Tambayoyi da sakonnin masu karatu ta imel da tes (5)

Assalamu alaikum babban malamina Baban Sadik da fatar kana cikin koshin lafiya kuma Allah Ya sa an yi Sallah lafiya, amin. Shin da gaske ne kafa turakun sabis (GSM Mast) kusa da jama’a yana illa ga lafiyar dan Adam, musamman ma radiation?

Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Saminu Artillery.  Wannan tambaya taka mun sha amsa makamantanta ko irinta, a baya – musamman a shekarun 2013 da 2016.  Malam Ali Fancy ya yi irin wannan tambaya a 2013, sai Malam Nasiru Kainuwa Hadeja da ya yi tambaya kan tabbacin ko sinadaran da wayoyin salula ke fitarwa yayin amsa kira na haddasa cutar sankara (cancer), a shekarar 2016.  Wadannan tambayoyi duk na amsa su ta hanyar bincike mai zurfi kuma a takaice.  Ga amsa tambayar da na bayar kan tasirin turakun sabis na kamfanonin wayar salula nan:

Wadannan cibiyoyi masu taimaka wa kamfanonin sadarwa yada tsarin sadarwar kamfanin wayarsu sun kasu kashi biyu ne; akwai na farko, da ke janyo tsarin sadarwar, wadda ke yada maganadisun sadarwar rediyo, wato “Radio Wabes.” Wannan nau’i shi ne wanda aka ce yana taimakawa wajen yada cutar sankara (Cancer), saboda maganadisun lantarki na rediyo da yake bazawa a muhallin da yake, wato “Electromagnetic Radiation.” Ire-iren wadannan galibi ba a girke su a cikin unguwa ko gari ko maraya, sai dai a bayan gari, ko a saman tsaunuka, kusa da unguwa ko gari ko mahallin da ake so su samu wannan tsarin sadarwa na wayar salula. Wannan ya sa ba a ajiye shi a kusa da jama’a. Kuma aikin hukumar sadarwar kowace kasa ce ta rika lura da inda kamfanonin sadarwar wayar salula ke ajiye ire-iren wadannan cibiyoyi. Shi ya sa ma yana daga cikin ka’ida, dole sai da wani jami’in Hukumar Sadarwa ta Kasa (kamar National Communication Commission, a Najeriya misali) kafin a dirke cibiyar a ko’ina ne.

Na biyun kuma shi ne wanda aikinsa bai wuce yadawa ko baza wannan tsarin sadarwa, don hana shi cushewa a bangare daya. A wasu lokuta a unguwa ko gari, za ka ga wani bangare ya fi wani bangaren garin daidaituwar tsarin sadarwa. Idan haka ta kasance, alama ce da ke nuna cewa akwai matsalar cushewar tsarin sadarwa a wani bangaren garin ko unguwar. Irin wannan cibiyar sadarwar ita ce za ka gani a girke a unguwanni misali. Ita wannan, a cewar masana, ba ta haddasa wata matsala ga lafiyar mazauna wannan wuri.  Domin aikinta shi ne yadawa ko baza tsarin sadarwar, ba wai janyo shi ta amfani da sinadaran maganadisun lantarki ba.  Shi ya sa suke kiranta “Cell Signal Booster.”  Da fata ka gamsu.

Dangane da abin da ya shafi alakar da ke tsakanin sinadaran maganadisun lantarki da wayar salula ke fitarwa yayin amsa kira, ga amsar da na bayar nan kasa:

ADVERTISEMENT

Wannan zance an sha maimaita shi, haka ma jama’a sun sha mini tambaya kan wannan al’amari shekara kusan biyar da suka gabata, kuma amsar da nake ba su dai ita ce zan ba ka: cewa har yanzu babu wani ingantaccen bincike na kimiyya, kuma amintacce, wanda ke nuna yawan amfani da wayar salula na haddasa cutar sankara, wato “cancer” ke nan.  Wannan jita-jita ce da kuma dari-dari da wadansu ke yi sanadiyyar sinadaran maganadisun lantarkin sadarwa (Radio Frekuency Electromagnetic Radiation) da ke fita daga wayar a yayin da mai waya yake yin waya.  Galibin masu yada wannan jita-jita ko yawan damuwa da wannan lamari na kafa hujja ce da wannan sinadari, wanda suka ce bincike ya nuna cewa zai iya haddasa wannan cuta.  Damuwar ta karu sosai cikin shekarar 2011, sa’ar da Hukumar Bincike kan Cutar Sankara ta Duniya (International Agency for Research on Cancer) ta nuna cewa akwai alamun nan gaba wannan sinadari na iya haddasa wannan cuta.

