✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tambuwal ya nemi taimakon Buhari kan ‘yan bindiga

Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya bukaci gwamnatin tarayya ta kai masa dauki a kan ‘yan bindiga da ke addabar  jihar. “An rasa rayukka…

Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya bukaci gwamnatin tarayya ta kai masa dauki a kan ‘yan bindiga da ke addabar  jihar.
“An rasa rayukka da yawa da lalata muhallan mutane da dama. Dubban jama’a sun nakasa a jiki da tattalin arziki,” inji shi a jawabinsa na barka da salla.
Sai dai kuma, ya yaba da matakan da gwamnatin tarayya take dauka na kare lafiyar ‘yan Najeriya daga cutar coronavirus.
Kazalika ya nuna farin ciki bisa goyon bayan da jama’ar Sakkwato suka bayar a wannan lokacin na cutar coronavirus.
Tambuwal ya kuma yi godiya  ga hukumomi da kamfanoni da suka taimaka wa jihar a yakin da take yi da annobar coronavirus.
A karshe ya jaddada bukatar daukar mataki ga masu tayar da kayar baya, da suka addabi wasu kananan hukumomin jihar ta Sakkwato.