✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi

234. An karbo daga Ibrahim dan Hamza ya ce: “Dan Abu Hazim ya ba ni labari daga Yazid daga Muhammad dan Ibrahim daga Isa dan…

234. An karbo daga Ibrahim dan Hamza ya ce: “Dan Abu Hazim ya ba ni labari daga Yazid daga Muhammad dan Ibrahim daga Isa dan Dalha daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), daga Annabi (SAW) ya ce: “Idan dayanku ya farka daga barcinsa, to ya yi alwala. Kuma ya sheka ya fyace sau uku. Saboda lallai Shaidan yana kwana bisa dodon hancinsa ne.”

Babi na Goma Sha Daya:

Ambaton aljannu da sakamakonsu da azabarsu. Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Ya jama’ar aljannu da mutane shin wadansu manzanni ba su zo muku ba daga gare ku suna ba ku labarin ayoyiNa a kanku, kuma suna yi muku gargadin haduwa da wannan yini naku…? (K:6:130).” Ma’anar Bakhsan wato nakasa. Mujahid ya ce: Sun sanya dangata tsakaninSa da Aljannu, wato kafiran Kuraihsawa sukan ce: Mala’iku ’ya’yan Allah ne mata, kuma iyayensu mata ’ya’yan aljannu mata. Saboda haka Allah Ya ce: “Hakika aljanu sun sani cewa: Lallai su wadanda ake halartarwa ne….” (K:37:158). Wato za a halarto da su wajen hisabi, kamar yadda ake halarto da rundunar mala’iku wajen hisabi.

235. An karbo daga Kutaiba ya ce: Daga Malik daga Abdurrahman dan Abdullahi dan Abdurrahman dan Abu Sa’asa’ah, mutumin Madina daga Babansa cewa: “Lallai shi ya ba shi labari cewa: Lallai Abu Sa’idul Khudri (Allah Ya yarda da shi), ya ce masa: “Lallai ni ina ganinka kana son kiwon tumaki da zaman kauye. Idan ka kasance cikin tumakinka ko ya ce, a cikin kauyenka ka rika kiran Sallah kuma ka daukaka muryarka da kiran Sallah. Saboda lallai babu wani mutum ko aljani ko dai wani abu da zai ji wannan murya face sai ya yi maka shaida da shi Ranar Kiyama.” Abu Sa’dul Khudri ya ce: “Na ji shi daga Manzon Allah (SAW).”

Babi na Goma Sha Biyu:

Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Hakika Mu Muka juyo da wadansu jama’a daga aljannu zuwa gare ka…..har zuwa fadarSa cewa: “Wadannan su ke ciki bata mabayyani.” (K:46:29-32).

Babi na Goma Sha Uku:

Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Saboda haka Ya watsa cikinta daga dukkan dabba (halittu)…” (K:2:164).

236. An karbo daga Abdullahi dan Muhammad ya ce: “Hisham dan Yusuf ya ba mu labari ya ce, Ma’amar ya ba mu labari daga Zuhuri daga Salim daga Dan Umar (Allah Ya yarda da su), cewa: Lallai shi ya ji Annabi (SAW) yana huduba bisa mumbari yana cewa: “Ku kashe macizan nan (biyu), ku kashe maciji mai zane biyu a baya da kumurci saboda suna gusar da gani (ido), kuma suna zubar da cikin mace.” Abdullahi ya ce: “Ana nan haka wata rana ina kokarin kashe wata macijiya sai Abu Aliyatu ya kira ni cewa: Kada ka kashe ta!” Sai na ce: “Lallai Manzon Allah (SAW) hakika ya umarci a kashe wannan macijin.” Sai ya ce, daga baya ya hana game da kashe na cikin gidaje, su ne wadanda ake umarta da su fita, sai su fita wato (Al-awamir, aljannu cikin gidaje da suke tare da jama’a).”

Babi na Goma Sha Hudu:

Fiyayyen dukiyar mutum Musulmi tumaki wadanda zai rika bin tsakanin duwatsu masu ruwa. (Saboda idan Kiyama ta yi kusa haka zai fi zama alheri daga zaman gari).

237. An karbo daga Imsa’il dan Abu Uwais ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Abdurrahman dan Abdullahi dan Abdurrahman dan Abu Sa’asa’ah daga Babansa daga Abu Sa’idul Khudri (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce; “Ya yi kusa ya kasance fiyayyen dukiyar mutum Musulmi ta kasance tumaki, yana bin kwarin duwatsu da inda ruwa ke taruwa domin ya tsira da addininsa daga fitina.”

238. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Abu Zinad daga A’araj daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Kan kafirci yana ta wajen gabas, alfahari da takama yana ga masu yawan dawaki da taguwa, rashin kula da addini yana ga wadanda suka cika aiki daga mutanen kauye masu gashin taguwa. Amma natsuwa tana ga masu yawan tumaki.”