Da Dumi Dumi

Tana bukatar a tallafa wa mata manoma a Jihar Kano

Wata fitacciyar manomiya da ke Jihar Kano, Hajiya Tabawa dahiru Garko, ta bukaci Gwamnatin Tarayya da kuma gwamnatocin jihohi da su kara bullo da hanyoyi na taimaka wa mata manoma, ta yadda su ma za su kara bunkasa sana’arsu ta noma da kiwo a kasar nan.Ta yi wannan tsokaci ne a wata tattaunawa da suka yi da wakilinmu, inda ta nuna cewa mata su ma suna noma mai yawan gaske, sai dai ba a cika ba su kulawa ba kamar manoma maza; duk da cewa mata su ne a sahun gaba wajen ganin tattalin arzikin kasa yana bunkasa ta kowane fanni.
Sannan ta bayyana cewa yana da kyau Gwamnatin Tarayya ta bullo da wani tsari na tallafa wa mata manoma, wanda zai kara masu karfin ci gaba da ayyukansu na noma da kiwo ba tare da samun matsala ba. Haka kuma ta yi kira ga gwamnatocin jihohin kasar nan da su ma su bullo da wani shiri, wanda zai taimaka wa mata manoma, ta yadda za a bunkasa samar da abinci a wannan kasa tamu.
Manomiyar ta kuma sanar da cewa matan Najeriya suna noma da kiwo sosai, amma ba su cika samun tallafi daga gwamnati ba, duk da irin yawan da suke da shi a karkashin kungiyoyi daban-daban tun da dadewa, inda ta yi fatan cewa Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohin kasar nan za su duba wannan bukata ta mata manoma, domin taimaka masu.
Dangane da yadda harkar noman mata yake a Jihar Kano kuwa, malamar ta shaida wa Aminiya cewa mata a jihar suna noma da kiwon dabbobi da kuma kiwon kifi, sannan ta nuna cewa akwai bukatar gwamnati ta kara himma wajen taimakawa masu, domin su ma su kara inganta harkokinsu na noma, musamman ganin yadda Gwamnatin Dokta Abdullahi Umar Ganduje take bullo da tsare-tsare na bunkasa noma a jihar ta Kano.
Haka kuma ta bayyana cewa tana noma duk wani nau’i na kayan amfanim gona a gonakinta, sannan tana kiwon dabbobi da kuma kiwon kifi; wanda a cewarta, yanzu haka tana da kifi fiye da dubu shida kuma nan gaba kadan za ta kara yawansu domin bunkasa kiwonsa.
Daga karshe ta yi amfani da wannan dama wajen yin godiya ga shugaban cibiyar horar da dabarun kiwon kifi ta Jihar Kano, watau Farfesa Armaya’u Hamisu Bichi saboda nasarorin da cibiyar ke samu wajen horar da dabarun kiwon kifi ga mata.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya