✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Taron Majalisar Dinkin Duniya na 74: Abubuwan da shugabannin kasashe suka tabo

Shugabannin kasashen duniya na ci gaba da jawabi a hedkwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin New York a wajen taron majalisar karo na 74.…

Shugabannin kasashen duniya na ci gaba da jawabi a hedkwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin New York a wajen taron majalisar karo na 74.

Shugabannin kasashen daya bayan daya sun rika hawa mumbarin majalisar suna gabatar da batutuwa tun daga ranar 24 inda za a kammala 30 ga Satumban  nan. A lokacin taron, shugabannin kasashen sun rika yi amfani da wannan dama da ake kallon babban taron diflomasiya na duniya suna gabatar da jawabai kan muhimman abubuwan da suke damun kasashensu.

Wannan taron yana zuwa ne a daidai lokacin da wutar zaman tankiya ke ci gaba da ruruwa a Gabas ta Tsakiya, yayin da  Firayi Ministan Birtaniya ke faman matsa lamba kan lallai ne Birtaniya ta fice dungurungum daga Tarayyar Turai a karshen watan Oktoba; sai a daya barayin kuma kiraye-kirayen lallai gwamnatocin kasashe su dauki kwakkwaran mataki wajen yakar dumamar yanayi.

Muhimman batutuwa a taron …Fito-na-fito tsakanin Amurka da Iran

An samu fito-na-fito a tsakanin kasashen Amurka da Iran sakamakon yadda dangantakarsu ta yi tsami, inda shugabannin kasashen biyu suka gabatar da jawabansu gaban majalisar; kowanensu yana bayyana bahasin da ya saba wa na dan uwansa game da halin tsaro a yankin Gabas ta Tsakiya.

Kasashen Amurka da Saudiyya da Jamus da Ingila da Faransa suna nuna wa Iran yatsa game da harin da aka kai cikin watan nan kan matatar mai ta kasar Saudiyya. Sai dai tuni Iran ta yi fatali da zargin cewa tana da hannu a harin, wanda ’yan tawayen Houthi na kasar Yemen suka dauki alhakinsa.

A jawabinsa ranar Talata, Shugaba Donald Trump ya ce: “Babu wata gwamnatin da ta san ya kamata da za ta mara baya ga niyyar Iran ta takalar fada da kuma ina-da-kisa.”

“Kuma idan ta ci gaba da nuna kunnen kashi, to ba za a dage takunkumin da ke wuyanta ba, bil hasali ma za a tsaurara su ne,” inji Trump.

Sai dai ya shaida wa zauren taron cewa, Amurka a shirye take ta kulla kawance da duk wata kasa da take bidar zaman lafiya da kuma kare mutuncin kanta da kanta.

Shugaban Iran Hassan Rouhani a nasa jawabin a zauren, ya kawar da yiwuwar zama kan teburin sulhu a tsakanin Iran da Amurka muddin ba a janye takunkumin da aka dora wa kasarsa ba.

Kafin jawabinsa jami’an Iran sun ce za a yi ganawar ce kawai idan Shugaba Trump ya yi abin da ya zama wajibi na sassauta takunkumin da aka saka wa Iran ta hanyar musanya su da saka ido na dindindin ga tashoshin nukiliyar Iran din.

A jawabin Rouhani ya ce, “Iran ta jure wa abin da ya kira ta’addanci kan tattalin arziki marar kan gado.”  Ya yi gargadin cewa yankin Tekun Fasha  “Na gargarar rugujewa, domin kalma guda na iya jefa daukacin yankin a cikin mummunan tashin hankali,” inji shi.

Kara daukar matakai kan sauyin yanayi

Muhimmin abin da ya yi kane-kane a kanun labarai a makon jiya shi ne batun matakai ko akasin haka da ake dauka kan sauyin yanayi, kamar yadda masu rajin kare yanayin suke cewa.

