✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Taron kasa: Akwai yunkuri na wargaza Arewa – Gwamna Babangida

Gwamnan Jihar Neja kuma Shugaban Majalisar Gwamnonin Jihohin Arewa Dokta Mu’azu Babangida Aliyu, ya ce taron kasa da ake shirin yi wani yunkuri ne na…

Gwamna Mu’azu Babangida Aliyu Na Jihar NejaGwamnan Jihar Neja kuma Shugaban Majalisar Gwamnonin Jihohin Arewa Dokta Mu’azu Babangida Aliyu, ya ce taron kasa da ake shirin yi wani yunkuri ne na wargaza Arewa, inda ya ce yankin zai iya dogaro da kansa idan kasar nan ta wargaje sakamakon taron.
Gwamna Babangida Aliyu ya bayyana haka ne a lokacin kaddamar da Gidan Rediyon Liberty FM da kuma taron bita mai taken: “Makomar Kafofin Watsa Labarai na Rediyo da Talabijin a Arewacin Najeriya: Wani Abin Lura a Bayan karni” da aka gudanar a Kaduna.
Gwamnan ya yi zargin cewa akwai yunkuri da dama da wasu daidaikun mutane suke a Arewa domin tabbatar da yankin bai kasance a dunkule ba. “Mutane da dama sun tunkare. Dagan an Arewa suke. Suna cewa mu dakatar da gwagwarmayar da muke yi. Kuma wasu daga cikinsu sun samu dama a matsayinsu na shugabanni amma ba su inganta rayuwar al’ummar Arewa ba,” inji shi.
Ya ce wajibi ne ga daukacin jihohin da ke Arewa su kafa kwamitocin wakilan da za su halarci taron na kasa. “Ko wane irin sakamako taron zai haifar, Arewa za ta iyya tsayawa da kafafunta. Idan za a samu danyen mai a Jamhuriyar Nijar, to, akwai danyen mai jibge a kogin Kwara da Sakkwato da Kogi da daukacin sassan Arewa. Kuma Jihar Neja ta ninka wasu jihohi a Kudu maso Gabas fiye da sau uku, idan wani abu ya faru Arewa za ta iya ciyar da kanta hart a rika fita da abinci ta hanyar noma zamani.”
Ya ce “Idan Jamhuriya Nijar da ake bayyana ta da mafi talaucin kasa a duniya za ta farka wata rana ta gano cewa tana da man fetur, sassa da daman a al’ummarmu za su iya dogaro da kansu. Amma babban al’amari shi ne hadin kan Najeriya. Wannan ne ya sa muke tsananin bukatar tattaunawa. Duk wanda yake da wanin abu a zuciyarsa ya bayyana shi. Kuma daga lokacin da muka hade ba za a sake samun wata magana ta raba kasa ko wani yana son ’yanci, babu.”
Gwamnan ya kuma yi watsi da zaben shugabanni gatsau, inda ya ce, “Ba mu bukatar zaben shugabannin da ba su shirya ba, saboda mutane da dama suna son cin zabe ta amfani da kudi, yayin da fiye da kashi 40 cikin 100 na yaran Arewa ba su zuwa makaranta.”
Gwamna Babangida ya ce shi da takwarorinsa sun mayar da wukarsu kube ne kan rikicin da ya addabi Jam’iyyar PDP don girmamawa ga Shugaba Jonathan da kuma kujerarsa da kuma amfanin Najeriya. Shugaban kungiyar Kare Muradun Arewa (ACF) Alhaji Aliko Mohammed ya ce sun tsara yadda ’yan Arewa za su halarci taron kasa kuma za su mikka shi ga gwamnonin.
Ya ce, “Idan za gudanar da taron wane ne za su kasance wakilan wannan taro? Shin za mu kori ‘’yan majalisar dokoki ne? Mun ba da shawara ga gwamnonin cewa duk wanda zai wakilci wani yanki a cikin kwamitin, wajibi ne wannan mutum ko mutane su iya magana da harshen wadannan mutane. Kuma wajibi ne ya zamo mai sadaukar da kai ga bukatun jama’ar. Kuma za mu zauna da sarakuna domin tabbatar da cewa mutanen da za su wakilci sun cika wadancan ka’idoji.”
Shugaban kungiyar Kare Hakkin dan Adam ta CRC, Kwamared Shehu Sani ya bayyana shirin taron kasar a matsayin bata lokaci da dukiya.
dan rajin kare hakkin dan Adam din ya ce, shirin na tattaunawar wani shiri ne na Fadar Shugaban kasa domin kawar da hankalin ’yan Najeriya daga dimbin matsalolin da ta gaza magancewa a kasar nan.
Shehu Sani ya ce, dimokuradiyya ba wata kyauta ce daga sojoji ba, a’a ta samu ne sakamakon gwagwarmaya da sadaukar da kai, inda ya ce, “Dimokuradiyya a karkashin mulkin Jam’iyyar PDP ba haifar da komai ba, baya ga zalunci da yawan keta hakkin dan Adam da sauran munanan abubuwa sakamakon rashin ‘kwarewar’ gwamnati.
Ya ce, “A shekara ta 2015, idan muka kafa gwamnatin Jam’iyyar APC, za mu yi watsi da rahoton taron kasar saboda ba zai yi amfanin komai ga jin dadin ’yan Najeriya ba. Malaman jami’o’i da likitoci ba su bukatar tattaunawa don janye yajin aikinsu. Rahoton kwamitin za a mika shi ne ga Shugaban kasa wanda tuni ya fara kamfe din neman mulki na wani zango, kuma ’yan Majalisar Tarayya su ma suna son su sake komawa. Idan APC ta yi waje da PDP, dimokuradiyyya ta gaskiya za ta ginu a kasar nan.”  
Da yake jawabi a wurin taron tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Ahmed Mohammed Makarfi ya ce babu laifi idan kasar nan ta yanke shawarar zama ta tattauna, inda ya kara da cewa, “Wajibi ne bangaren Zartarwa da na Majalisa su sallama ikonsu ga bangaren shari’a idan ana son taron ya yi tasiri.”
Sanata Makarfi ya ce, kamata ya yi a shirya taron tattaunawar ga ’yan Boko ’yan siyasa, maimakon kabilun kasa da kungiyoyin addini da masarautu wadanda dama kansu a hade suke, inda ya ce talakan Najeriya bai da matsala kan hadin kai.
“Matsalar ita ce ’yan Boko ’yan siyasa. Matsalar tana tare da mutanen da suke son hawa mukaman siyasa. Talaka yana bukatar kyakkyawan shugabanci da zaman lafiya da kwanciyar hankali. Amma wannan taro kamar yadda alamu suka nuna ba zai haifar da wani sakamakon kirki ba,” inji shi.
Sauran wadanda suka yi magana sun hada da wakilin Gwamnan Jihar Kaduna Malam Ahmed Maiyaki da kuma shugaban gidan talabijin na DITb/Alheri Redio, Dokta Hakeem Baba Ahmed da kuma shugaban gidan Rediyon Liberty Alhaji Tijjani Ramalan wanda ya ce suna kokarin kafa gidan talabijin na Liberty da jaridar Liberty a shekarar 2014.