✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Taron kolin karawa juna sani na Jihar Yobe zai habaka noma da kiwo tare da samar da ayyukan yi – Gwamna Buni

Gwamna Mai Mala Bunin a jihar Yobe, y ace taron karawa juna sani da gwamnatin jihar ta gudanar a makon nan, a birnin Damaturu, an…

Gwamna Mai Mala Bunin a jihar Yobe, y ace taron karawa juna sani da gwamnatin jihar ta gudanar a makon nan, a birnin Damaturu, an kirkire shi ne da zummar bunkasa tare da tabbatar da dorewar harkokin noma da kiwo wuri guda.

A tsokacin da ya yi lokacin bude taron, a babban dakin taron gidan gwamnatin jihar, gwamnan y ace taron na wuni hudu zai zama gwadaben samar da ayyukun yi da kuma dorewar ci gaba tare da walwala a jihar.

Gwamna Buni ya bayyana cewar, kamar yadda lamarin yake a kusan ko wacce jiha a Najeriya, galibin al’ummar jihar Yoben manoma ne; kuma sun dogara da ita a zaman sana’a.

“….Dan haka noma da kiwo, ya zama kashin bayan tattalin arzikinmu.”Inji Gwamnan, ya kara da cewar, “Kuma lallai ne mu yi duk wata mai yiwuwa wajen bunkasa bangaren ta yadda zai zama ana gogayya da shi.”

 

Ya nunar da cewa taron, wanda aka yiwa taken: ‘Habaka ayyukan noma da kiwo dan wadatar abinci tare da bunkasar arziki’ zai taimaka wa jihar gaya ta fuskar mayar da harkar noma ta zama babbar abar dogaro wajen inganta tattalin arzikin jihar.

“A daidai lokacin da kasarmu ke ci gaba da lalubo wasu hanyoyin samun kudaden shiga na daban da kuma samar da ayyuka tare da fitar da al’umma daga kangin fatara; babu alamun da ke nuni da kamar ko muna alkinta harkar noma yadda ya kamata, a matsayin babbar hanyar bunkasa arziki.”

“Duk da irin albarkar kasar noma mai tarin yawa tare da maza majiya karfin noman da muke da su a jihar nan, har yanzu harkar noman kusan kacokan ana yin ta ne a tsari irin na dauri. Har way au, duk da irin gagurumin kokarin da gwamnatocin da suka gabata a nan jihar suka yi ta harkar noman, har yanzu ba a rabu da bukar ba.”   Inji Buni.

Gwamnan ya ci gaba da cewa: “Na yi Imanin cewa idan dai mun dukufa, to kuwa lallai za mu kai gaci. Kuma ina imanin noma da kiwo sune ginshikan da za samar mana da damammaki maras iyaka da al’ummarmu za ta amfana da shi wajen inganta rayuwarsu. Hakan ne ya sanya muka ga dacewar mu kira masana a bangaren noma domin su yi musayar miyau kana su baje mana basirarsu ta yadda za mu inganta noma a jihar Yobe.”

Ya kuma bayyan cewa, a karshen taron gwamnatin jihar za ta kafa ‘Kwamitin kwararru’ wanda zai yi duba na tsanaki tare da kalailace ire-iren batutuwa da mukalun da masanan suka gabatar a yayin taron, da zummar duba yadda gwamntin za a aiwatar da su a zahirance.

Mai Mala Buni ya ce, Farfesa Abba Gambo, shugaban tsangayar noma ta jami’ar Jihar Yoben, shi ne zai  shugabanci wannan kwamitin.

“Bisa umurnina, Mukaddashin Sakataren Gwamnatin Jiha, zai fara aikin kafawa tare da nada mambobin wannan kwamitin ba tare da bata wani lokaci ba,” inji Gwamna  Mai Mala Buni.