Kwanaki bayan miliyoyin mutane a fadin duniya sun yi jerin gwano inda suka nemi lallai a kara daukar matakai game da tunkarar sauyin yanayi, fiye da shugabannin kasashe 60 sun halarci wani taron koli kan sauyin yanayin a ranar Litinin din makon nan. Masu rajin kare muhallin sun ci gaba da jerin gwanon har zuwa shekaranjiya Laraba.

Shugaban da ya fara jawabi a zauren majalisar shi ne  Jair Bolsonaro na Brazil wanda ya sha suka sosai kan manufofinsa game da tattalin arziki da kuma na muhalli a yayin da wutar daji ke ci gaba da ci a gandun dajin  Amazon da ke kasar ta Brazil.

Shugabannin da suka kaurace wa taron

Daga cikin shugabannin da suka ki halartar taron akwai Firayi Ministan Isra’ila da Shugaban kasar Benezuela Nicolas Maduro da fiye da shugabannin kasashe 50 ke wa kallon haramtaccen shugaba. Sauran sun hada da Shugaban Rasha Bladimir Putin da kuma Shugaban  China Di Jinping.

Sai dai shugabannin wadannan kasashen da ba su halarci taron ba sun aike da wakilansu zuwa babban zauren muhawarar na diflomasiyar duniya.

Ranar farko ta taron

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Mista  Antonio Guterres da Shugaban Zauren Tijjani Muhammad-Bande ne suka bude jawabai a taron a safiyar ranar Talata. Sa’annan Shugaban kasar Brazil ya rufa musu baya. Bayan nan sai shugabannin Masar da Amurka da Turkiya suka gabatar da nasu jawaban. Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya zama Shugaba na biyar da ya gabatar da jawabi a zauren, inda ya tabo batutuwa daban-daban da suka shafi Najeriya.

Shugaba Buharin ya bada fifiko a jawabinsa  sosai kan batun badakalar nan da ta shafi kasar da wani Kamfanin Ireland mai suna P&ID. Ya ce wadansu miyagun kungiyoyin kasa da kasa na kokarin damfarar Najeriya biliyoyin Dala. Shugaba Buhari ya bayyana yarjejeniyar kasuwanci tsakanin Kamfanin P&ID na Ireland da Gwamnatin Najeriya a matsayin yunkurin damfarar kasar Dala biliyan 9.6. Wata kotun Birtaniya ce ta bai wa Najeriya umarnin biyan makudan kudaden ga kamfanin na P&ID bayan wargajewar yarjejeniyar iskar gas da aka kulla tsakanin bangarorin biyu a shekarar 2010. Kamfanin ya cimma yarjejeniya da gwamnatin Najeriya domin gina matatar iskar gas a Jihar Kuros Riba, amma yarjejeniyar ta susuce bayan shekara biyu. Kamfanin ya kai gwamnatin Najeriya kotun birnin Landan kan zarginta da karya ka’idojin yarjejeniyar.

Wannan ne karo na farko da Shugaba Buhari ya yi tsokaci a bainar jama’a kan wannnan batu wanda ya haifar da cece-kuce a ciki da wajen Najeriya. Shugaba Buhari ya kuma nanata wa zauren majalisar niyyar gwamnatinsa ta ci gaba da yaki da cin hanci da rashawa, yayin da ya caccaki kafafen sada zumunta saboda yadda ake amfani da su wajen yada miyagun ayyuka da tashe-tashen hankula da labaran karya.

Sai dai tun farko babbar jam’iyar hamayya a Najeriya wato PDP ta soki Shugaba Buhari cewa ya je taron ne ‘ba tare da wata kwakkwarar  manufa ko jawabin da zai gabatar ga zauren’ ba.

A ranar Talatar shugabannin kasashe 38 ne suka gabatar da jawabai ciki har da kasashen Afirka takwas da suka hadar da Najeriya da Nijar da Masar da Burkina Faso da Angola da Rwanda da Senegal da kuma Moroko. Shugabannin wasu manyan kasashen ma sun gabatar da nasu jawaban a ranar Talatar da suka hada da Birtaniya da Spain da Faransa da China da Japan da kuma Turkiyya.