✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tambayoyin Duniyar Ma’aurata (6)

Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili da fatar Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga…

Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili da fatar Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban amsa a kan hanyoyin rage fadace-fadace a tsakanin ma’aurata daga inda muka tsaya makon jiya:

 

9. Hanya ta tara ita ce koyi da mafi kyan misali, wato Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam). In ya yi fushi da daya daga cikin iyalansa, to yakan kaurace mata ce da magana sai ta yi nadama ta tuba kuma ta nemi afuwarsa. Don haka ba  mazantaka ba ne maigida ya yi ta mita an yi kaza ba a yi kaza ba, an bata kaza ba a gyara kaza ba, ba mazantaka ba ne maigida ya yi ta cacar baki  da sa-in-sa da uwargidarsa, kamewa daga yin haka shi ne mazantaka kuma hakan zai kara masa kwarjini wajen uwargidarsa. Sannan in uwargida ranta ya baci har kai ta ga daga murya ga maigida, to ba daidai ne maigida ya nuna ba ta isa ta raina shi da sauransu ba, ga abin koyi yadda ake daga Sarkin Muminai Sayyidina Umar (Radiyallahu anhu):

Wani mutum ya zo don ya kawo karar matarsa a kan yadda take daga murya tana mayar masa da magana. A lokacin da yake jirar fitowarsa daga gida sai ya jiyo shi ma Sarkin Muminai Umar (Radiyallahu anhu), matarsa na masa irin haka kuma ya yi shiru yana saurarenta bai ce mata komai ba. Sai mutumin nan ya juya zai koma, yana furta wa kansa ‘in haka abin yake ga Umar Sarkin Muminai wanda ya yi kaurin suna wajen nagarta da jarunta, to ina ga ni da ba kowan kowa ba?’

A lokacin Sayyidina Umar (Radiyallahu anhu), ya fito daga gidansa ya ga mutumin ya juya yana komawa sai ya kira shi ya ce “Me kake bukata daga gare ni ya kai bawan Allah?”

Sai ya ce: “Ya Sarkin Muminai, na zo in kawo karar matata ce a kan saurin kufula da nacin mita, sai na tarar kai ma matarka tana maka haka, sai na koma ina tunanin in abin haka yake ga Sarkin Muminai, to ina kuma ga ni?”

Sarkin Muminai Umar dan Khaddabi ya ce da shi: “Ya kai dan uwana! Ina hakuri da ita saboda hakkokinta a kaina. Tana dafa min abinci ta gasa min gurasa ta wanke min kayana ta shayar da ’ya’yana kuma duka wadannan ba dolenta ba ne! Sannan tana  samar mini natsuwar zuciya kuma tana katange ni daga ayyukan sabo. Don haka ya sa nake hakuri da ita.”

Sai mutumin ya ce “Ni ma haka take a gare ni Ya Sarkin Muminai!”

Sai Umar (Radiyallahu anhu), ya ce “Ka yi hakuri da ita ya dan uwa! Domin wannan rayuwar dai gajera ce.”

Wannan shi ne abin koyi da maza, lallai rage mazantaka ne maigida ya tsaya yana cece- ku-ce da uwargida ko matarsa.

Ga mata kuma abin koyi gare ku Uwar Mu’minai A’isha (Radiyallahu anha) wacce ta hanyar rantsuwarta ce kadai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ke gane cewa tana fushi da shi. Don haka in maigida ya ba ki haushi ya kule, ki daure ko a fuska kada ki nuna masa balle ki caccaba masa bakaken maganganu. Ki yi ta neman tsarin daga Shaidan da kuma rokon Allah Ya juya miki wannan bacin rai zuwa wani alheri na musamman. Allah Yana tare da ke koyaushe Ya san halin da kike ciki kuma Ya san jajircewar da kike yi na hadiye fushinki da girmamawa da karrama mijinki kuma zai saka miki da mafi kyan sakamako. Dubi dai dabi’ar Uwar Muminai na boye fushinta gaba daya daga mijinta abin kaunarta, irin wadannan kyawawan dabi’un zamantakewa da iya bi da miji suka sa ta zama mafi soyuwa daga cikin sauran matan Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam). Wani misalin kuma shi ne uwargida ki kwatanta cewa in mahaifinki ya bata miki rai yaya za ki yi? Za ki je ki zakalkale kina gaya masa magana son ranki ko za ki dukar da kai ki yi shiru cikin ladabi da girmamawa? To maigidanki ya fi mahaifinki muhimmanci don biyayyar miji ta fi ta uba girma a gaban Allah Madaukakin Sarki. Don haka sai a rika sara ana duban bakin gatari.

Sai mako na gaba insha Allah da fatar Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.