✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tankar mai cike da mai ta yi hadari a Legas

Wata tankar mai cike da man jirgin sama da ya kai lita 44,000 ta yi hadari, inda tankin man ya rabu da jikin motar a…

Wata tankar mai cike da man jirgin sama da ya kai lita 44,000 ta yi hadari, inda tankin man ya rabu da jikin motar a gadar Otedola da ke Legas a safiyar yau Laraba. Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Legas (LASEMA), ta isa yankin da abin ya faru.

A cewar jami’an Hukumar LASEMA,  sun ce tankar man mai lamba EKY 814 XX ta yi hadarin ne sanadiyyar gudu da tukin ganganci da direban motar yake yi, hakan yasa tankin man fita daga jikin motar.

Jami’in hulda da jama’a na Hukumar LASEMA Nosa Okunbor, ya tabbatar da aukuwar hadarin tankar man.