✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tambayyoyi daban-daban

A likitance akwai shekararren ciki kamar yadda akan gani a al’adance, har akan kira yaran da shekarau? Daga Binta I. Amsa: Eh, mun yarda akwai kwantaccen…

A likitance akwai shekararren ciki kamar yadda akan gani a al’adance, har akan kira yaran da shekarau?

Daga Binta I.

Amsa: Eh, mun yarda akwai kwantaccen ciki ko shekararren ciki. A da dai likitoci sun sha nuna shakku idan aka ce musu ga wani ciki ya haura wata tara, saboda a likitance kamata ya yi idan ciki ya kai wata tara to naquda za ta zo, idan kuma ba ta zo ba matar za ta zo a cire mata shi ta hanyar magunguna ko tiyata. To idan duka biyun ba su faru ba tabbas matar za ta yi ta zama da abinta, wataqila har sai abin da ke ciki ya mutu, wanda shi ma nan-da-nan jiki zai yi waje da shi.

 

Ko za a taimaka mini da yadda zan yi al’adata ta daidaitu. Na ga lambarku a jarida na ce bari in tambaya.

Daga H.K.L

Amsa: Eh, akwai maganin da likitan ko likitar mata za ta iya rubuta miki wanda zai daidaita miki al’ada. Sai dai ba za a iya ba ki ba a wannan kafa dole sai a asibiti. Ita wannan kafa ta shawarwari ce da ilimantarwa.

Magungunan da za a iya fadarsu ta wannan kafa magunguna ne wadanda ko a shago za ki iya saye wadanda muke kira ober-the-counter irinsu Panadol. Shi kuma wancan na daidaita al’ada dole sai likita ya ganki

 

Ni tun ina dan shekara bakwai wani qurji ya fito mini a baki, har zuwa yanzu na girma na yi aure amma bai bace ba. Ba ya ciwo amma wani lokaci yana yi mini qaiqayi. Shin wannan wata matsala ce?

Daga Babangida Sani, Abuja

Amsa: Eh, kuma a’a. Abin da ya sa aka ce haka shi ne cewa tunda abin (wanda ake ganin kamar tsiro ne) tun kana qarami ne ya fito maka, wataqila fiye da shekara 20, zai yi wahala a ce yana da illa ga lafiya. Da yana da illa ta lafiya da ba ka kai yanzu ba. An kuma ce eh, matsala ce saboda abin wataqila a yanzu yana damun rayuwarka ta yau da kullum, misali yadda sifar bakinka take. Wato wannan idan haka ne, za ka iya zuwa likitan baki (madillofacial) ya duba ya gani ko wataqila ya yi tiyata ya cire maka shi gaba daya.

 

Mai dakina ta haifi ’yan biyu kimanin wata hudu ke nan, shin yaushe ya kamata a fara ba su wani abinci sabanin ruwan nono, kuma wane abinci ya dace a fara ba su?

Daga Umar. M.M

Amsa: Kai masha Allah, Allah Ya raya. Ka zama takwara. Daga wata biyar ko shida za a iya fara gwada musu abinci mai taushi irin su Saralak da firiso ko kamu da aka sa wa madarar jarirai, gami da ’yan kayan itatuwa masu sauqin sha ko ci kamar ayaba da ruwan lemon fata. Amma ’yan biyu a wasu lokuta ruwan nono ba ya isarsu.

Idan aka samu irin wannan dole sai an qara musu da madarar gwangwani ta jarirai bayan ruwan nono. Amma idan akwai ruwan nono sosai suna sha suna qoshi, ba sai an qara ba a yanzu.