✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tambayoyi da amsoshin likita game da kiwon lafiya 1

Ina son ka yi mini bayani a takaice, wadanne irin kwayoyin cuta ne sauro ke sanya wa mutum? Daga Aminu Dankaduna AmanawaAmsa: kwarai kuwa ba…

Uwa da jaririntaIna son ka yi mini bayani a takaice, wadanne irin kwayoyin cuta ne sauro ke sanya wa mutum?
Daga Aminu Dankaduna Amanawa
Amsa: kwarai kuwa ba kwayar cutar maleriya kawai sauro ke sa wa ba, idan ya yi cizo, domin sauro iri-iri ne; akwai wanda ke sa kwayar cutar maleriya idan ya yi cizo, wanda irinsa ne ya fi yawa a nan Arewa. Akwai kuma masu dauke da kwayar cutar da kan sa ciwon shawara wato ciwon yellow feber, wadanda suka fi yawa a Kudancin kasar nan. A kasashen tsakiyar Afirka irin su Congo da Burundi da na kasashen Latin Amurka da wasu sassa na kasar Sin, akwai masu dauke da kwayoyin birus masu sa ciwo irin su zazzabin Dengue da wasu kuma masu dauke da kwayoyin na birus dai masu sa irin munanan zazzabi mai sa saurin kisa.
A can wajejen kasashen Indiya kuma akwai sauro masu dauke da kwayar cutar da kan sa wani irin ciwon gwaiwa ko ciwon tundurmi (wani ciwon kafa da za a ga ta yi suntuntun kamar ta giwa, wanda mu ma akan ga irin daidaikunsu a jikin masu bara a titi, wadanda idan hukumomi ko masu hali suka tsaya mawa, za a iya yi musu magani, kuma za su iya samun waraka). Shi ya sa kasashen da suka gane sauro suke yaka ba cutar da yakan haifar ba, saboda ko a ina yake a duniya zai iya sa wata cuta.
Ko likita zai taimaka min da karin bayani. Yarona ne aka yi masa allura ba ya takawa. Na je na yi wa likita bayani ya ce ba komai. Wani kuma ya ba shi magunguna kala uku. An ba shi ya sha amma yau wata uku ke nan yaro ba ci gaba. To idan aka yi wa yaro allura irin wannan, idan ta baci mene ne abin yi? Ko ta kashe jijiyoyin ke nan?
Daga Ilyasu A. Minna
Amsa: E, jijiyoyin laka suna da wuyar sha’ani. Idan aka taba su wato aka ji musu ciwo, suna da wuyar warkewa. Domin akan iya daukar shekaru ma ba su warke gaba daya ba. An yi wa yaro allura yanzu da wata uku ma, wanda shi ma wannan tsawon lokaci da aka dauka ba abu ne mai kyau ba. Kamata ya yi a ce tun da farko an tura ku babban asibiti wanda za a iya duba kafar sosai sa’annan a yi mata gashi, tun da abin jijiyoyin laka ya shafa, magani kawai ba ya taimakawa sai an yi gashi, wato physiotherapy. Don haka babban asibiti za ku nema wanda za a samu bangaren gashi, idan an ci sa’a ta farfado. Sa’annan a kiyayi zuwa allura a shagunan sayar da magani da wurin sauran mutane da ba su kware ba.
Wai me ke kawo furfura ne ga mutum dan shekara goma sha biyar, shin tsufa ne ko rashin lafiya? Ya mutum zai rabu da ita?
Daga Muhammad, Kogi
Amsa: Hausawa sun yi gaskiya da suka ce baiwa ce, don kuwa ba ciwo ba ne. Duk da cewa wasu masana suna ganin cewa idan mutum ya wahala sosai ko bai tsufa ba sumarsa za ta iya yin fari amma kuma dai akwai samari wadanda ba wata wahalar duniya a gabansu kuma suna da furfura, kuma ba shi da abin da zai magance ta, idan ba rini ba. Ka san ko wasu daga cikin tsofaffin gaske da yawa ma rina sumar suke ka ga kamar ba furfura.
A likitance ma wannan ba wata matsala ba ce, abin da ke faruwa shi ne, dama akwai wadansu sinadarai a jikin dan Adam da suke sa fata da suma baki. Idan aka samu wani abu ya sa suka daina fitowa, to dole fata da suma su yi haske. Misali, a jikin zabaya babu wannan sinadari don haka fatarsa da sumarsa farare ne.  A mutane da suka je kasashe masu sanyi, suka zauna suka dade a can, za a ga fatarsu ta dan yi haske kuma sumarsu ta fara furfura, saboda wannan yanayi na sanyi yana rage fitowar wannan sinadari.
Ko da gaske ne sinadarin kashe kwayoyin cuta na spirit wanda ake fesawa bayan an wa mutum aski yana kodar da suma ya sa ta yi furfura?
Daga Mujahid, Kaduna
Amsa: A’a, shi wannan sinadari shi kadai ba zai kodar da suma ba amma idan aka hada shi da wani sinadarin na kyamikal mai iya kodar da gashi to za su hadu su iya sa wa.
Me ya sa idan mutum ya yi rashin lafiya kamar mura ko zazzabi ko gudawa sai fatarsa ta yi duhu. Idan kuma ya warke sai ta yi haske?
Daga Alhussai Dakace Zariya,
Amsa: E, rashin lafiya takan taba duk jiki ne, kuma ita fata da yake ita ce madubin jikin, nuni kawai take da abin da ke faruwa. Ko zafin zazzabin da ake ji ai daga cikin jini hucin yake fesowa ya zo fata. Duhun fata dama yana nuni ne da karancin ruwa a cikin jiki a mafi yawancin lokaci, wanda kuma shi ne yake nunawa a fata, kuma duk yawanci rashin lafiyar da ka lissafo, wato mura ko zazzabi ko gudawa suna karar da ruwan jiki ai.
Zazzabi kona ruwan jiki yake a cikin jini, mura karar da ruwan jiki take ta hanci, gudawa karar da ruwan jiki take ta ciki. Da zarar kuma an kawar da wannan abu da ya kawo karancin ruwa, aka kuma kara ruwan sai ka ga jiki na sheki. karin ruwa kuma ba dole sai na asibiti ta jijiya ba, idan mutum ba ya amai ya yi ta shan ruwan gishiri da sukari ko ma ruwan gari, haka ko wani lemo sai ka ga an wartsake.
Ina fama da yawan majina wacce ke sauko mini daga kai zuwa cikin baki. Haka kuma duk lokacin da na ci abinci sai majina ta sauko ta baki ta hanci. Ina mafita?
Daga Yusuf Ladan
Amsa: Da walakin goro a miya. Yawan majina haka kawai mutum ba mura yake ba da akwai matsala. Ka samu ka je asibiti a duba ka. Idan kuma mura ce ba sai ka je asibiti ba, da kanta za ta tafi.

