✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tambayoyin Duniyar Ma’aurata (2)

Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa a  wannan fili, da fatar Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga…

Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa a  wannan fili, da fatar Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga amsoshin wasu daga cikin tambayoyin da masu karatu suka aiko.

Na ji kin ce zuwa zance da ba da kudin hira da sauransu al’adu ne da suka ci karo da shari’a. Ni kuma na san malamai da alarammomi da suke zuwa wajen hira kuma su ba da kudin zance su rika yawan yin waya da ’yan matan nasu kamar kowa. In har yin hakan yana cin karo da shari’a ba ni zaton za su rika aikatawa.

Amsa:

Don malamai da alarammomi na aikata abu ba shi ke nuna cewa abin nan daidai ne ba, in kuma ba su aikata wani aiki ba shi ke nuna cewa abin nan ba daidai ba ne. Umarnin Allah da koyarwar Sunnar Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) su ake dubawa wajen tabbatar da halacci ko haramcin kowane aiki. Kwararan dalillai duk a Kur’ani da Sunnah sun nuna irin al’adun neman aure a kasar Hausa sun ci karo da shari’a nesa ba kusa ba musamman a wannan zamani.

Don Allah Malama Nabila ki yi wa ma’aurata bayani game da mutuwa irin shirin da ya kamata su yi mata domin tabbas daya zai mutu ya bar daya.

Amsa:

Lallai ka yi tambaya mai matukar muhimmanci. Wannan shiri ne da ya kamata dukkan mai rai ya yi masa tanadi na musamman.

 

  1. Shiri na farko da ya kamata ma’aurata su yi game da mutuwa shi ne ta yarda da sakankancewa cikin rai da zuciya cewa tana iya fado musu koyaushe ba zato ba tsammani, wannan zai sa su kara kaimi wajen kiyaye dokokin Ubangiji da kuma aikata ayyukan alheri.
  2. Shiri na biyu shi ne ma’aurata su sani kyakykyawan karshe shi ne komai, kuma ba wanda ya san yaushe ne karshen nasa zai zo? Don haka mafi wayon cikin mutane shi ne wanda ya dage da aikata kyakkyawa da guje wa mummuna da sanin cewa karshensa na iya zuwa a kowane lokaci. A takaice dai kyautata dabi’a, halaye da ayyuka ne babban shiri na biyu da ya kamata ma’aurata su yi game da mutuwa.
  3. Shiri na uku da ya kamata ma’aurata su yi game da mutuwa shi ne kyautata zamantakewa a tsakaninsu da juna. A dage sosai wajen faranta wa juna rai, a dage sosai wajen guje wa bata wa juna rai. A dage sosai a yaki Shaidan ta hanyar guje wa yawan gardandami da fadace- fadace da yawan jin haushin juna. Wannan shi zai sa in mutuwa ta raba wanda aka bari din ya tsananta kewa ga yawan addu’a ga mamacin. Akwai matar da ta bayyana cewa da mijinta ya rasu sai ta ji kamar kamar an cire mata kaya ce saboda ya yi zamantakewa da ita bisa kwara da danne hakki da tsananin takurawa.
  4. Shiri na hudu shi ne wasiyya rubutacciya da kuma ta baki. Ya kamata ma’aurata su rubuta wasiyyar abubuwan da suke yi sannan a gabatar bayan rasuwar daya daga cikinsu, wasiyya ana son ta kunshi bayanin wanka da Sallar Gawa, bayanin bashi duk wanda ke bin ka da wanda kake bi. Bayanin wata kyauta da kake so a ba wani ko wata wacce ba ta wuce ka’idar shari’a ba. Bayanin yara kanana, kula da su da aurensu da sauran duk wani bayani yadda mutum yake son a yi kaza ko kada a yi kaza bayan mutuwarsa. Ita wasiyya ana son kullum a rika sabunta ta saboda mutuwa na iya zuwa a kowane lokaci.
  5. Shiri na biyar shi ne ma’aurata su rika yawan rokon junansu yafiya kuma su rika yawan yafiya da afuwa ga junansu domin mutuwa na iya zuwa koyaushe, wanda ya mutu na iya tafiya Lahira da kullatar dan uwan aurensa a zuci. Ta hanyar yawan neman yafiya da yawan yin afuwa ne kadai za a guje wa haka.
  6. Shiri na shida shi ne yawan yi wa juna nasiha da tunatarwa wajen kiyaye dokokin Ubangiji da guje wa ayyukan sabo. Musamman ga ma’auratan da suke son auratayyarsu ta kasance har gidan Aljannar Ni’ima. Domin in ayyukanku suka sha bamban to wajen zamanku a Lahira ma zai sha bamban. Don haka in har kana son matarka so na gaskiya ka tsare mutunci kuma ka tabbatar ba ta bin bokaye da ’yan tsibbu, haka ke ma in har kina son mijinki ki yi hakuri da dan kadan da ya samo, ki dage da yi masa addu’ar samun kudin halal da tsari daga na haram, zina da sauran abubuwan rudin zamani. Wannan shi ne kadai hanyar tsirarku gaba daya a duniya da Lahira.

Da fatar Allah Ya sa mu dace da kyakkyawan karshe, amin. Sai mako na gaba insha Allah, da fatar Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.