✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Taron Gwamnonin PDP sharholiya ne kawai – Ishak Hadeja

An bayyana taron gwamnonin Jam’iyyar PDP da akayi a makon jiya a Jihar Jigawa da cewa sharholiya ce kawai Gwamna Lamido ya shirya don neman…

An bayyana taron gwamnonin Jam’iyyar PDP da akayi a makon jiya a Jihar Jigawa da cewa sharholiya ce kawai Gwamna Lamido ya shirya don neman gindin zama a wurin Shugaba Jonathan bayan sun riga sun gano ba ya tare da su.
Wani jigo a Jam’iyyar APC Alhaji Is’hak Hadeja ne ya bayyana haka a tattaunawarsa da wakilinmu a Dutse, inda ya ce babu bambancin taron da irin sharholiyar da tsohon Gwamnan Jihar Alhaji Saminu Turaki ya shirya wa sarakuna inda aka yi wadaka da dukiyar talakawan jihar.
Alhaji Hadeja ya ce abin takaici makudan kudin da Gwamna Lamido ya narka wajen gyara masaukin gwamnoni da shimfida kafet din da suka taka don shiga gidan Gwamna sun isa a biya kudin jarrabawar daliban jihar ko sayen kujerun  zama da gwamnati ta kasa sanyawa a ajujuwan makarantunta.
Ya ce talakawan Jigawa suna cikin mawuyacin hali saboda talauci da yi masu kama-karya, inda ya ce, yanzu talakawan jihar sun gane Gwamna Lamido yana yi masu ban-kwana ne ta hanyar musguna musu saboda gwamnatinsa ta kusa karewa. Alhaji Is’hak ya ce da zarar Gwamna Lamido ya bar kujerar Gwamna za su gurfanar da shi a gaban kotun kare hakkin dan Adam domin nema wa jama’ar da ya zalunta a zamanin mulkinsa hakkinsu.
Ya ce maganar cewa Gwamna Lamido zai tsaya takarar Shugaban kasa a PDP mafarki ne domin ya san babu yadda za a yi Jonathan ya ba shi damar tsayawa takara ba domin Nijeriya ta fi karfin Gwamna Lamido.
Sai dai a martanin shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Jigawa Alhaji Salisu Mamuda Kuit ya ce Is’hak Hadeja ba mutum ne da za a tsaya ana ba shi amsa ba domin ba ya da alkibla. “Za mu hada shi da yara matasa daidai shi don su mayar masa da martani, amma bai ishe mu fada a fagen siyasa ba,” inji shi.