✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tarihin Masarautar Wukari da asalin Jukunawa

Aminiya ta yi nazari a kan tarihin Masarautar Wukari da kabilun da suke rayuwa cikinta, mun nazarci rubutun masana tarihi da al’adu daga bangare daban-daban,…

Aminiya ta yi nazari a kan tarihin Masarautar Wukari da kabilun da suke rayuwa cikinta, mun nazarci rubutun masana tarihi da al’adu daga bangare daban-daban, kama daga tushen masarautar ta Wukari, asalin kabilunta daga ina suka fito da wasu daga cikin garuruwan da suka zauna kafin tarewarsu a Wukari da kuma rabe-raben kabilunta.

Tushe

Bayan rushewar Daular Kwararrafa da ke da hedkwata a Api, sai Jukunawa waɗanda su ne ke shugabantar daular ta Kwararrafa suka matsa gaba zuwa wannan bigire, suka kafa garin da a yanzu ake kira Wukari. Wannan kalma ta Wukari, asalinta shi ne Ukari,  kuma kalma ce ta Jukunanci mai ma’anar ‘Ka fifita.’ Sarkin Jukun na 40, Aku Uka Katakpa, shi ne ya jagoranci wannan ƙaura a  1596 (Adamu, 2016; Oleyede, 1996). Duk wanda ke shugabantar wannan masarauta, shi ake kira Aku Uka, kalmomin da ke da ma’ana ta Sarkin da ya fi kowane Sarki a duniya; kamar yadda (Adamu, 2016) ya fitar.

Wannan gari shi ne ya zamo tubulin canjin tarihin Jukunawa, ya kuma zama sabuwar hedkwatar daular Jukunawa zalla, maimakon daular haɗa-ka ta Kwararrafa da Jukunawa suka shugabanta wacce ke ƙunshe da mabambantan kabilu.

Jama’a

Tunda farko, garin Wukari an kafa shi ne unguwa-unguwa, kuma kowace unguwa mazauna cikinta kusan zuriya guda ce. Daga cikin irin wadannan unguwanni akwai Go-Ndoku, da ke nufin Gidan Sarki ko Fadar Sarki. Sai wasu unguwannin da suka haɗa da Kinda Kubyo da Adikyu-Gashi da Ndo Abonta da Kwanse da Ndo-Nwugye da Tsupando da sauransu (Adamu, 2016).

Gari ne wanda ke kewaye da ganuwa da kuma ƙofofi bakwai duk da cewa a yanzu, ƙofar Arewa ce kaɗai ta saura da jama’a ke amfani da ita; wacce kuma a zamanin baya, mafita ce ta gawarwakin jinin sarauta. Haka kuma a tsakiyar garin akwai tsohuwar kasuwar da tunda aka kafa garin take.

Sahun farko na sauran kabilu mazauna wannan gari na Wukari akwai Gobirawa, waɗanda kasuwanci ya kai su garin kuma suke zaune kusa da fadar Sarki, wanda har ta kai ga shugabansu mai suna Maiwuya ya auri ’yar Sarkin Wukari na wancan lokacin abin da ya ba shi damar da aka yi masa sarautar Sarkin Kasuwar Wukari da ke da alhakin tattara haraji.

Haka  kuma a 1932, a zamanin Aku Amadu Agbumanu, wadansu jama’a daga Sakkwato sun ƙaura zuwa Wukari, bayan tuɓe Sarkin Musulmi Muhammadu Tambari da aka yi, wanda ya yi gudun hijira zuwa garin na Wukari, inda a can ya rasu kuma aka binne shi a can. A yanzu haka sauran zuriyarsa suna zaune a wannan gari na Wukari a wata unguwa da ake kira Unguwar Sakkwato wacce ke daura da Akata.

Bayan zamowar wannan gari na Wukari hedkwatar Masarautar Jukunawa, shi ne kuma hedkwatar Karamar Hukumar Wukari a Jihar Taraba. Yanzu haka wannan gari yana da ci gaban da har ta kai ga yana da jam’o’i uku da kuma sauran manya da ƙananan makarantu.

Daga farkon kafa wannan gari zuwa yau, sarakuna 27 ne suka shugabance shi. na farkonsu shi ne Angyu Katakpa (1596 – 1615), sai kuma na ƙarshe wanda har yanzu yake kai, Dokta Shekarau Angyu Masa-Ibi, Kubyo II (1976 zuwa yau).

