✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Taron kasa ya dauki harami

Babban Taron kasa da Shugaba Goodluck Jonathan ya kira ya dauki harami a ranar Litinin da ta gabata, bayan da Shugaban kasar ya bude shi…

Babban Taron kasa da Shugaba Goodluck Jonathan ya kira ya dauki harami a ranar Litinin da ta gabata, bayan da Shugaban kasar ya bude shi a babban dakin taro na Cibiyar Nazarin Shari’a ta kasa a Abuja.
An fara taron ne a daidai lokacin da jama’a daban-daban ke ci gaba da kokawa kan rashin cacantar taron da kuma kukan danniya daga bangarori da dama.
Wakilan taron sun yi ganawarsu ta farko a ranar Talata kafin a dage zaman taron zuwa ranar Litinin mai zuwa, kuma za a rika zaman taron ne daga ranakun Litinin zuwa Alhamis na kowane mako.
Shugaban taron Mai shari’a Idris Legbo Kutigi wanda ya yi jawabin bude fara taron inda ya sanar da dage zaman don ba wakilai damar kintsawa a soma muhawara gadan-gadan.
Taron dai zai tattauna dukkan batutuwa da suka addabi ’yan kasa, kamar rabon arzikin kasa, da matsalar rashin tsaro da rashin aikin yi da tsarin shugabanci na Shugaban kasa mai cikakken iko ko kuma tsarin Firayi Minista da sauransu.
Sai dai kuma gwamnati da ta kira taron ta haramta wa mahalarta taron su 492 su tabo batun raba Najeriya a tsawon zamansu na wata uku.
A ranar Litinin ne Shugaba Goodluck Jonathan ya bude taron, yana mai tabbatar da cancantar yinsa don lalubo kyakkyawar makoma ga kasar nan.
Dokta Goodluck wanda ya ce ba ya da wata boyayyiyar bukata da yake son cimmawa a wannan taro, ya bukaci wakilan taron sun tattauna batutuwan da za su ciyar da kasar nan gaba.
Babbar jam’iyyar adawa wato APC ta kaurace wa taron, inda ta ce bata lokaci ne kawai da barnata dukiyar al’umma.
A watan Oktoban bara ne Shugaba Jonathan ya ce za a yi taron kuma tun a lokacin ne batun ke ta janyo ka-ce-na-na-ce.
Wata kungiyar Musulmi mai suna Muslim Solidarity Forum ta soki yadda aka tsara wakilan taron inda ta ce daga cikin wakilan 492, Musulmi na da wakilai 190 ne kawai, lamarin da ta bayyana da zabagen rashin adalci da wata muguwar manufa ga makiya addinin inda ta yi kira ga Majalisar koli kan Harkokin Addinin Musulunci da sauran daidaikun Musulmi da kungiyoyinsu su kaurace wa taron.
Shugaban kungiyar Dokta Isah Maishanu ya fadi wa taron manema labarai a Sakkwato a ranar Talata cewa tsarin wakilan taron ya saba wa sashi na 14 (3) da sashi na 15 (2) na tsarin mulkin 1999, kuma ya saba wa jagoran taron da ita kanta gwamnatin ta fitar na zaben wakilan taron inda aka tauye Musulmi.
Wakilanmu a zauren taron sun ce addu’ar da Kutigi ya yi cikin Larabci a wajen bude taron ya tayar da kura bayan da Fasto Tunde Bakare ya ce shugaban ya yi magana da wani harshe da bai fahimta ba. Ya ce in da shi zai tashi ya ce ‘A yabi Ubangiji wani na iya cewa yana kokarin mayar da wurin coci.’
Sannan lokacin da Mataimakin Sakataren Taron harkokin gudanarwa ya ce za a kebe daki daya a matsayin masallaci ga wakilai Musulmi, sai wasu wakilai Kirista suka ce su ma suna bukatar wurin ibada, musamman a yanzu da suke azumi, domin su rika bauta da shan ruwa.
Har wa yau a yayin tattauna yadda za a yi zama a zauren taron ma sai da aka yi takaddama, bayan da sakataren taron ya ce za a sanya suna a kujerun zaman amma wakilan Kudu maso Kudu suka ce atafau sai dai duk wanda ya riga zuwa ya zauna a kujerar gaba. Sannan bukatar Sajen Awuse ta wakilan su zauna a matakin jihohi ma ba ta samu karbuwa ba. A karshe Cif Segun Osoba ya kawo shawarar a tsara zama ta bi tsarin abacada na sunayen mahalarta taron inda ya soki tsarin zama kan kabilanci ko bambancin addini.