LAFIYAR MATA DA YARA

A makon da ya gabata likita ya yi bayani a kan hanyoyin kariya daga ciwon daji na mama, da na karanta sai hankalina ya tashi domin ina jin wani kullutu a kasan hammatata, amma shekaruna ba su fi sha bakwai ba. Akwai matsala ke nan?
Daga Nana, Potiskum
Amsa: A’a, ba mu ce kullutu a hammata ba, a kan maman muka ce duk wadda ta ji sai ta je an duba, duk da cewa idan aka ji a kan maman hade da karkashin hammatar matsala ne. Idan a karkashin hammata ne kawai to ana kyautata zaton kaluluwa ce, wadda kan samu idan mutum ya ji ciwo; kwayoyin cuta suka shiga, ko idan yana da maruru ko dai wani kurji mai durar ruwan diwa kamar taya-ni-muni (pimples).
Ni ma na ga bayanin hanyoyin kariya daga ciwon dajin inda ka ce yin amfani da kwayoyin ba da tazarar haihuwa ma na iya sa wa, to sauran dabarun fa irinsu allura?
Daga Muhammad Ibrahim
Amsa: Shi sinadarin da ke cikin wannan kwaya sunansa oestrogen, wanda ke cikin allura kuma progesterone. Kowanne na da nasa amfani da nasa illar. A asibiti ana yi wa kowace mace tambayoyi na irin hadarin da za ta iya shiga idan an ba ta wani sinadari. Misali, ba a ba mace mai kiba ko hawan jini wannan kwaya. Shi ya sa kuma mukan ce kowace mace ta tabbata ta yi wa ma’aikaciyar lafiya bayani cikakke kuma ta ba ta amsoshi cikakku. Ita ma ma’aikaciyar ta yi mata bayani cikakke na irin illolin kowacce dabara da irin abubuwan da za ta ji idan an ba ta. Bayan kwana biyu idana ba ta ji dadinsa ba sai a canza.
Likita me ke kawo rashin ruwan mama ga matar da ta haihu? Sau da yawa nakan ji an ce mace ta haihu amma ba ta da ruwan nono. Ina mafita?
Daga Ali Fancy, Garko
Amsa: Akwai abubuwa da dama masu kawo irin wannan. Akwai yunwa ko rashin isasshen abinci, akwai zullumi, akwai rashin isasshen hutu ko barci, akwai kuma ciwon damuwa (domin haka kawai wasu matan da sun haihu kuma maimakon murna sai ciwon damuwa ya shige su). Idan aka lura za a ga dayan wadannan ko ma fiye, to su za a duba a yi maganinsu.
Amma dama ruwan nonon farko da kan fara zuwa bayan mace ta haihu kadan ne, a wasu matan ma babu kwata-kwata sai jariri ya fara tsotso tukuna yakan zo. Wato wasu suna kuskuren barin jariri da yunwa bayan an haife na tsawon lokaci wai ana jiran ruwan nono ya zo, ka ga mace tana ta matsowa da hannu. Ba haka ya kamata ba.
Da an sa sabon jariri kan nono ya fara tsotso kwakwalwa kan fitar da wani sinadari wai shi prolactin, wanda zai bi ta jini ya zo kan maman ya ba da umarni kofofin da ke sakin ruwan nono su bude. Idan akai ta matsowa da hannu wannan sinadari ba zai sauko ba.