ciwon suga cewa idan dai mutum sai ya yi allura sugansa yake sauka (wato masu ciwon sugan da ke kan allura), to fa ba shi ba azumi.
Idan kuma kwayoyin magani kawai yake sha, to zai iya yin azuminsa amma da kashedin sai ya yi sahur, domin muddin ya kuskura ya kasa riskar sahur, gara ma ya sha azuminsa saboda rikicewar da jikinsa zai iya yi. Idan aka samu wasu karin bayanai na masana ma a kan wannan batu, za a sanar wa masu bibiyarmu a wannan shafi.

LAFIYAR MATA DA YARA

Amsoshin tambayoyi

Shin me ya ke janyo karancin jini ga mai ciki? Haihuwa ta uku ana ce mini jinina ya yi kasa kuma har bayan na haihu da wata uku sai na rika jin jiwa tana diba ta. To wane irin abu ya kamata na rika ci domin samun jini sosai?
Daga Maman Faruk, Kano
Amsa: Ban da abubuwa masu kawo karancin jini a sauran mutane (kamar zubar jini ta hadarin abin hawa ko tsutsar ciki da dai sauransu), akwai abubuwa da dama da ke kawo karancin jini ga mai ciki amma abin da ya fi kwashe wa mai juna biyu jini shi ne dan da ke ciki, wato ko kin nemi abinci da magunguna masu kara jini ko ba ki nema ba, shi dai abin da ke ciki zai kwashi nasa daga jikinki daidai yadda yadda yake bukata.
Wasu masu juna biyun kuma sukan yi dan zazzabi ko na mura ko na cizon sauro ko na wani ciwo daban, wanda kwayoyin cuta kan kawo. Shi ma wannan ciwo yakan iya sa jini ya ragu domin kwayoyin cuta sukan lahanta jini.
Ban da kwayoyin cuta kuma, akan iya samun cewa an samu zubar jini kafin a haihu, wanda shi ma wannan zai iya sa karancin jini, wanda har yai sanadin zubewar cikin.
Wato dai duk abin da ya kawo karancin jini ga mai juna biyu zai iya sanadin zubewar ciki idan ba a dauki matakin maganin matsalar ba.
Abubuwa masu kara jini sun hada da korayen ganyayyaki kamar alayyahu, ugwu da zogale da sauransu. Sauran sun hada da nama, hanta, koda da makamantansu. Ko da mace mai juna biyu ta samu wadannan a kullum, yana da kyau a je asibiti a karbi magungunan karin jini, domin wadannan magunguna ba sa yawa a mace mai juna biyu sai dai ma su yi kadan.
Muna son karin bayani a kan kwanakin tsakiyar wata. Dama akwai watan Musulunci mai kwana 28 da me 32? Kuma idan al’adarta a farkon wata ko tsakiya ko karshe take yaya za ta gano kwanakin tsakiyarta?
Daga Ummu Ammar, Kano
Amsa: Irin wannan ce ta sa a rubutun na ce sai kin zauna da likita ko kwararriyar ungozoma idan kina son bayanin kwanan watan mace. Domin kamar yadda kika nuna a wannan tambaya taki, ashe ba maza ne kawai ba su san kirgen watan al’ada ba, har da wasu daga cikinku matan. Ba watan sama ne mai kwana 32 ba, watan al’adarku ake nufi, wato yawan kwanakin da za a samu kafin zagayowar wata al’adar. Ke wasu ma sukan kai kwana 35 al’ada ba ta zagayo ba, wasu kuma cikin kwana 20 ma.
Game da ciwon mara ga mata lokacin al’ada. Na je asibiti an ba ni magani, na amshi allura, na sha maganan Yarbawa amma har yanzu yana tashi. Mece ce shawara? Ko da gaske yana hana haihuwa?
Daga A’isha, Legas
Amsa: Ai ita ma irin wannan matsala har yanzu sai dai maganin da zai sa ki ji dama-dama, ba wanda zai nuna miki maganin da za a sha a ce yau ga shi kin warke. Akan dai samu cewa wasu suna daina samun matsalar idan sun haihu, wasu kuma sai sun daina ma al’adar suke samun sukuni. Ba kanshin gaskiya kuma a cewa wai irin wannan ciwon mara na hana haihuwa.