✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Taron kasa zai haifar da da mai ido kuwa?

A ranar 1 ga Oktoba, 2013 ne Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya bayyana kudurinsa na neman a yi taron kasa. Ya bayyana hakan ne a…

Shugaban Kasa Goodluck Ebele JonathanA ranar 1 ga Oktoba, 2013 ne Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya bayyana kudurinsa na neman a yi taron kasa. Ya bayyana hakan ne a yayin da yake yi wa ’yan kasa jawabi lokacin bikin cikar Najeriya shekara 52 da samun ’yancin kai. Daga nan ya kafa kwamiti mai dauke da mutane 13, a karkashin shugabancin Sanata Femi Okurounmu.  
Wannan kudurin ya haifar da cece-kuce a kasar nan, inda wadansu suka yi hasashen taron ba zai haifar da da mai ido ba; yayin da wadansu kuma suka ce kwalliyar taron za ta biya kudin sabulu.
A makon jiya ne Shugaba Jonathan ya nada tsohon Babban Jojin Najeriya Idris Legbo Kutigi, a matsayin shugaban taron kasa, inda Farfesa Bolaji Akinyemi, tsohon Ministan kasashen Waje a matsayin mataimakinsa, kuma Dokta balerie Azinge take matsayin Sakatare. Za a gudanar da taron ne da mambobi 492, inda za a fara a ranar Litinin mai zuwa 17 ga wannan watan, za a kwashe har tsawon wata uku.
Sai dai tun da aka fitar da sunayen mambobin taron sai korafe-korafen rashin adalci suka kara yawaita, inda a yayin taron da Dattawan Arewa suka yi a Kano, a ranar Litinin da ta gabata kan matsayin Arewa a wurin taron kasa ne suka ce akwai wata makarkashiya da ake shirya wa Arewa a lokacin taron kasa.
A lokacin da Dokta Hakeem Baba-Ahmed yake jawabi yayin taron ne ya ce, “An shirya gudanar da taron kasa ne don a wargaza hadin kan Arewa, a  kuma ninka matsalolinta, inda yin hakan zai amfani Shugaba Jonathan wajen kamfe dinsa.”
A wurin taron dai Farfesa Auwalu Yadudu na Jami’ar Bayero da ke Kano, ya ce taron ba zai haifar da da mai ido ba, zai zama tamkar wadanda aka yi a baya ne, wato kamar wanda aka yi a lokacin tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo.
Mai magana da yawun kungiyar Dattawan Arewa, Farfesa Ango Abdullahi ya ce an shirya taron ne don Shugaba Jonathan ya bakanta Arewa.
Barista Solomon Dalung na Jami’ar Jos ya ba da shawarar idan har ana so taron kasa ya haifar da da mai ido, to ya kamata Shugaba Jonathan ya bari sai bayan watan Mayu, 2015 a lokacin wa’adinsa ya kare, ko kuma ya hakura da sauran kwanakin da suka rage masa don a yi taron kasa mai cikakken iko.
Wadansu kungiyoyin Musulmi sun koka cewa a cikin mambobin da aka zaba Musulmi suna da kashi 39 ne, yayin da wadanda ba musulmi ba suke da kashi 60 cikin 100. Su ma al’ummar kudancin Kaduna sun ce gwamnatin Jihar Kaduna ba ta nada kowa daga yankinsu ba, duk kuwa da cewa shugaban kasa ya nada mutanen yankin kamar su Zamani Lekwat da sauransu.
Ba wai daga bangaren Arewacin kasar nan ba ne ake ci gaba da samun korafe-korafen kan taron kasa ba, ko a shiyyar Shugaban kasa ana ci gaba da yin korafe-korafe a kan mambobin da aka zaba don gudanar da taron.
A makon jiya ne wadansu manyan kungiyoyin kabilar Urhobo da Ijaw da kuma Itsekiri suka gudanar da zanga-zanga kan cewa ba a zabi ko wakili daya daga cikinsu ba.
kungiyar kabilar Matasan Ijaw (IYC) ce ta fara rubuta wa Shugaban kasa takardar korafi kasancewar ba a zabi wakili daga cikinta ba.
