✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Taron Makomar kasa? (2)

Tambayar da kila wani zai yi ita ce shin taron makomar kasar ne za a yi ko kuwa taron makomar al’ummar da ke dambare cikin…

Tambayar da kila wani zai yi ita ce shin taron makomar kasar ne za a yi ko kuwa taron makomar al’ummar da ke dambare cikin kasar? Kamar yadda muka sha fada a kullum, ba ruwan kasar nan da matsalolin al’ummarta. Ba ruwan kasar nan rashin hadin kan al’ummarta. Ba ruwan kasar nan da irin bambance-bambancen addinai da kabilu da jinsunan da wai ke damun ta. Matsalar kasar ta mutane ce ba wasu can daban ba. Saboda haka idan ana son a taru a tattauna, ba makomar kasar za a tsinkaya ba, makomar mutanen da ke cikinta.
Muna son mu san makomar mutane sama da milyan 60 da ke da tabuwar hankali da ke cikin kasar nan da yadda za a sama musu mafita daga cikin ukubar da wasu marasa hankalin suka jefa su a ciki. Muna so mu san su wa za su wakilci wadannan tababbu a wajen taron da wa kuma za su kaura don neman musu mafita.
Su wa kuma za su wakilci mutane sama da milyan 80 da ke kwana da tashi cikin talauci da rashi da fatara da yunwa a wajen wannan taro? Shin wadanda suka fito ne daga Kudu ko daga Arewa? Ko wadanda suka kasance Musulmi ko Kirista ko wadanda ba su da addini? Shin ko kuwa wadannan gungun mutane da ke kwana da yunwa daga cikin maza ko mata ko yara ko manya za su fito? Sai mun fahimci matsayinsu a wajen wannan taro za mu san inda kasar ta sa gaba ko za ta sa gaba.
Haka kuma, su kuma mutane sama da milyan 21 da ke yawo da watangaririya ba aikin yi ko sana’ar da za su samu na toshe uwar hanji su wa za su wakilce su a wurin wannan taro? Ko su ba mutane ba ne, kuma ‘yan kasa a cikin wannan tarayya? Shin ko su bai dace a san makomar su ba, sai ta kasa da ke zaune sumul? Sai mun sama wa irin wadannan mutane mazauni a wajen wannan taro abubuwa za su inganta, domin kuwa idan ba su sami lokacin tattaunawa da wadanda suka iza su cikin kogin wahala ba, duk wani taron makomar kasa ba zai je ko’ina ba, domin kuwa ba abin da muke yi sai zolayar kan mu da kan mu.
Ya kuma dace mu san wa zai wakilci mutane sama da milyan 50 da ke shiga da fici cikin harkar karatu tun daga Firamare har zuwa Jami’a, amma maimakon ilmi ya shige su, sai dai su yi hannun riga da shi. Ya dace a san me ya sa suke yin hannun riga da ilmin, alhali ilmin ne ya kamata ya gina su, su kuma su ne ya kamata su gina kasar, har ta tada komadar da za ta taimaka wa makomar kasar.
Shin don Allah a taya ni tunani domin ni dai har yanzu ban san yadda za a yi da mutane sama da milyan 40 da ba su da wurin kwana ko da a cikin kauyuka da garuruwan da suke zaune ba, balle a ce sun iso Abuja don tattauna makomar kasar tamu? A ina za su kwana in sun iso Abuja, na tabbata ba dai a Asokoro ko Maitama ko sauran wuraren alatun Abuja ba, domin kuwa tun a nan za su gane cewa ai taron makomar kasar da ya dace a yi shi ne a canza wurin kwana, mutanen da ke  zaune a Abuja ko Kaduna ko Lagos ko Fatakwal su koma cikin kurkukun da su talakawan suka fito, sannan a fara batun tattauna makomar kasa.
Shin shi taron na makomar kasar da za a yi zai ba makwabtan da ke tattare da rayuwar rashin magudanun ruwan kwarai ko titunan kwarai ko sauran abubuwan more rayuwa damar su halarci taron? Za a ba su dama su tattauna makomar rayuwarsu ta rashin ingantattun abubuwan more rayuwa? Za a ba masu takawa a sayyada cikin matsuwa ta rashin hanyoyin kwarai damar su bayyana wa duniya halin da suke ciki? Za a ba masu kekuna damar su bayyana yadda masu mashin da motoci ke cin mutuncinsu a lokacin fafutikar neman mafita a rayuwa? Shin za a ba masu motoci damar su farke zuciyarsu game da rashin hanyoyin kwarai da ke nuna motoci da sauran abubuwan hawa na bukatar sanin makomar su ba wai kasar kadai ba?!
Ina kuma fatar a wannan taron na makomar kasar za a gayyato daruruwan mata da mazan da ko dai sun kasa yin aure, ko kuma wadanda suka yi daga cikinsu, sun kasa zaman auren saboda wahalar rayuwa ko wadansu daga cikin su, mazaje ko matayensu suka mutu, suka ka bar su da jangwam. Haka kuma ina za a sa wadannan mutanen da ba su san wata aba wai ita kasa ba saboda fyade da madigo da ludu su ne wasu suka mayar musu da rayuwar yau da kullum?
Idan ba an nazarci da tattauna ire-iren wadannan matsaloli ba kafin a tattaru a Abuja, kai ko ma ina ne ake niyyar taruwa don tattauna makomar Nijeriya, ba abin da za mu yi face aiki babangiwa, za mu ba wasu ‘yan tsiraru ne damar su sake lakume dan abin da ya rage mana daga romon arzikin kasar da tuni mun san makomarta, mu ne dai ba mu san makomar kanmu da kanmu ba, domin mun kasance cikin dimuwa, ta yadda idan ma an je wajen taron makomar kasa, za mu kasance cikin halin wuji-wuji gano gabas, mu kaso gano gabas din, domin mun dage nuna sama ko kasa wai can ne gabas. Saboda haka lokaci ya yi da talakan kasar nan zai fahimci cewa duk wani taro da ba taronsa ba ko na neman masa makoma ba ko na makomar ilmin ‘ya’yansa ko zamantakewar makwabtansa ko kuma ci gaban tattalin arzikinsa da kuma ingantuwar siyasar mulkinsa ba, taron banza ne, taron je-ka-na-yi-ka-ne, ba kuma abin da zai haifar sai karin ukuba ga wanda bai ji, bai gani ba.
Allah dai ya kyauta!
Mun Kammala