✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tarayyar Afirka za ta samar da rundunar sojan ko-ta-kwana

Shugabannin Afirka sun yi shirin samar da rundunar sojan ko ta-kwana, don shawo kan juyin mulki da ’yan tawaye da yake-yake a yankin, ta yadda…

Shugabannin Afirka sun yi shirin samar da rundunar sojan ko ta-kwana, don shawo kan juyin mulki da ’yan tawaye da yake-yake a yankin, ta yadda za a rage dogora da sojojin kasashen duniya, da tallafin kudi a harkar tsaro. Shugabannin sun yanke wannan amtsaya ce a wajen bikin cikar tarayyar AU shekara 50 da kafuwa.
Shugaban Tarayyar Afirka, Firayiministan Habasha Hailemariam Desalegn ya bayyana shirin samar da rundunar sojan ko-ta-kwana don kawo dauki ga rikice-rikicen da ka iya tasowa a yankin, inda ya yi nuni da cewa Shugaban Afirka ta Kudu ya bayar da wannan shawarar. Bya ga Afirka ta Kudu da ta yi asarar sopjojinta a rikicin Afirkta ta Tsakiya, inda ’yan tawaye suka yi juyin mulki, Habasha ma ta yi alkawari bayar da gudunmuwarta ga rundunar, kamar yadda jami’an gwamnatocin suka bayyana a wajen taron Tarayyar Afirka.
“kasashe da dama sun amince su bayar da gudunmuwa, ta yadda za a shawo kan rikice-rikice a fadin Afirka, wadanda suka hada da sauyin gwamnati ba tare da bin ka’idojin da kundin tsarin mulki ya shimfida ba. Wannan shi ne al’amarin da za a dauka da muhimmanci, a cewar Hailemariam.
Matsalar tsaro da Tarayyar Afirka (AU) ke fama da ita tsawon shekara biyu, ya hada da juyin mulkin Guinea –Bissau da yakin Mali da rikicin Najeriya, da suaran rikice-rikice da ake fama das u a gabashin nahiyar, wato a kasar Kongo da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.
Rundunar soja za ta kasance mai karfin mutum dubu biyar, wadda za ta fara aiki nan da shekara ta 2015, kuma jami’an kungiyar AU sun bayyana cewa da wuya ma a iya cimma wannan manufa.
Kwamishinar Zaman lafiya da tabbatar da tsaro ta AU, Ramatane Lamamra ta ce “rikicin kundin tsarin mulki” ta yadda za a dauki matakin difulomasiya wajen warware matsalar juyin mulki da kuma keta hakkin dan Adam, wadannan na daga cikin al’amuran da za a rika kawo wa dauki, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito.