✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tambuwal ya sa zare da Wamakko a Sakkwato

Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya sa zare da tsohon Gwamnan Jihar, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko inda ya yi barazanar fallasa magabacinsa matukar…

Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya sa zare da tsohon Gwamnan Jihar, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko inda ya yi barazanar fallasa magabacinsa matukar ya ci gaba da matse shi a bango.

Gwamna Tambuwal ya yi wadannan kalamai ne a ranar Asabar da ta gabata a gaban dimbin magoya bayansa da suka tarbo shi don kara nuna masa suna tare da shi bayan faduwa a zaben fitar da gwani na Shugaban Kasa da jam’iyyarsu ta PDP ta yi.

“Kowannenmu ya san abin da aka yi Sakkwato mun bar kaza a cikin gashinta ne, saboda muna da tarbiyya ta magabata a lokacin da na zama Gwamnan Jihar Sakkwato magabatan jiha wadanda Allah Ya ba shugabanci ba masu ganin su ne shugabanni ba, sun yi min magana cewa Aminu duk abin da ka gani Sakkwato ka ja layi, haka aka yi kuwa na yi shirina ina kira ga wadancan jama’a (su Wamakko) su bar ni shiru kada su bari in bude bakina, don ina buda baki zasu bar gari ko EFCC ba za ta iya karbarsu ba.” inji Tambuwal.

Gwamnan ya ci gaba da cewar Allah Shi ke bayar da mulki, gare Shi suke nema ba su dogara ga kowa ba, saboda haka ’yan siyasa su bari a zauna lafiya a yi siyasa mai tsabta, duk wanda Allah Ya bai wa mulki shike nan, kuma yana amfani da zukata da niyyoyin mutane ne. Allah Ya san bai da wata niyya ta yaudara ko cin zarafin wani an gani bai taba kama wani, a ci mutuncinsa ba.

“Ban taba nuni ba har taro an yi na jihohi har da Jamhuriyar Nijar an kawo mutane muka bari aka yi taro aka tashi lafiya, muna jawo hankalinmu cewa Sakkwato tamu ce, mu duka ko kwai aka kashe mu ne muka yi hasara, in an ci zalin wani aka yi masa fashi mu shugabanni muna da hakki kan haka muka ce kada a biye wa ’yan ta’adda, don mu ba ’yan ta’adda ba ne ba mu goyon bayan ta’addanci,” inji shi.

“Sakkwato mu ci gaba da zaman lafiya kamar yadda muka shimfida wannan shekara uku da rabi tare da shugabanninmu kowa ya san kafin shigowar wannan gwamnati tamu akwai yara kangararru masu yin abin da suka ga dama, mata ba su iya fita wani lokaci ma ana bai wa maza tsoro da halinsu na ta’addanci,” inji Gwamna Tambuwal.

Ya yi kashedi ga iyayen kangararrun yaran “Ba iyayen da suka haife su ba, iyayen da suka lalata su, su sani Allah Yana ganinsu, kuma zai isar wa iyayen yaran da suka haife su da duk abin da suka yi na ba su tarbiyya ba daidai ba ce, ina kira ga iyayen su bari mu ci gaba da zaman lafiya. A madadin jam’ar Sakkwato ina ba da tabbacin za mu goyi bayan Atiku da yardar Allah zai karbi mulkin kasar nan, ganin yadda abubuwa suka lalace,” inji shi.

Awoyi kadan bayan kammala gangamin da wadansu ke kallon ya yi nasara ne a kan bacin ran da APC suke ciki kan sakamakon zaben fitar da gwani da jam’iyar ta yi kwanakin baya, na dora musu wanda ake ganin baya da magoya baya a jihar, jagororin jam’iyyar suka yi taron sirri don dinke barakar da aka samu da kau da jita-jitar da ake yadawa a gari cewa Faruku Malami Yabo zai koma PDP.

Bayan kammala zaman sirrin ne mai magana da yawun Sanata Wamakko Bashir Rabe Mani ya fitar da bayanin zaman ya yi nasara har wanda ya zo na biyu a zaben fitar da gwanin, Honarabul Faruku Malami Yabo ya karbi ya zama Mataimakin Gwamna ga Ahmad Aliyu da ya zo na daya.

Ya ce matakin karbar Mataimakin Gwamna da Faruku ya yi an cimma shi ne a gidan jagoran APC na Jihar Sakkwato, Sanata Wamakko a zaman sirrin da aka yi da Sanatan da dan takarar Gwamnan da Mataimakin Gwamnan Jihar Kano da Katukan Sakkwato da ’yan Majalisar Wakilai uku.

Wannan mataki kan iya canja alkaluman siyasar Jihar Sakkwato ganin magoya bayan Faruku na da yawa da rawar da suke iya takawa na samun nasarar Jam’iyyar APC.