Su wane ne Jukunawa

Jukun, kalma ce da ke nufin ‘Mutum’ a harshen Jukunanci (Okunna da Gausa, 2014), kuma, harshe ne da wadansu jama’a ke magana da shi. Duk wanda ya gaji wannan harshe ya zama Bajukune, jam’insu kuma, Jukunawa. Su mutane ne masu karɓar baƙi da son zaman lafiya da son jama’a da biyayya da fafutikar ƙwatar ’yanci, kuma a lokaci guda jarumai a fagen yaƙi (Taraba Online, 2014). Suna yaƙi da duk nau’o’in danniya da zalunci. Sun kafa Daular Kwararrafa tare da haɗin guiwar wasu ƙabilu da suka haɗa da Igala da Ibira da Nupe da sauransu. Kwararrafa daula ce da ta yi yaƙi da wasu daga cikin manyan daulolin ƙasar Hausa kamar Kano da Katsina da Zazzau da sauransu. Daular da ta ruguje daga baya ta samar da sabuwar Daular Jukun zalla da ke da hedkwata a garin Wukari, Jihar Taraba.

Asali

Jukunawa sun shigo garuruwan baƙaƙe (Bilad Sudan) daga Gabas. A wata tattanawa da aka yi da Mai martaba Sarkin Pindiga, Alhaji Muhammad Sayoji Ahmad a ranar 13/02/2017, ya ce, Jukunawa sun fito ne daga kasar Yemen, suka shigo ta ƙasar Sudan ta yau, inda suka yada zango a garin Kartum (Khartoum ta Sudan). Daga nan suka rankayo ta gefen Kogin Chadi, kama-kama har suka zo Dutsen Bima. Daga wannan dutse na Bima ne suka rabu gida biyu; kashi ɗaya daga ciki suka kama hanyarsu tiryan-tiryan har zuwa Dutsen Binga, inda suka kafa wani gari wanda a yau ake kira da Yalwa. Nan suka zauna a kan wannan dutse har zuwa lokacin da Sarkin Gombe Umaru Kwairanga ya ci su da yaƙi, abin da ya haifar da tarwatsewarsu zuwa wasu sassa na wannan yanki har zuwa kusa da Kogin Benuwai a wani yanki da ake kira Pi, wanda daga baya ya zama hedkwatar Daular Kwararrafa.

Dokta Dawuda (2011), da Mac-Leba (2009), sun ruwaito cewa Jukunawa daga Yemen suka zo. Dokta Dawuda (2011) ya ƙara da cewa Jukanawa asalinsu Yahudawa ne saboda zuwan Yahudawa Najeriya har garin Wukari, don gudanar da bincike kan baraguzan kayan yaƙi da suke da alaƙa da su. Sannan ya nanata cewa su Jukunawa suna da wani salon rubutun da ya ke kama da Hibiranci (Harshen Yahudu).

Amma (Okunna, Emman, Gausa da Solomon, 2014 da Ujorha, 2012), sun haɗu kan cewa asalin Jukunawa daga ƙasar Masar suke, inda a Ujorha (2012), aka nuna cewa akwai kamanceceniyar al’adu da addini da Jukanawan Kona da mutanen tsohuwar Masar, duk da cewa takardar ta ruwaito tsangayar tarihi ta Kwalejin Ilimi ta Tarayya (FCOE) da ke Jalingo ta danganta asalin nasu da Yemen.

Sai kuma ra’ayin kundin sani na Britannica (2010) da suka ambata cewa Kwararrafa wata daula ce mai ƙarfi daga Sudan. Wannan ra’ayi na Britannica (2010), ya samu ƙarin haske daga (Okunna, Emman, Gausa da Solomon, 2014) cewa sun taso ne daga Gabas ta Tsakiya zuwa Sudan ɗin.

Saboda haka idan muka tattara waɗannan bayanai sai mu ga cewa asalin Jukunawa daga Gabas ta Tsakiya suka zo suka zauna a Sudan tun cikin ƙarni na 4, sannan suka shigo ƙasar baƙaƙe inda suka fara yada zango a Kukawa, sannan suka koma Ngazargamu, sai kuma Dutsen Mandara  daga nan sai Mubi ta tsohuwar Jihar Gwangola wacce yanzu take Jihar Adamawa, sai garin Kilba, sai Kogin Hawal duk a Jihar Adamawa ta yau. Sai kuma suka zarce zuwa Shane daga nan sai Pindiga, waɗanda su kuma a yau suke cikin Jihar Gombe. Daga nan sai Gwana ita kuma a Jihar Bauchi, inda daga ƙarshe suka yada zangonsu na ƙarshe a garin Wukari wacce ta zama babban garinsu har zuwa yau ɗin nan. Shi garin Wukari yanzu yana cikin Jihar Taraba.