A wasikar da kungiyar IYC ta rubuta mai dauke da sa hannun mai magana da yawunta, Mista Eric Omare ta ce: “kungiyar IYC tana bakin cikin rashin zabar wakili daga cikinta don taron kasa mai zuwa. An yi hakan ne don a kange matasan yankin Neja-Delta daga bayyana matsalolin da suke ci musu tuwo a kwarya.”
A makon jiya ma kungiyar kabilar Itsekiri mai suna Itsekiri Leaders of Thought (ILT) ta gudanar da zanga-zanga a garin Warri don bayyana rashin jin dadinta, sakamakon rashin zabar wakili daga cikinta kan taron kasa. A yayin zanga-zangar ’yan kungiyar sun bukaci gwamnatin tarayya ta gyara kura-kuran da ta yi yayin zabar mambobin taron.
kungiyar kabilar yankin Ogoni (MOSOP) da ke Jihar Ribas, a wasikar da ta rubuta mai dauke da sa hannun Shugabanta Legborsi Saro Pyagbara ta ce, ta kadu matuka bayan ta duba mambobin da za su gudanar da taron kasa, amma babu dan kabilarta, suka ce abin ya ba su mamaki, inda wadansu kabilu suke da wakilai kusan 40. Suka ce hakan ba adalci ba ne.
A yankin Yamma kuma musulmin yankin Yarbawa sun ce an mayar da su saniyar-ware a harkar taron da za a gudanar.
Su ma kabilar Nufawa sun ce a cikin wakilai 90 da za su wakilci kabilun kasar nan a wurin taron babu ko daya da aka zaba daga cikin kabilarsu.
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Alhaji Balarabe Musa ya ce taron zai zama na shan shayi ne kamar wadanda suka gabace shi.
Ya ce bayan an kammala taron za a mika shi ga shugaban kasa kafin ya tura shi ga majalisar tarayya, don haka za a iya gudanar da canje-canjen da za su dadada wa shugaban kasa. A yi nazari, shugaban kasa ne ya nemi a yi taron, shi kadai ya nada kwamitin shirya taron mai mutane 13, shi ne dai ya zabi shugaban taron, wato Idris Kutigi, shi ya zabi mambobin kwamitin, don haka sai abin da yake so za a yi.
Sai dai kuma Darakta-Janar na cibiyar horar da lauyoyi ta kasa (NIALS), Farfesa Epiphany Azinge ya ce taron zai ba ’yan Najeriya damar bayyana matsalolin da suka yi cacukwi da rayuwarsu, sannan zai kawo hanyoyin da za a magance matsalolin da suka dabaibaye Najeriya.
Wani abu da yake kara sanya shakku da ake ganin ko kwalliyar taron za ta biya kudin sabulu shi ne zabar tsohon Gwamnan Jihar Bayelsa Diepreye Alamieyeseigha a matsayin wanda zai wakilci jama’a, bayan ’yan sandan kasa da kasa (Interpol) sun taba kama shi a Landan kan zargin yin sama da fadi da dukiyar talakawa, inda daga karshe aka yanke masa hukunci dauri a gidan yari a Landan din.
Haka kuma an yi zargin a cikin mambobi 492 da za a yi taron da su, Shugaban kasa ne ya zabi kashi 25 cikin 100, inda jam’iyyar PDP a matakin tarayya da kuma jihohi suka zabi mambobi 150.
Shugaban kasa ya ware Naira biliyan 7 ne don shirya taron, inda za a kashe Naira biliyan 5.97 wajen biyan dakin kwanan mambobin taron, inda za a ba kowane mamba Naira miliyan 4 don ya biya dakin kwanansa yayin taron.
Duk da korafe-korafen da ake samu, abin tambaya a nan shi ne, anya taron zai haifar da da mai ido kuwa?