Da Dumi Dumi

Tambayoyi da sakonnin masu karatu ta imel da tes (3)

Assalamu alaikum Baban Sadik, Ina fata kana lafiya. Ina son zama daga cikin mabiyan shafinka na Dandalin Facebook ne, amma ban san sunan shafin ba. Shi ya sa nake son ko za ka taimaka min da sunan, saboda in yi “Like’’ don amfana da abubuwa masu amfani. Na gode. Sunana Sa’idu Abubakar daga Jihar Nasarawa: 09080080326

Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Sa’id. Shafina da ke dandalin Facebook, wanda na bude shi musamman don fadakar da masu karatu, ana iya samunsa a wannan adireshin ne: www.facebook.com/taskarbabansadik <http://www.facebook.com/taskarbansadik>.  Da zarar ka shigar da wannan adireshin, za ka samu shafin, amma ba za ka iya karanta dukkan bayanan ba, sai ka shigar da suna (username) da kalmar sirrinka (password) na Facebook.  Idan ba ka da rajista da Facebook, sai ka yi rajistar sabon shafi.  In kuma shigar da adireshin zai maka wahala, idan kana da shafi a Facebook sai ka nemi: “Taskar Baban Sadik”, nan take za a budo maka shafuka masu makamancin sunan, za ka ga nawa shafin dauke da hotuna da kuma makaloli masu alaka da fannin kimiyya da fasahar sadarwa. Daga nan sai ka riski shafin ka matsa alamar “Like” don a rika sanar da kai a duk saa’r da na sabunta bayanan da ke shafin.

Muna murna da zuwanka.  Allah Ya sa mu amfana da juna baki daya.  Na gode.

Assalamu alaikum Baban Sadik, matsalata game da shafin Facebook dina ne; idan na shigar da kalmar sirri sai ya nuna min sunan wani.  Idan na sake nemo shafin, to, sai na ga duk abokaina babu ko daya.   Wace hanya zan bi domin hana masu yin kutse a shafin facebook dina?  Daga Ahmed Garba Zubarau, Auyo, Jigawa. 09070608002

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Ahmad. Wannan ke nuna cewa shafin ya samu matsala ke nan.  Ta yiwu wani ya kwace shafin ne, tunda har idan ka hau ba ka ganin sunanka sai sunan wani, kuma shafinka ne.  Abin da zan iya fahimta dai a takaice, shi ne, wani ya kwace shafinka. Hanya mafi sauki ita ce ka kai koke ga hukumar Facebook don su taimaka maka cikin sauki. Wannan wani abu ne da suka saba yi. Domin ko na ce zan yi maka bayani filla-filla kan yadda za ka dawo da shafin ba lalle ba ne ka fahimta cikin sauki. Ka shiga wannan adireshin:  <https://m.facebook.com/hacked>.

ADVERTISEMENT

Da zarar ka hau shafin, za ka ga shudiyar alama mai take: “My Account is Compromised”.  Idan ka matsa, za a bukaci wasu bayanai daga gare ka. Dole ka ba su bayanai na gaskiya, kuma tabbatattu. Da su za su yi amfani wajen karbo maka shafinka.  Da fatar ka gamsu, kuma ina yi maka fatar alheri.  Allah Ya sa a dace, amin.

Salamun alaikum Baban Sadik, yaya fama da mu?  Allah Ya yi tukuici da Firdausi, amin. Tambayata ita ce: don Allah ko akwai matsala idan kullum ina sa wayata caji a kwamfuta?  Daga Al-Ameen Zariya. 07035586603

Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Al-Ameen. A iya sanina babu wata matsala don ka sa wayarka caji ta hanyar amfani da wayar caji a kwamfuta. Domin yana daga cikin abin da aka kintsa a cikin wayar salula, ya zama ana iya amfani da  makamashin lantarkin jikin kwamfuta don yin cajin batirinta. Na sanar kuma zan kara sanarwa, cewa duk asalin makamashin lantarkin da za ka yi amfani da shi wajen cajin wayar salula, dole ne ya zama mizanin karfinsa ya dara na mizanin batirin wayar.  Na yi dogon bayanai a tambayar da wani dan uwa ya yi kan tasirin cajin waya da na’urar “Power Bank”, watanni uku da suka shude. Za ka iya samun wannan bayani cikakke a wannan adireshi da ke Taskar Baban Sadik: https://www.babansadik.com/sakonnin-masu-karatu-2019-11/ <https://www.babansadik.com/sakonnin-masu-karatu-2019-11/>.

Dangane da haka, idan ka yi la’akari da mizanin ma’adanar lantarkin kwamfuta da na wayar salula, ko kusa na kwamfuta ya fi girma. Illa kawai ka sani, shi caji ta amfani da kwamfuta kan dauki lokaci kafin cajin ya cika, idan ka kwatanta da lokacin da asalin na’urar caji kan dauka kafin ya cike batirin waya. Wannan kuma ba wani abu ba ne, saboda a kwamfuta akwai abubuwa da dama da suke amfani da makamashinta; ba wai kai-tsaye wutar ke isa batirin wayarka ba. Sabanin na na’urar caji da aka killace musamman don daukowa da loda makamashin lantarkin daga asalinsa zuwa cikin batirin wayarka.

Wannan shi ne dan tsokacin da zan iya yi a halin yanzu.  Da fata ka gamsu.  Allah Ya sa a dace, amin.

Salamun alaikum Baban Sadik, Allah Ya ja kwana mu ci gaba da kwankwadar karatu. Don Allah a taimake mu da lambar da akan tura don kulle taskar banki cikin gaggawa. Barayin waya sukan ciri kudi ta asusun mutum na banki, su sa kati a layin wayar da suka sata, sai mutum ya je cirar kudinsa, sai ya gane ashe sun kwashe.  Al-Ameen Zariya:  07035586603

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Al-Ameen.  Akwai lambobi da kowane banki ke bayarwa ga kwastomominsa. Duk sako idan banki ya aiko maka sanadiyyar cire kudi ko sanya kudi a taskarka ta banki, a kasa za ka ga sanarwa daga bankin cewa idan kana da matsala ka kira wata lamba ta musamman.  Idan kuma bacewa ko sace maka katin ATM  aka yi, ga lamba ka kira don toshe katin kafin a sace maka kudaden da ke ciki.

Hanya mafi sauki ita ce, ka yi iya kokarinka wajen kare dukkan bayanan taskarka na banki don kada wani ya sace su.  Wannan ita ce hanya mafi sauki.  Hausawa kan ce: “Rigakafi ya fi magani.”  Don haka, duk bankin da kake da taska da su, yana da kyau ka san lambar da ake iya tuntubarsu idan matsala ta auku. Wannan ita ce hanya mafi sauki.  Da fata ka gamsu.

 

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya