Da Dumi Dumi

Tambayoyi da sakonnin masu karatu ta imel da tes (6)

Tambayoyi da sakonnin

Assalamu alaikum Baban Sadik.  Muna yi maka godiya da wannan namijin kokari da kake yi ga al’ummar kasar nan ta hanyar wayar da kanmu a kan kimiyya da kere-kere. Ni dai ban taba rike babbar waya ba, to wace shawara za ka ba ni? Da irin wacce zan fara idan na tashi saya?  Ashiru Manyan Gobe Mashi, Katsina: 09051512524

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Ashiru. Sayen wayar salula yana rataye ne da abubuwa da dama. Abu na farko shi ne yanayin hali na kudi. Nawa ka yi niyyar kashewa wajen sayen wayar, yana da alaka ne da irin wayar da za ka iya saya. Sannan yanayinka. Akwai wadanda masu kudi ne, amma ba sa son rike babbar waya. Ko dai saboda tsoron munana zato gare su daga jama’a, musamman barayi. Ko kuma tsoron ba za su iya yin tattalinta ba.

Ta yiwu abubuwa na saurin kubucewa daga hannayensu, ko suna aiki ne a wajen da ke dauke da hadari ga na’urori irin wayar salula. Wannan ke sa ka ga sun rike karamar waya, ba don ba za su iya sayen babbar waya ba.  Bayan haka, ya danganci wayewar mutum. Wadansu suna da kudin kuma suna son sayen wayar, amma ba su waye ba – watakila ba sa jin Turanci. Wannan zai sa su takaitu da karamar waya. Saboda sayen babbar waya wajensu hasarar kudi ne. Sannan a karshe, ya danganci me kake son yi da babbar waya. Idan bukatarka ba ta wuce aiwatar da kira da karbar kira ba, sayen babbar waya hasarar kudi ne.

Amma idan akwai abubuwa da yawa da kake son yi, wadanda sai babbar waya kadai ta mallake su ko take iya aiwatar da su cikin sauki da sauri, a nan za a iya cewa ka sayi babbar waya.

Don haka, ba zan iya ce maka ga irin wayar da za ka saya ba kai-tsaye. Kada ya zama waya ce mai tsada, alhali kai kuma ba ka da kudin da za ka iya mallakarta. Da a ce ka yi min bayanin yanayinka da iya kimar kudin da za ka iya sadaukarwa don sayen wayar, sai in ba ka shawarar irin wacce za ka saya.

ADVERTISEMENT

Don haka, ka dai samu waya mai iya hawa Intanet cikin sauki, mai dauke da babbar ma’adana, mai saurin budo shafuka kuma mai daukar caji na tsawon lokaci.  Ina yi maka fatar alheri da dacewa da wayar da ta dace da kai.  Na gode.

 

Assalamu alaikum Baban Sadik, gaisuwa mai yawa tare da fatar alheri.  Ina da waya kirar Tecno K7, in ina aiki da ita sai kawai ta cije ta tsaya, har sai batir ya dauke. Ko mece ce matsalar?  Daga Faisal Usman Binkola, Mayo Belwa LGA., Adamawa.

Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Faisal. Wannan alama ce da ke nuna cewa wayar tana da matsala babba, ba karama ba. Ko dai ta kamu da cuta (Birus) ne da ke addabarta, ko kuma tana fama da karancin ma’adana.

Ita wayar salula kamar dan Adam take; tana bukatar dan sarari don numfasawa da ma’adana isasshiya don adana abubuwan da ake zuba mata da kuma wata ma’adana ta wucin-gadi da ake kira: “RAM” – wato “Random Access Memory.” Wannan ma’adana ta wucin-gadi ce ke daukar dukkan bayanan manhajojin da kake budewa a wayarka, don samun damar tu’ammali da su cikin sauki.  Idan misali ka budo manhajar karba da aika sakonni, wato: “Message,” kana latsawa, wayar za ta dauko bayanan manhajar daga ma’adanar wayar, wato “Internal Memory” zuwa wannan ma’adana.  Da zarar ka gama amfani da manhajar, sai wayar ta mayar da su inda ta debo su.

Wannan ma’adana ta RAM tana zuwa ne mizani-mizani. Ba iri daya take a kowace waya ba. Manyan wayoyi masu tsada sun fi zuwa da RAM mai babban mizani, saboda samuwar tarin manhajoji da wayar ka iya zuwa da su, ko damar saukar da bayanai masu yawa, saboda girman babbar ma’adanarta.  Idan aka yi rashin sa’a mizanin RAM din wayarka karami ne, kuma ka tara manhajoji masu yawa a kan wayar, sannan kana budo manhaja sama da daya ko biyu a lokaci daya don amfani da su ba tare da ka rufe ta farko ba, wayar za ta shake ta kasa numfasawa, saboda karancin ma’adanar RAM din. Wannan ma daya ne daga cikin dalilan da ke sa waya ta zama haka.

Bayan nan, idan wayar tsohuwar waya ce mai dauke da tsofaffin manhajoji kuma ba a sabunta mata bayanan babbar manhajarta, wato “Update,” to, haka na iya faruwa da ita.  Don haka, hanya mafi sauki shi ne ka kai wajen masu gyara nagartattu don su duba maka ita. Domin bai kamata waya ta rika dogon suma irin wannan ba. Wannan shi ake kira: “Hanging.”

Wannan shi ne dan abin da zan iya cewa, tunda ba ganin wayar na yi ba kuma ba cikakken bayani ka yi kan nau’inta da yanayin sabunta ko tsufarta ba.  Allah Ya sa a dace, amin.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya