Da Dumi Dumi

Tankar mai ta kama da wuta a gadar Otedola Legas

Tankar man

Wata tankar mai dauke da man fetur da ya kai lita dubu 33 ta kama da wuta a safiyar yau Asabar.

Tankar mai lamba KJA-900XR  ta kama da wuta ne a yankin Ojodu zuwa Berger kusa da gadar Otedola da ke cikin jihar Legas.

A kwanakin dai an ta samun hadarin tankar mai a wannan yanki.

Hukumar bada agajin gaggawa LASEMA ta halarci wajen da gobarar ta kama da misalin karfe 5:15 na asubahin yau, kuma jami’an LASEMA sun taimaka wajen kashe wutar tankar. Kamar yadda Darakta Janar na LASEMA, Dakta Olufemi Oke-Osanyintolu, ya sanar.

ADVERTISEMENT
Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya