Da Dumi Dumi

Taron Tattunawa na Daily Trust: Yadda za a dada inganta dimokuradiyya a Najeriya – Namadi, Shettima da Fayemi

Ministar Harkokin Jinqai Hajiya Sadiya Umar Faruq tana miqa wa Mama Rosie cakin kyautar Gwarzuwar Afirka ta Daily Trust ta bana Hoto: Felid Onigbinde
Ministar Harkokin Jinqai Hajiya Sadiya Umar Faruq tana miqa wa Mama Rosie cakin kyautar Gwarzuwar Afirka ta Daily Trust ta bana Hoto: Felid Onigbinde

A jiya Alhamis ce aka gudanar da taron tattaunawa na Trust Dialogue da Kamfanin Media Trust mai buga jaridun Daily Trust da Aminiya ke daukar nauyi  duk shekara.

Taron na bana shi ne karo na 17, kuma an sanya wa taron taken; “Shekara 20 da Mulkin Dimokuradiyya a Najeriya: Riba, Rashin Ribarsa da Damarmakin da ke Cikinsa.”

Taron ya gudana ne a Dakin Taro na Rundunar Sojin Saman Najeriya da ke Kado, Abuja, inda tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Alhaji Namadi Sambo ya shugabanci taron, sannan Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan ya kasance Babban Bako na Musamman.

A jawabin maraba a wajen taron, Shugaban Hukumar Gudanarwar Kamfanin Media Trust, Malam Kabiru Yusuf ya ce, “Duk da yawan tabbacin da gwamnonin Arewa maso Yamma da Shugaban ’Yan sanda suke ba mutane, har yanzu ana ci gaba da satar mutane.”

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Alhaji Namadi Sambo ya yaba wa mahukuntan Kamfanin Media Trust bisa kokarinsu na ci gaba da tsara wannan taro har tsawon shekara 17, “Ina jinjina wa mahukuntan Daily Trust kan kokarin da suka yi na ci gaba da wannan taro na tattaunawa tsawon shekara 17 da suka wuce.

ADVERTISEMENT

Alhaji Namadi Sambo ya ce dawowar mulkin dimokuradiyya a 1999 yana daya daga cikin manyan abubuwan ci gaba da suka faru a Najeriya tun samun ’yancin kai.

“Duk da kalubalen da muke fuskanta wajen ci gaban siyasa, mun samu ci gaba matuka musamman a hadin kai.”

Ya ce tarihin dimokuradiyya ba zai cika ba, sai an hada da jajircewar da tsohon Shugaban Kasa Gooodluck Jonathan ya yi na samar da sahihin zabe ta hanyar ba tsohon Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Attahiru Jega damar gudanar da zabe na kwarai, sannan ya taya abokin hamaryarsa Shugaba Buhari murnar nasarar zaben tun kafin Hukumar INEC ta bayyana shi, inda ya ce kiran ya sa “Ya shiga tarihi sosai.” Sai ya bukaci ’yan jarida su ci gaba da gudanar da ayyukansu na ganin gwamnati ta yi aikin da ya dace, sannan su guji saba wa ka’ida a lokacin aikinsu.

A jawabin daya daga cikin masu jawabi a taron tsohon Gwamnan Jihar Borno, Sanata Kashim Shettima ya gargadi ’yan siyasa kan su yi taka-tsantsan wajen neman mukamai, su guji akidar ko a mutu ko a yi rai, inda ya ce a mafi yawan lokaci wadanda suka zafafa neman matsayi a siyasar, ba su ne ke nasara ba a karshe.

Ya ce, “Duk yadda muke ganin mulkin dimokuradiyya, yadda mutum zai iya zuwa kotu kawai ma babbar nasarar dimokuradiyya ce. Damar bayyana ra’ayi ma yana cikin abin da ya raba mulkin dimokuradiyya da mulkin kama-karya. Don haka a wajena, babbar nasarar mulkin dimokuradiyya ita ce samun ’yancin daga mulkin kama-karya. Domin kasancewa karkashin mulkin kama-karya kadai ya isa sauya tunanin mutum.”

 Manyan Baqi a taron tattaunawa na shekara-shekara na Daily Trust da aka gudanar jiya a Abuja        	     					    Hoto: Abdul Musa
Manyan Baqi a taron tattaunawa na shekara-shekara na Daily Trust da aka gudanar jiya a Abuja Hoto: Abdul Musa

Sanata Kashim ya kara da cewa, “Akwai abubuwan ci gaba da dama a karkashin mulkin dimokuradiyya na kasar nan a shekara 20 da suka wuce. ko ma me za ka fada a game da mulkin Olusegun Obasanjo, zai yi wuya ka ki bayyana kokarinsa na hada kan kasar nan tamkar tsintsiya. Sannan duk tunanin mutum game da hakan, ya yi karfin zuciya wajen kafa hukumomin EFCC da ICPC.

“Sannan ba za a manta da marigayi Umaru Musa ’Yar’aduwa ba, wanda shi ne ya aza tubalin yi wa siyasar kasar nan gyaran fuska. Kuma wani babban ribar dimokuradiyya shi ne yadda tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya tserar da kasar nan daga fadawa cikin rikici, ta hanyar amincewa da shan kaye,” inji shi.

Sai ya bayyana cewa zuwan Shugaba Buhari ya canja tunanin mutane, musamman wajen dawo da martabar kasar nan.

A jawabin, ’yar Majalisar Wakilai, Lynda Chuba Ikpeazu cewa ta yi, “Rashin jam’iyyun siyasa masu akida yana matukar jawo wa siyasa koma-baya a Najeriya.” Sai ta bukaci a rika yi wa gwamnati suka mai ma’ana.

Kuma ta bukaci masu zabe su rika tunanin gobensu da ta ’ya’yansu a lokacin zabe.

A jawabin Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, kuma Gwamnan Jihar Ekiti Mista Kayode Fayemi ya ce, “Mun samu ci gaba a bangarori da dama a shekara 20 da suka gabata.”

Game da batun Rundunar Tsaro ta Amotekun da aka kafa a jihohin Yamma kuwa, cewa ya yi, “Batun bude rundunar tsaron Amotekun ya sa na ga damarmaki da abubuwa da za su iya yiwuwa.”

 

…Mama Rosie daga Afirka ta Kudu ta lashe Gwarazuwar Afirka ta Daliy Trust na bana

A shekaranjiya ce kuma aka karrama Gwarazuwar Afirka ta bana ta Daily Trust, inda wata mata ’yar kasar Afirka ta Kudu Rosalia Mashale da aka fi sani da Mama Rosie ta lashe kyautar.

Maman Rosie ta lashe kyautar ce bisa irin kokarinta da tallafin da take ba yara marayu masu fama da cutar kanjamau su 5,305, a karkashin Gidauniyarta ta Baphumelele Children’s Home, inda ta taimaka wa marayun har wadansu daga cikinsu suka zama manya a kasar.

Shugaban Kwamitin Kyautar, kuma tsohon Shugaban Kasar Bostwana, Mista Festus Mogae ne ya sanar da haka a taron bayar da kyautar.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya