✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Taron kasa: Jonathan ya raina majalisun kasa – Sadau Garba

Wani lauya mai zaman kansa kuma Daraktan Cibiyar Kare Hakkin dan Adam da ke Kaduna Barista Sadau Garba ya ce taron kasa da ake gudanarwa…

Wani lauya mai zaman kansa kuma Daraktan Cibiyar Kare Hakkin dan Adam da ke Kaduna Barista Sadau Garba ya ce taron kasa da ake gudanarwa a halin ba ya da wuri a dokokin Najeriya kuma ya saba wa sashi na 4 na tsarin mulkin 1999 da ya ba Majalisar Dokoki ta kasa ikon yin dokoki don zaman lafiyar kasa.
Barista Sadau Garba ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da Aminiya, inda ya ce abin da taron ke kokarin yi aiki na Majalisar Dattijai da ta Wakilai, amma sai ga shi an fara kashe kudin da zai kai Naira biliyan bakwai ga wakilan da wasu barci kadai suke yi a wurin taron.
Ya ce idan Shugaban kasa yana neman shawara ce akwai majalisar ministoci da ta dokoki da kuma mashawartansa kamar yadda sashi ta 5 ya nuna, in kuma yana son bayanin doka ne sai ya tuntubi Ministan Shari’a.
Barista Sadau Garba ya ce taron kasar taro ne na shan shayi da ya zamo raini ga majalisar dokoki ta kasa da dokar kasa, musamman da aka dauko mutanen da ake zargi da laifi aka sa a cikin taron.  
Ya ce tunda babu tanadin taron a kasafin kudin bana lokaci ya yi da majalisar dokokin za ta farka daga barci ta dauki mataki a kai, inda ya shawarci shugaban taron Mai shari’a Idris Kutigi da sauran masana shari’a da ke cikin taron su nuna wa Shugaban kasa cewa bai dace a ba su Naira miliyan hudu kowane wata ba, kamata ya yi mahalarta taron su yi muhawarar kyauta.
Sai ya yaba wa ’yan kalilan din wakilan da suka ce ba za su karbi ko kwabo daga kudin ba, inda ya yi kiran a karkata wannan kudi wajen gina makarantu da asibitoci da samar da wutar lantarki da sauransu musamman a wannan lokaci da malaman makarantun kimiyya da sana’a suke yajin aiki.