Rabe-Raben Jukunawa

Gamgum (2015), ya ce daga ƙarni na ashirin zuwa yau, Jukunawa sun rarrabu zuwa kashe-kashe kamar haka:

  1. Jukunawan Asali: Waɗannan su ne wadanda ba su da wani harshe in ban da Jukunanci; su ne duk wani mutum da iyayensa da kakaninsa Jukunawa ne sannan kuma ba ya da wani harshe sai Jukunanci.
  2. Jaukunawan Dole: Waɗannan su ne Jukunawan da suna da harshensu na asali da ba Jukunanci ba, amma wasu dalilai suka saka su zama Jukunawa. Dolen da ake nufi a nan tana iya zama ta fuskar yaƙi kamar bayi da ake kamawa lokacin yaƙi ko kuma ’yan-ci-rani da ke zuwa cikin Jukunawa su zauna har wani lokaci mai tsawo da ka iya sanyawa asalinsu ya ɓace, saboda haka sai su zamo ba su da wani harshen uwa sai Jukunanci.
  3. Ƙawayen Jukunawa: Waɗannan su ne mutanen da suke da wani gado ta fuskar harshe da al’adu da asali da daula, kuma suka ci gaba da riƙe waɗannan al’adu nasu, amma kuma akwai dangantaka ta ƙut-da-ƙut da ka iya zama ta zamantakewa, tattalin arziki, siyasa, addini, ko wani abu daban, da suka ƙulla don cimma wannan manufa tare. Iri waɗannan Jukunawa sun haɗa har da waɗanda suka yarda su ba da jiziya don kuɓuta daga hare-haren yaƙin abokan gaba na cikin ƙarni na 14. Misali, akwai waɗanda suka nemi tallafin Jukunawa don samun kariya daga hare-haren yaƙe-yaken Kano, Katsina da Zazzau a shekarun ƙarni na 5 na 6 da na 14.

A wata tattaunawar da aka yi da Alhaji Gambo Garba, Galadiman Pindiga a ranar 13/02/2017, ya ce, Jukunawan Asali sun karkasu zuwa:

  1. Jukun Wukari.
  2. Jukun Pindiga.
  3. Jukun Kona.
  4. Jukun Kuteb

Yaƙe-yaƙe

Jukunawa wadanda suka samo asali daga Kwararafa, mutane ne masu matuƙar jarumtaka wajen yaƙi, a binciken da aka gudanar, an ci karo da cewa, Jukunawa sun yi galaba a yaƙin da suka gwabza da manyan daulolin ƙasar Hausa da suka haɗa da Kano, Katsina da kuma Zazzau. (Northern Nigerian Publishing Company, 1970; Wikipedia, 2016).

Wannan magana muna iya ƙarfafa ta daga sunayen wasu unguwanni biyu da ke cikin biranen Kano da Zariya. A garin Kano akwai unguwa mai suna ‘Yakasai,’ wacce ruwayar kunne-ya-girmi-kaka ke cewa kalama ce da ke nufin ‘Za mu dawo’ ko ‘Muna dawowa,” da ta fito daga bakin Jukunawa lokacin da suka ci Kano da yaƙi. Haka kuma akwai unguwa mai suna Tudun Jukun a cikin birnin Zariya, wacce ita ma Jukunawa suka kafa ta bayan sun ci garin Zariya da yaƙi.

Sarki Ali Mai na Daular Borno, shi ne ya taka musu birki lokacin da suka kai wa Ngazargamu harin yaƙi kamar yadda Wikipedia (2016), ya naƙalto a kundin tarihin Katsina (Katsina Chronicle).

Yawan jama’a

Duk da ba wani cikakken ƙayadadden adadin yawan jama’ar Jukunawa, amma ana hasashen yawansu ya haura miliyan biyu da rabi (Shishi, 2014). Jukunawa suna zaune cikin garuruwa da dama a  jihohin Taraba da Benuwai da Nasarawa da Kano da Kaduna da Katsina da Filato da Adamawa da Gombe da sauran garuruwa a jihohin da yawansu ya kai  jihohi 22 a Najeriya da kuma wani yanki na Arewa maso Yammacin ƙasar Kamaru (North Western Cameroon).

Al’adu

Daga cikin manyan al’adun Jukunawa, akwai mai suna Ukenho, wacce ake gudanar da ita a ƙarshen shekara. Sannan akwai Ungu da sauransu.

An ciro wani sashi na wannan tarihi, daga shafin: http://nigeriamasterweb.com/blog/inded.php da Encyclopædia Britannica (2010). Jukun People. Encyclopaedia Britannica Ultimate Reference Suite.  Chicago