Don samun karin tabbaci, na tuntubi shafin Hukumar Lura da Yaduwar Cutar Sankara a kasar Birtaniya, wato: “Cancer Research, UK”.  A cikin bayanan da ta sabunta a shafinta da ke: www.cancerresearchuk.org a ranar 20 ga watan Oktoba na shekarar 2016, ta nuna cewa wannan zance har yanzu babu kanshin gaskiya a cikinsa. Domin dukkan binciken da aka gabatar a baya masu nuna wata alaka da wannan cuta ba su cika sharuddan binciken kimiyya nagartacce da za a iya gina hukunci a kansu ba.  Hukumar ta ce hatta rahoton da hukumar binciken cutar sankara ta duniya ta fitar a shekarar 2011 bai da nagartar da za a iya dogaro da shi.  Wanda shi ya sa ma hukumar ita kanta ta ce ta sanya wayar salula ce cikin jerin na’urorin da take “lura da su” don ganin ko wannan sinadari na iya tasiri wajen haddasa wannan cuta. In kuwa haka ne, ashe babu cikakken tabbaci ke nan.

Ba wannan wayar salula kadai ba, hatta na’urar yada siginar Intanet, wato: “WiFi” da na’urar wutar lantarki na zamani, wato: “Digital Meter,” ana tuhumar suna iya zama sanadi.  Sai dai a shekarar 2012 an sake gudanar da wani bincike wanda ya tabbatar da cewa babu sila, ko alaka ta sisin kwabo tsakanin sinadarin da wadannan na’urori ke fitarwa da wannan cuta.  Wannan har wa yau shi ne bayanin da Cibiyar Lura da Cutar Sankara ta kasar Amurka, wato: “National Cancer Institute” ta fitar a shafinta.  Babban dalili shi ne, wannan sinadari da wayoyin salula da sauran na’urorin sadarwa ke fitarwa ba ya furzar da sinadarin ayon (ion), ba wannan kadai ba, babu sinadarin ayon ma tare da shi. Amma sinadarin maganadisun lantarkin sadarwa mai fitar da sinadarin ayon (ion) ne ke haddasa cutar sankara.  Don haka, tunda wannan sinadari ba ya dauke da ayon a cikinsa, ke nan ba shi ba ne ke haddasa wannan cuta.

Hukumar Lura da Cutar Sankara ta kasar Birtaniya ta ci gaba da cewa, ya zuwa yanzu dai babu wani abin dogaro da ke tabbatar da wannan zargi, sai ma akasinsa. Domin, a cewarta, in da gaske ce wannan sinadari na sanadin kamuwa da cutar sankara, akalla an kwashe shekara kusan 30 ana amfani da wannan na’urar sadarwa ta wayar salula a kasar Ingila, misali, amma tsawon wannan lokaci, yawan masu cutar sankara bai karu ba.  Da a ce wannan na’ura na haddasa wannan cuta, ya kamata a ce a duk shekara ana samun karuwar masu kamuwa da cutar fiye da kima, musamman ta la’akari da yawan masu mu’amala da wayar salula a kasar baki daya.  Amma hakan bai kasance ba.  Ba a kasar ba kadai, a duk duniya har yanzu ba a samu wani mutum daya da ya taba kamuwa da cutar sankara sanadiyyar yawan amfani da wayar salula ba.

A karshe dai, abin da hukumar ta karkare bayani dashi dai shi ne, idan ma wannan sinadari na haddasa wannan cuta, to, ta yiwu sai bayan lokaci mai tsawon gaske, wanda babu wani bincike na kimiyyar zamanin yau da zai iya hasashen tsawon lokacin da za a iya kamuwa da cutar sanadiyyar amfani da wannan na’ura.  Da fatan ka gamsu.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya